30

292 36 6
                                    

Rabbana Hablana min azwaajina wadhurriy-yatina, qurrata 'ayioni wa-jalna lil-muttaqeena Imaama

vote

Sati daya kenan da zulfa'u tazo gurin fuhutu ta tarar tana bacci,bata koma ba itama fuhutun bata nemeta ba kowa harkan gaban shi yakeyi,fuhutu ce zaune tana duba littafinta da yake sun kusa fara exams din seconds semester na 300level gaba daya kwakwalwarta tayi charge tana karatun kaman batayi a zuciyata cewa take Allah sarki besti ana can calfornia ana cin amarci.

Bayan ta dan samu  ta karanta iya abubuwan da take ganin sunr da muhimanci sai ta rufe littafan ta ajiyesu,sannan ta nufi kitchen domin yiwa khairinta abinci dan lokacin dawowan shi daga office ya kusa gaba daya kwanakin nan jinta take kamar bata lafiya wasu abubuwa takeji da bata saba jiba kwai dai daurewa takeyi,bayan ta dora sanwa ne ta dawo parlour ta zauna tare da mike kafafu ta dauki ragowar hollandia data ajiye dazu tana sha.

Haka kawai taga mutun a kanta a tsaye ba sallama bakomai duk data tsorata amma sai tayi kamar bata san da mutum a gurin ba,kare mata kallo tayi ta wutsiyar ido a ranta tace dani kike zancen dan zako ki shekara atsaye gurin nan,kara lafewa tayi a jikin kujerar tare da mayarda hankalinta akan drama da take kallo.

Hushi ne yazowa zulfa har wuya dan tasan cewa ta ganta amsata daine baxatayi ba "kee"zulfa'u ta fada cike da gadara kin amsata tayi saima kara kunkuade hollandian takeyi tana santin karya "dake fah nake magana" zulfa'u ta kara fada tana dawowa gaban fuhutu kallonta tai tace "Lafiya dai koh?

"Lafiyarce takawo haka ai" ta fada cike da ganganci ta kara da cewa "kuma nasan kin ganni tun dazu a tsaye amma kikayi kamar baki ganni ba"fuhutu tace "duk musulmin kwarai sallama yakeyi kamin ya shiga guri koda kuwa dakinsane da shi kadai ke zama a ciki,toh taya kike ganin zan amsa maki ba ba bakiyi haka ba dan the last time I checked nan ba gidan kafirai bane"ta fada a natse ba tare data koda kalli kurar data kwasota ba,kitchen ta domin duba abincinta

Zulfa'u kam baki ta saki galala tana kallonta lallai yarinyar nan tama ce wani abu me take nufi kenan, bata da tarbiya ranta ne ya kara baci tabita har cikin kitchen din tace "wlh ki fita idona na rufe har ni kike cewa mararar tarbiya "dariya ce ta kama fuhutu yanda take ta cika tana batsewa wai ta kirata marar tarbiya amma sai ta kanne tace "yanzu dan Allah ko kunya bakyaji yanda kika zo dinnan kike wani ciki kina batsewa saboda neman rigema,dan idan zan iya tunawa tunda aka kawoni gidan kofar part dinki idan dai bai zama doleba ba  zuwa nakeyi amma ke har kinzo ba adadi sa'anan duk zuwan da kikeyi banga amfanin shiba ko daya"

"kin san me zulfa?bata jira ta amsa ba ta cigaba dacewa "bana son rigima Allah lafiya ma banida shi, other half ya kusa dawowa bana so yazo ya sameni ina abunda bai kamace niba,dan Allah ki fita" fuhutu ta fada tana nuna mata hanya tace

"Zan fita amma wallahi kisani zan dawo"ta fada tare da buga kofar da karfi sabida tasan idan Abdallah ya sameta a gurin wai kuma tana tadawa matarshi hankali ba gaira ba dalili toh kuwa ba zataji dadadi ba.

Amma wallahi Allah kadai zai hanata koyawa fuhutu hankali wato marin data mata a shopping mall da kuma wanda ta saka momy ta mata duk ta manta "hmmmm"  idan taki ramawa to bata ciki zulfa'u ba, hahaha wasa farin girki aka ce

Wunin ranar gaba daya a cikin rashin jindadi tayi shi ba wanda ya isa ya hanata gyarawa fuhutu zama a gidan nan wlh koh khalifah bai isaba balle har azo ga Abadallah.ita kuwa fuhutu daker taga ta kare girkinta dan har ga Allah batada lafiya,bayan ta gama taje ta waso ruwa ta dan shirya jikinta sannan ta samu guri ta dan kwanta.

Da yake yaue su Abdallah sunyi meeting sosai da mutane so basuyi saurin tashi daga aiki ba sai gurin karfe 6 har da rabi,tare suka shigo gidan shida khalifah kowa ya nufi part dinshi don kimstawa kamin a kira sallar magariba,gaba daya parlorn ya dauki sanyi gashi kuma da duhu,mamaki ne ya kamashi dan yasan cewa idan dai tana gida wutan a kunne yake,

Ida shiga dakin yayi gani yayi kamar mutun a kwance kan kujera tana karkarwa aikuwa da sauri ya saki jakar dake hannun shi ya nufeta,jijigata ya shigayi cike da tashin hankali ta kuwa bude idonta daker a galabaice

"Cikina ke ciwo"ta fada a wahalce ai bai ma tasaya jin karin bayani ba ya dauketa yayi waje da ita hankali tashe yana kwalawa maigadi kira,mota ya sakata gidan baya ya shiga mazaunin driver ya jata da karfi saura kadan ya bige maigadi

Khalifah da tunda yaji Abdallah yana kiran maigadi murya ba a natse ba hankalinshi ya tashi yacewa zulfa'u "ba yayanki bane ki daga murya a waje"tace

"Shine"a tsorace aikuwa ko alwalar da yakeyi bai ida ba ya fito,fitowarshi tayi daidai da ficewar Abdallah daga gidan,ganin idan ya tsaya tambayar abunda yafaru bata lokacine yasa shi,shiga mota shima ya fita aguje yabi bayan dan uwanshi.

Cike da rudani zulfa'u ta tambayi maigadi abin daya faru yace shima bai saniba yadai ga maigida ya fita da hajiya rai a hannun Allah kamar ma ta mutu yake gani nan take hankalinta ya tashi Allah dai yasa bata gayawa Abdallah cewa ta shigo gurinta ba,daker ta iya yin alwala yayi sallah ta kira wayan Khalifah dashi Abdallah duk ba'a dauka,ta khalifah ma daga baya ta tsinceta akan gadon dakinshi.

Shikuwa Abdallah suna fita ya nufi private hospital daita cikin sauri kuwa suka karbeta,bayan an shiga cikin wani daki daita ne ya nemi wayarshi don ya kira yan gidansu amma ya lalaba baijita ba,sai lokacin ya tuna cewa gurin daukan fuhutu ne ta fado daga Aljihun gaban rigarshi,guri yasamu ya zauna a daya daga cikin kujerun dake gurin

Dagudu khalifah ya fado cikin reception din asibitin hankali tashe,dan tunda yaga ya nufo asibiti yasan cewa fuhutuce ba lafiya,har zai tambayi receptionist din sai ya hangi Abdallah a zaune dafe dakai.

——————————————
Kuyi voting da commenting dan girman Allah
Vote
Comment
Share
And
Follow
Nagode

Mrs umar

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now