NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
🌱 *13*🌱
Y'an uwanta sai ji suke dama karta tafi, haka mahaifiyarta ma Yabi.
Maijiddah tasa k'anwarta ta rakata hayi gidan wani kawunsu, ta samo filisco da karara, bayan da suka dawo gida da Yabi ta gani ta tambayeta me zatayi dasu, sai Maijiddah tace ai can birni suna son su sosai batasan dai amfanin da suke dashi ba amma Hajiya Uwa ce ma tace ta samo mata, Yabi dai ta bita da ido cike da mamaki.
Suna nan zaune saiga yaro ya shigo da Fura mai yawan gaske, wai Iyatu ta aikosa tace aba Maijiddah idan zata wuce ta kaima Alhaji Abdullahi injita, Yabi ta karb'a tace yace "angode"
Akace komai saidai idan ba'a sa masa rana ba, kwanci tashi yau har Maijiddah ta cika sati d'aya gam, yauce ranar komawarta birni.
Kasancewar babu nisa sosai tsakanin Rimin Gado da cikin Jihar Kano yasa bata bar gidansu ba saida tayi sallar la'asar, tako samu y'an rakiya buya guda kamar masu kai amarya.
Kafin ta shiga mota saida tace da k'aninta "idan ka koma gida ka tina ma Inna fa kar ta rik'a barin wayarta ba caji, dana isa ma zan kirata" yace mata "to".
Ta shiga mota suka yita waving juna irin wanda baya k'arewa, tana " bai bai (bye bye)" su kuma suna "bai bai bai" (🤣🤣🤣).
*****************
*KANO*Sun iso garin kano da wuri amma saboda mugun traffic yasa itace bata dangana da gidan nasu ba sai ana kiran magrib (kun jini nima da d'aure ma k'arya gindi "wai gidansu").
Lokacin data isa gidan tsit, Yawale ne kad'ai gaban gate yana alwala, yana ganinta ya aje buta ya mik'e tsaye yace " Maijiddah ya akai kika dawo? Da kun kirani a waya da baki dawo ba, saboda banason tashin hankali, Hajiya ranta ya b'aci dake na tambayeta me kika mata bata kulani ba"
Ga mamaki na yana rufe baki ta zube k'asa tace "ina wuni Baba, mun same ku lafiya?"
Saida yayi shiru na wani d'an guntun lokaci sannan yace "lafiya lau"
Ta cigaba da cewa "mutanen gida duk suna ta gaishe ka, Inna nata godiya dasa albarkar abunda ka aika masu, koda yake naji kunyi waya jiya da daddare"
Gyad'a kai kawai yayi.
Taja y'an kayanta tace "Baba na gaji wallahi bari na shiga daga ciki" ai sai Yawale ya saki baki ya bita da ido harta shige, ya kasa cewa komai.
Ita ko a zuciyarta cewa tayi "uhmm lallai ma Baba insunsan wata ai basu san wata ba, zama dani daram wai akace kuturwar uwa zama dake dole"
Taci sa'a koda ta shiga bata iske su Hajiya ba kowa na d'aki sai yaron nan Safwan shi kad'ai a parlour yana kallon cartoon, kallon-kallo aka rik'a yi, shidai a zuciyarsa yace wannan daga ina? Itama haka, shaf tama manta da cewa yayar Khalil zata zo, haka suka gama kallon juna da yaron ta wuce hanyar d'akinta.
Tana shiga d'akin ta kira Yabi ta fad'a mata ta iso, Yabi tayita hamdala dana cewa "to barka, Allah yayi albarka Allah kuma ya taimaka" Maijiddah ta amsa da amin.
Shikam Yawale yana daga waje amma jira yake kawai yaji yadda za'a k'are.
Safwan yaje ya samu Momyn su yace " Mami who is dat lady?" Da sauri Hadiza ta fuskance sa domin kunsan duniyar yanzu abun tsoro ce bare kuma yara da idanuwansu a bud'e yake suna ganin komai, ta yamutse fuska sannan tace "A lady, where?"
"Yes A lady, in d parlour i was watching cartoon When she comes in, she stared at me 4some secs b4 she move in, Mami is she a gud person? She scared me" Inji Safwan.
