NAMIJIN GORO*
*Na Aysha Sada Machika*
🌱 *30* 🌱
Ta k'ura masa ido batare da tace komai ba, sai ma wani azababben miyau danaga ta had'e dak'yar ya wuce mak'oshinta.
A karo na biyu Kamal ya sake tambayarta,
"Kinyi shiru, don Allah ki fad'aman kina sona"
Kallon nasa dai ta cigaba dayi, sanin rashin tsoro irin na Maijiddah shiyasa nayi tinanin lokaci guda zata bashi amsa dai-dai da yadda take ji acikin ranta, amma inaaaa kalmar so a inda ya dace tafi k'arfin wasa.
"Kinyi shiru Maijiddah" ya sake fad'a.
Maijiddah ta zamo jikinta kamar zata saukar da guiwowinta k'asa tace,
"Naji duk abubuwan dakace Yayanah, wallahi maganganunka sunsa kwakwalwata juyawa sau babu adadi, ka tadani idan bacci nake, idan kuma wasa kake ka sanar dani, kaja kunnuwa sosai don naji abunda ka fad'a dakyau domin na tabbata ban jiyo daidai ba"
"Dai-dai kikaji Maijiddah, nine dai Yayanki Kamal nazo gareki da k'ok'on barata, ki amince dani, ki bani amanar rayuwarki na miki alk'awari zan kula dake tare da dukkan buk'atunki" cewar Kamal, cikin k'osawa dajin amsa daga gareta.
Maijiddah ta lumfasa sannan tace,
"Idan bazaka damu ba don Allah kad'an bani lokaci nayi tinani, wallahi jina nake kamar bani ba, waiko dagaske ni kake nufi? Kodai wata ce can ta daban, nice fa Maijiddah k'anwarka mai aikin gidanku, d'iyar Maigadin gidanku, hala baka ganeni bane?"
Kamal ya mik'e tsaye fuskarsa cike da murmushi domin shi maganarta ma dariya ta bashi, sannan yace "ked'in dai ke nake nufi, na baki lokaci kamar yadda kika buk'ata don nima ba sauri nake ba kuma banaso nayi rushing d'inki, tek ur tym dear, think over it ina sauraronki"
Ya fice daga d'akin batare daya tsaya jin abunda zata sake cewa ba, itakam ya batta nan a sandare, ta mik'e tsaye taje jikin mirror ta k'arema kanta kallo, ta rik'a shashshafa jikinta, tanaso ta tabbatar da eh lallai itace Zahiri ba bawani abu ba.
Jikinta ya matuk'ar yin sanyi gyaran d'akin ma da take ai saidai ya jira ta gama fira da zuciyarta tukun.
*********
Washe garin ranar.
Maijiddah kam saita tsinci kanta da tsananin jin kunyar had'a ido da Kamal, hakan yasa ta rik'a nuk'u-nuk'un fitowa daga takinta tayi aiki.
Tana bud'e k'ofarta suka sake yin karo da Khalil, ta dafe goshinta da hannu ta kallesa tana yamutse fuska.
"Wai kai sai kazo bakin k'ofar mutane kayi tsaye kamar b'arawo kokuma mai duba" Maijiddah ta fad'a ranta bace.
"Memakon ma ki bani hak'uri kin bigeni saiki wani fara masifar da kika saba" Khalil ya mayar mata.
Maijiddah ta k'arasa fitowa daga cikin d'akin ta maida k'ofa ta rufe, ta jingina da k'ofar sannan tace,
"Mema kazo yi k'ofar d'akina?"
"Nazo na kalli k'ofar ne na juya, ko kinada matsala da hakan?" Inji Khalil.
Maijiddah tad'an hararesa sannan tace "kaji dashi, idan ka tashi zuwa kallon k'ofar ka rik'a had'awa da bangon duk ka kallace kaji ko?" Ta wuce ta barsa nan.
Tana wucewa yace "oho dai aidai kinji zafi, jarababba kawai, wallahi wannan yarinyar taga wurin kwana na ta cika tsiwar bala'i"
Ba shiri Maijiddah na gama shara ta wuce da gudu wurin Mariya, ta kwashe duk yadda sukayi da Kamal ta fad'a mata, Mariya ta buga wani uban ihu sannan ta tashi ta rik'a tsalle tana juyi, saida Maijiddah ta zaunar da ita sannan ta tsaya suka fara maganar hankali.
