5

539 57 2
                                    

Karfe 7 na safe ta tashi daga bacci da addua a bakinta sai da ta danyi mintuna kadan tukuna ta tashi ta shiga bandaki ta hada ruwan zafi tayi wanka ta fito ta kimtsa riga da wando tasa masu kyau blue ta saka hula baka ta fesa turaruka masu kamshi ta dan tatara dakin ta ajiye komai a mazaunin shi ta fito....dakin Zainab ta nufah bata tararar da ita ba ta san cewa Ammi tana bangaren Abba so ba zata same ta a daki ba sai kawai ta wuce kitchen.... sallama tayi musu suka amsa tace inah kwanan ku lami ce ta amsa tana cewa "lafiya qalau anty"itah kuwa Zainab kyaleta tayi itama taki kulata duban lami tayi tace "Ammi ta fada maki abun da za'a dafa? Aa bata fada ba amma ki tambayi yaya Zainab juyowa tayi gurinta tace "yaya ammi ta fadi abun da za'ayi?girgiza mata kai tayi tace "aa wai duk abun da mukaga yayi kawai muyi".."OK toh ke zakiyi koh ni zanyi"..kuyi kawai ni sai nayi juice toh kawai tace mata..

Tunani ta farayi wanne irin abinci zatayi ganin sun dade basa Nigeria so ya kamata tayi musu abincin yan gayu irinsu sai kawai ta yanke shawarar dafa macaroni da dankali... Lami Dan Allah akwai alayyahu a gidan koh?lami tace eh akwai sauran na jiya da akayi danbu

Toh dan Allah ki yanka mun kanana ba manya ba tace toh ita kuma ta dauko macaroni tayi parboiling dinta
ta agiye a gefe sannan ta dauki attarugu da albasa ta markade a blender dama ta dafa namanta ta yanka kanana ta dauki dankali Shima ta yanka kanana(cube)kunna gas tayi a aza tukunyar tah ta dauko man gyada ta zuba da yayi zafi ta zuba markaden kayan miya da nama da kuma dankali tasa kayan su maggie da kayan kamshi irin su curry ta motsa da ya soyu sai tasa ruwan namanta data dafa kadan ta kuma zuba macaroni din ai kuwa sai gida ya karade da kamshi

Lami tace wai anty fuhutu kice yau zamuci girki shiyasa nake so kice zakiyi girki sabida nasan zaki zo mana da sabon abu.. murmushi kawai tayi tace inah alayyahun yake? gashi ta mika mata bude tukunyar tayi za zuba tare da motsawa sosai sabida koinah ya samu sannan ta rufe Ammice ta shigo tace wake mana delicious food haka tun kan musa a baki kamshi ya kosar damu... lami tace Ammi autarkice ...dama na sani badai Zainab ba sai dai autata dariya tayi tace inah kwana ammi ta amsa mata da lafiya qalau sannu da aiki yawa ta fada tana sauke abincin juyashi tayi sosai tace lami dauko kulolin a zuba daukowa tayi ta mika mata ta zuba sukayi setting dining table tare da kimtsa kitchen din sannan tace tau mun gama komai koh sai kuma jiran mayan baki murmushi lami tayi tace kina sokanar Ammi koh.

Hmmm kawai tace ta fita palour ta shiga ta tararar da su zainab,Ammi, Ahmad da kuma yazid a zaune tace breakfast is ready..., yaya Ahmad ya kyaleta yace kamar kin san yunwa ta kusa ta kashe ni Abba da yake shigowa yanzu yace "waya hanaka zuwa ka girka"gaba daya suka dube sama in da Abba yake daukowa tare da kwashewa da dariya ban da Ahmad inah kwana abba na fadah yana yatsine fuska murmushi abba yayi yace lafiya qalau yaya Ahmad

Yaya Ahmad da abba ya fadah ne ya bawa Ahmad dariya daga nan kowa ya gaida shi ya amsa sannan suka nufi dining table gaba daya tashi Zainab tayi za tayi serving..,fuhutu tace barshi yaya ni zanyi serving komawa tayi ta zauna ita kuma ta tashi daddy ta fara sawa sai Ammi sai kuma ta zubawa sauran itama ta zubawa kanta ta zauna sai kuma akayi shuru daga nanan...

Bayan kowa ya gama cin abinci aka dawo palour Abba ya dubi Ammi yace "yaushe Mujahid yace zasu sauka koh ba yau bane? tace yau ne mana wai karfe 11....yace ok ni zan wuce office Ina da patience"tace toh Allah ya kai lafiya..., Amin ke ba zaki school bane yau?tace ka manta yau public holiday ne..,mantawa nayi shiyasa toh sai na dawo ya fada yana daukar jakarshi

fuhutu tace "Abba kawo jakar na kai maka mota" yace toh autana gashi ya mika mata jikar gaba daya suka fito zuwa rakiyar shi ya dubi Ahmad yace ka sameni office anjima yace toh..,daga nan ya shiga motar shi zai tafi kenan fuhutu tace Abba ya maganar motana?

Yace karki damu tana kan hanya kinji koh tace toh ya jah motar shi ya yafi suka koma ciki..., yazid da Ahmad suka tafi dakin su while su Ammi suka zauna a parlour suna hira...,suna cikin hakane wayar fuhutu tayi ringing dauka tayi tare da barin gurin ta nufi dakin ta tana cewa.

"Hello bestie ya kike, tace Lafiya qalau Alhmdllh kina gida dai koh?tace eh,tace toh gani nan zuwa, tace ok.

Zamanta kawai tayi bata koma parlour ba data gaji da zaman ne ta kwanta daga nan kuma bacci ya dauke ta..., Cen cikin bacci taji Kamar ana Kiran sunanta farkawa tayi tana sallati tace "Jiddah kasheni zakiyi, dariya tayi tana cewa me zai sa na kashe ki bestie,tace ba dole nace haka ba kina kirana kamar kurmace ni maimakon ki tadani a hankali tace

Toh sorry oyah tashi mu tafi duban ta tayi tace "inah kuma zamu nifa na gaji kuma su yaya Mujahid sun kusa sauka so ki bari kawai su zo sai mu tafi duk inda zamu.., Jiddah ta zauna kan gado tace toh shikenan..

Fuhutu ta tashi tace "bari na dauko maki cake kici kamun su zo ta fada hadi da fita daga dakin.., ba'a wani jima ba sai gata ta fito da cake din a plate da kuma drink tace gashi.., Jiddah ta dauki cake daya tasa a bakin ta tana ci,fuhutu tace kun gaisa da ammi? Jiddah ta harareta tace da bamu gaisa ba ai ba zaki ganni a dakin ki ba,fuhutu tace yi hakuri malama dariya sukayi gaba daya daga nan kuma suka ci gaba da hirarsu da baya karewa.

************************

Ban san ta inda zan fara baku hakuri ba wallahi na san nayi laifi kwana biyu banyi updating ba abubuwa ne suka mun yawa amma ga wannan kuyi hakuri 🙏dashi

Pressing that little star⭐️ below won't take anything from u so please don't forget to help me change the colour.thank you all for the love and support even though the votes are not impressive😫

Vote
Share
And
Comment

Love you all😍😍😘😘

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now