22

325 36 7
                                    

Zulfa'u tace"da kuwa ta bani cause that will be better for the both of us"fuhutu tayi murmushin bakin ciki tace"yanda kike mana magana kamar wasu yayanki,i thought by now har kin karbe turaren ai"tace

"Kina tunanin ba zan iya bane? fuhutu ta saki hannun little tace"toh kiyi sauri ki karbe karmuyi wasting time dinki mana"ta fada tana tura mata jiddah kusa da ita, har zata fizge turaren jiddah tayi saurin rike mata hannu fuhutu ta wanka mata mari mai zafi,ta kuwa fasa ihu rike da kunce ai kuwa da sauri fuhutu ta dauki little jiddah kuwa taja masu Carter dinsu suka bar gurin da sauri .

Rike da kunce take tana kallon hanyar da sukabi har su raudah suka zo suna tambayarta abun daya faru,ba tare da tace komai ba ta rabasu ta wuce abinta rokon Allah take ya hada ta dasu sai ta masu abunda ba zasu taba mantawa ba, raudah tace "Wai meya faru da ita ne,itace fah tayi wannan ihun"mamah tace"ita dai ta sani mutun sai mugun bakin hali kamar ba yayarmu ba,komai nata is different shiyasa yayah mujahid ke mata walakanci everytime"daga nan kuwa ya cigaba da shopping dinda yakeyi,wadan da suka zo kallo kuma suma suka cigaba da harkokinsu.

**********
Dariya ce ta kwubuce masu yi kawai sukeyi ba kakautawa, jiddah tace"sannu uwar zafin hannu shine kika bawa diyar mutane mari koh?tace"the girl is too rude is better we teach her some lessons"

"Ni dai kiyi sauri mubar gurin nan kar mu shiga hannu"fuhutu tace"hannu kam...ba wani hannu da zamu shiga tunda ba wanda ya ganmu lokacin da muke fada,kuma ai baki sani ba kamin na mareta ai make sure ba wanda ya ganmu so worry not"

Abubuwan da suka kara ba yawa daga nan suka tafi gurin biyan kudin aka masu calculating suka bada kudin,har suka dawo gida dariya abun yake ta basu yanda suka gudu kamar wasu yara,basu bawa aunty hanifa labari ba sabida sun san zata masu fada ne so, little kawai suka sauke a gida tare da nashi shopping bag din, jiddah ta wuce don tayi dropping fuhutu,tsayuwar motarsu yayi daidai da fitowarshi daga cikin gida zashi masallaci dan sallar magariba.

Tsaye yayi yana kallon motar jira yake su fito ya tabbatar da abun da yake gani, jiddah tace"mun shiga uku"fuhutu ta daure fuska tace"ke dai kika shiga uku ba ansan da fitowarmu ba meye kuma abin tsoro wallahi ke kike saka Yaya mujahid yana raina mu"dariya ce ta kama jiddah"yayan ne kike ciwa ya raina mu toh ai sai kije ki mare shi koh dan naga kiyi training a fuskan yarinyar nan yanzu kin iya mari so meye abun tsoro"fuhutu tace"rufa mun asiri kema kinsan gaba da gabanta aljani ya taka wuta,idan za wanye lafiya acen nan kam ba ma sai na fadah ba"

"Nidai ki fita am going kinga dare yanayi koh"har zata amsata sukaji knocking a kan window glass din motar da yake motar tana da tainted,kuzo kuga idanun jiddah kamar zasu fadi kasa fuhutu tayi saurin fitowa daga motar gaba daya, jiddah kuwa ta sauke glass dan ba yanda za'ayi tafito sabida side dinta yake a tsaye

"Yaya ina wuni"suka fada a tare,bai amsa masu ba yace"daga ina kuke?ya fada ya kallon jiddah a shagwabe tace"shopping muka tafi kuma ai we took permission before going out"baki sake yake kallonta kamar wani sha katafi fuhutu kuwa ikon god kawai take kallo,gani yayi ta mai kyau sosai haskenta kamar ma kara fitowa yayi saurin daure fuska yayi yace"the last time I checked you didn't come to me looking for permission to go out,kuma dai naga nina saka dokar nan so meyasa baku zo gurina dan neman permission ba kukaje gurin Ammi da daddy? sukayi tsuru,tsuru ya dubi fuhutu yace"wuce ciki kamin raina ya bace"ta wuce tana turo baki .

Ya maida duban shi gurinta ,kanta a duke tana wasa da hannunta kwantar da murya yayi yace"Dadah meyasa ba kya jin magana ne dan na hanaku fita shine kuka bita bayan gida kuka tafi koh"tace"toh kayi hakuri ba zamu sake ba i promise"

"Toh yanzu ki shiga ciki kinga sallah za'ayi zan shigo anjima,I want to talk to you ok?ta daga kai ba tare da tace komai ba yace"that's good"tare da wucewa ya nufi masallaci bata san lokacin da ta sauke ajiyar zuciya ba indai tana tare dashi jin take kamar wata mararar lafiya duk jikinta yabi ya mutu,ga wani abu da takeji a cikin ranta game dashi daya wuce na Yaya da kanwa, ikamar da aka tada ne ya fargar da ita daga tunanin da takeyi da sauri ta fito daga cikin motar ta shiga gidan.

**********
Basu suka gama meeting da turawan da suke so suyi partnership dasu ba sai gurin karfe biyu na rana,koda suka gama gaba daya a gajiye suke sallah suka somayi kamin sukaje restaurant din company suka ci abinci suka koma office khalifah yace"muje gurin daddy mana naga kamar yanzu ya dawo shima so his in the office"Abdallah yace"Allah dgai yasa lafiya"

"Amin"khalifah ya amsa mai sannan suka tashi suka nufi office din gm, secretary dinshi suka gayawa ta masu iso sabida komai akan tsari yake,ba dan kawai suna matsayin Yaya a gurinshi ba zaisa idan sunzo su shiga ba tare da neman izini ba,tace masu yana magana da mutane su bashi few seconds yanzu zai gama dasu,bayan mutanen sun fito suka shiga da sallama ya amsa masu kuwa a natse "daddy barka da hutawa"da fara ya amsa masu.

"Barka dai khalifah ya aikin naku "ya tambaya"lafiya qalau Alhmdllh"

"Toh madallah"daga nan kuma kowa yayi shuru,maza da jan aji ashe dai a nan Abdallah ya koyo miskilanci sai daya dauki mintuna kamin ya gyaran murya yace"dama abun da yasa nake neman ku shine....,

__________________________


Mu hadu a next page domin jin meyasa daddy ke neman su

Su zulfa'u ansha mari fah

Vote
Comment
Share
And
Follow




                   Mairo❤️

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now