36-37

1.5K 75 5
                                    

NAMIJIN GORO*

*Na Aysha Sada Machika*

*Ina alfahari daku akoda yaushe mutanen arzik'i, Allah yabarmu tare yakuma bar zumunci AMEEN*

*Aysha Hamisu Malumfashi*
*Nafisa moh'd Jos*
*Fatima Umar Sulaiman*
*Khadija Ahmad (Orem)*
*Asiya Munir (Sister)*
*Habiba Sanee Bk*
*Aysha Yak'ub Gusau (Uwani)*
*Halima Abububakar (Mekeke)*
*Farida Lawal Garba*
*Ummah Umar Funtua*
*Bahijjah Kamilu*
*Yusrah M Sada*
*Salsabila Moh'd*
*Halima Abdullahi Bagiwa*
*Rahama Hassan Rimi*


                🌱 *36* 🌱


Yayi sauri ya fito daga d'aki yazo ya same ta.

"Jiddah waye ya kirani d'azu?" Ya tambaya.

Batare data d'ago ta kallesa ba ta amsa "nima bansani ba, nadai ji waya na ringing na zagaya baya na d'auko sai gaka ka shigo"

"Ok tnx" abunda ya fad'a kenan ya juya.

Bayan wucewarsa sai ta mik'e tsaye tana tinani "to waye ya kirasa? Abun mamaki ina kira wayar na ringing, kodai..... Kai anya" irin tinanin data rik'ayi kenan.

**********

Maijiddah na zaune kan dakalin shiga cikin gida tayi shiru ita kad'ai tanata sak'ar zuci, sai ji tayi and'an tab'ata a wuya da tsinke, tayi sauri ta juyo, murmushi tayi bayan data ga Kamal ne a tsaye bayanta, ya matso ze zauna tace "Yayanah ka bari na d'auko maka kujera akwai k'ura wurin"

"Akwai k'ura wurin amma ke kika iya zama? Nima ki barni na zauna haka"

Kamal ya zauna kusa da ita, sai tad'an d'ago kai ta kallesa sai kuma ta maida ta saddar k'asa, Kallonta kawai Kamal yake yana murmushi.

"Yaya Kamal ba'a mamaki da ikon Allah, amma ina mamakin yadda zuciyarka ta kamu da sona, bayan ga y'ammata nan iri-iri, yaran manya, masu ilimi, masu kyau, wanda suka had'a komai da komai, dukda nima na kamu da sonka amma hakan be hanani k'osawa na farka daga baccin da nake ba, bansan ranar da zatazo na dena ganin kamar mafarki nake ba" Maijiddah ta fad'i haka kanta na k'asa.

"Sai ranar da aka kawoman ke gidana a matsayin mata ta, ranar ne zaki farka daga wannan mafarkin naki, Maijiddah ina ganin kamar akwai wani abu da baki sani ba, idan so ze shigo gida baya sallama kuma baya jiran izini saboda gidansa ne, duk duniya babu wanda yayi arzik'in SO domin shi SO ko ina yanada gida, shiyasa duk inda yagadama dole ya shiga ya zauna kuma dole ayi masa maraba, haka SO babu ruwansa da yaren dake fatar baki, yaren zuciyoyi kawai yake d'auka, SO babu ruwansa da maik'ud'i ko talaka, SO babu ruwansa da kyau ko muni, SO babu ruwansa da fari ko bak'i, babu ruwansa da jahili ko mai ilimi, SO yasha gaban duk tinanin me tinani, don haka takurama zuciyarki wurin nemo dalilin dayasa nake sonki wahalarwa ne, nidai nasan i luv u wt no reason dats y no reason can stop me 4rm loving u en dat i promise K'anwata"

"Nagode" ta fad'a atak'aice.

"Me nayi miki na godiya?"

"Komai ma"

Kamal ya sake sakin murmushi batare daya ce komai ba.

Nan suka shiga fira yanata bata labarin china, abincinsu da yanayin mutanensu dakuma yanayin rayuwarsu, tayita dariya.

***********

Parlour Hajiya Uwa ta iske Khalil, Kamal da Maijiddah kowa da abunda ke ransa, sai tace da Maijiddah "ke tashi ki bani wuri zanyi magana da y'ay'ana"

Maijiddah ta mik'e zata wuce Khalil ya tashi ze bita.

"Kai bindi ina zaka? Bakaji me nace bane?" Hajiya Uwa ta masa magana

NAMIJIN GORO...Where stories live. Discover now