9

342 48 3
                                    

MARYAM❤(marmiee)

Tanaji a jikinta kamar ana kallonta shiyasa ta kasa cin abincin yanda ya dace gashi ya mata dadi,ta kuma kasa daga idonta taga waye ke mata kallon kurulla haka,gaba daya ta takura sai zagaye take da spoon din akan abincin ta kasa kaiwa baki.

Ammi data lura da yanayin da jiddah take cikin sai tayi tunanin kunya takeji duban fuhutu tayi ba wasa tace"ke tashi ku shiga ciki ke da jiddah naga ta kasa cin abinci kamar kunya takeji", "kunya kuma Ammi?ta fada tana kallon jiddah "zaki tashi koh sai na bata maki rai"Ammi ta fada rai a bace tashi tayi tana zubure baki ta dauki abincinta tayi gaba,ita kuwa jiddah albarka take sawa Ammi a cikin ranta daukar nata tayi itama tabi bayan fuhutun, bayan sun wuce ne ta girgiza kai tace "ayi yaro da shegen musu mstww" sannan ta cigaba da cin abincinta.

Har ta bulle kallonta yake,amma dai Ammi bata mai adalci ba yana cikin jin dadin shi aka katse mai,duka da haka yafi tunda ya lura a tsarge take tun dazun bazai so ace ta kasa cin abinci akan shi ba,daga nan ya dauki spoon din ya fara cin abincin shi.

Suna shiga dakin suka zauna ajiyar zuciya jiddah tayi sannan ta shiga cin abincinta ba tare da ta damu da kallon da fuhutu take mata ba na tuhuma "meya hanaki cin abinci a dining dan na san ba wani kunya bane cause if I could remember this is not the first time you are eating together with everyone in this house"shuru ta mata sai data gama sannan ta dube ta tace

"It's nothing kawai I don't feel like eating cikin mutane"ita dai fuhutu bata yarda ba cause ta san halinta duk abinda yasa ta kasa cin abinci a gaban mutane to babba ne "hmmm"kawai tace ta dauki wayarta tana dannawa ita kuma jiddah ta kwanta.

Suna cikin hakane dakin yayi shuru wayar jiddah tayi ringing dauka tayi ta kara a kunnenta "toh gani zuwa" kawai ta fada ta kashe wayar ta dubi fuhutu tace "bestie anty hanifah ta kira tace nazo na raka su kasuwa suyi sayayya kin san zasuje umarah"ta fada tana gyara gyalen ta "ok toh sai kin dawo ki gaida mun da Hajiya Kice nayi missing dinta kuma sai nazo mata bankwana"hararar ta tayi tace

"Alquran baki isa ba tare zamu idan ba haka ba,ba inda zani"ta koma ta zauna fuhutu kuwa kallon bakida hankali ta mata tace "kiran Hajiyar ne ba zaki ba? Tace "shi sosai idan har ba zaki tashi mu tafi tare ba"daker dai ta yarda ta cenza kaya suka fito.

Palourn ba kowa sai TV daketa magana shi kadai dakin Ammi suka nufa fuhutu ta mata bayani ta masu sai sun dawo tare da ce masu su gaida mata da Hajiya sai tazo, fito warsu daga dakin Ammi yayi daidai da fitowar mujahid daga part dinshi fuhutu kadai ta lura dashi yitayi kamar bata ganshi ba tayi gaba abunta, ita kuwa jiddah idonta na kan waya tana tafiya so bata lura dashi ba,shi kuwa da yaga haka sai ya tsaya kan hanya.

Sai jin tayi ta bugi mutun dafe kanta tayi dan kuwa bugun ya mata zafi,dagowar da zatayi taga yaya mujahid ne haba ai kuwa jikinta ya fara makarkata ga hawayen daya cika mata ido ne ya sauko kan kuncen ta, gashi kuma ta kasa magana balle har ta bashi hakuri addu'a take a ranta Allah ya kawo fuhutu ta ceceta,shi kuwa kura mata ido yayi, yana jiran tayi magana amma taki tayi sai mutsu mutsu ta keyi tsoro da fargaba duk ya cikata dariya ma abun yaso bashi.

Gyaran murya yayi tare da gyara tsayuwar shi yace "dadah me yasa kike danna waya idan kina tafiya baki san ba kyau bane? "na-sa-sa-sani" ta fada cikin inina da tsoro, dariya ce ke cinsa amma ya danne yace "ina zaku" har zata amsashi fuhutu da take gurin tun dazu tana kallonsu tayi gyaran murya amma hakan bai sa ya dubeta ba da taga haka sai tace

"Jiranmu fah akeyi kin zo kin tsaya a nan kizo mu tafi mana"duban ba kya ganin ya tare hanya tayi mata, ba tare daya kalleta ba yace " tunda ba zaki amsaniba ki koma ciki idan lokacin zuwanki gida yayi ni da kaina zan kaiki" mai makon tayi magana sai ta fara kuka,wani irin bakin ciki ne ya Kama fuhutu ji take kamar taje ta shako wuyanta dama jiddah akwai baki amma sai tsoro, tsoron ma yafi yawa akan mujahid.

Da taga cewa idan ta biye masu ranta baci zaiyi sai ta koma mota ta barsu a nan, shi kuwa gogan namu kallonta kawai yake duk abubuwan nan da takeyi sha'awa yake bashi ga kuma kamshinta daya cika shi, suna cikin hakane wayarta tayi ringing MY WORLD yayi appearing kan wayar karaf a kan idon shi take yaji wani abu yazo ya mai tsaye a makoshin shi, daya ga bata da niyar dauka yace

"Ki dauka mana" tana so tace mai kawai ba saita dauka ba Hajiyace take jiranta dama, amma data tuna da cewa idan baiji tayi magana da ita a waya ba bazai taba yarda ba sai ta dauki wayar tasa hand's free ai kuwa sai ga Hajiya cikin tana cewa "idan ba zakiba baby ki fada mun mu tafiyar mana kin barmu muna jiranki cikin inina tace "wallahi ina hanya na kusa isowa" Hajiya kuwa ba sake sauraranta ba ta kashe wayar.

Kafeta da ido yayi yace "meyasa baki gayamun cewa Hajiya ke jiranki ba"har zata bashi amsa ya juya ya fice yana cewa "a dawo lafiya kar kuma ki biyewa auta gurin shashanci dan na san halinta yau lafiya gobe babu"dariya maganar ta bata, ta kuwa dara dan ta san idan fuhuti taji toh za'ayi fitina babba"toh"tace sannan tabi bayan shi suka fita.

Gefen garden din gidan ya nufa ita kuwa ta nufi motarta,ta tabbatar da cewa fuhutu kasheta kawai ne ba zatayi ba, waya ta tadda tanayi sai murmushi take gefen mai zaman banza ta bude ta zauna data gama wayar kuwa koh kallonta batayi ba har ta tambaye ta meya faru key ta yiwa motar ta jata da karfi, ita dai jiddah bata ce komai ba har suka isa gidansu motar da akayi parking bakin gate din gidan sukabi da kallo kafin fuhutu tayi horn aka bude masu gate suka shiga.

Bayan tayi parking tayi saurin fita ta bar jiddah a cikin motar direct palorn gidan ta nufa da gudu tana cewa "my one and only Hajiya kina ina" su kuwa wayan dake cikin parlorn sun riga da sun gane wacece ke fadar haka idan aka cire mutun daya dake makakin yanda budurwa zata dinga kuwa haka sabida a yanda yaji muryarta ba yarinya bace har yaji ya tsane ta baya son macen da bata da natsuwa Hajiya cikin jin dadi tace "gani nan daughter na"duk dacewa aguje take sai da tayi sallama kamin ta shigo direct gurinta ta nufah tace "hajajuna ina wuni? Kin san nayi missing dinki kuwa sati biyu kenan banzo gidan nan ba shine baki tambayeni ba"ta idar a shagwabe Hajiya ta ce

"Fuhutu rigima ai nayita tambayar yar uwarki ke tace abubuwane suka maku yawa sabida kun kusa ku fara exams koh ba haka bane baby? Ta fada tana kallon jiddah data shigo tun dazun tace "hakane" hanifah tace "autan Ammi yau kuma ba zamu samu gaisuwaba? Da sauri ta juyo ta kallesu tace "Allah sarki Aunty hanifah sorry kin san idan ina tare da Hajiya manta kowa nakeyi"

dariya akayi gaba daya ta koma cewa"yaya Manir da aunty hanifah ina wuni? Sukace "lafiya qalau"da hanifah ta ga cewa basu lura da yayanta ba sai tace "baku gaida mutun daya ba"gaba daya suka hada baki suka ce "yana ina? Da hannu ta nuna masu kujerar da yake zaune fuhutu dake zaune daskarewa tayi ita kuwa Jiddah dake tsaye juwa taso kayar da ita, baki bude suke kallon shi ko wace ta kasa yin magana

Ba zan iya zama banyi updating ba so gashi kuyi hakuri dashi zanyi editing anjima insha Allahu
Share
Vote
Comment
And
Follow
Thanks 🙏

MARYAM(marmiee) 💖

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now