26

393 37 0
                                    

Sai gurin karfe 3 suka gama shiryawa sunyi kyaue abunsu kowacce da gyalenta mai dan girma idan ka gansu sai kace yan biyu,Dayake families din gaba daya sun zama daya yanzu su hajiya da Ammi ma sun tafi wankin amaryen tun dazun suka tafi so suka rage,wayan Jiddahce tayi ringing da sauri taje ta dauka sallama tayi cikin murya mai sanyi ya amsa mata " Ina wuni? "Lafiya qalau how are you doing?

"Am cool and you? "Alhamdulillah so ina waje Ina jiran gimbiyar tawa ta fito idan ta shirya"murmushi tayi a kunyace tace "gani nan fitowa" tare da kashe wayar "huhu sai ni kanwar mujahid baban soyayya wai Yayan da kike tsorone kikewa magana haka lallai ya iya soyayya" fuhutu ta fada rike da baki

"Toh meye ruwanki a ciki naga dai kema ina jinki kika kare taki soyayyar na samaki ido ne, dan haka a barmu musha abun mu ehe"dariyar mugunta fuhutu tayi tace "yoh dama waya hanaku ni banida case kinji yarinyar zakiyi bayani dai idan kika hadu da Aunty hamidah"

Wannan karo bata amsata ba ta wuce inda  ta ajiye jakar hannunta ta dauka ta fice,kishi ya motsa kenan hmmm gara ki saba tun yanzu fuhutu ta fada a ranta, nata tarkacen ta dauka itama tabi bayanta


**********
Kusan tare motarsu ta shigo unguwar tasu Jiddah,kowane ya samu guri yayi parking a bakin gidan Abdallah ne yayi saurin fitowa ya nufi motar mujahid,shima fitowa yayi suka gaisa Abdallah yace "babban yaya uba akace so gara nazo na kawo gaisu kamin ace an fasa bani auren" dariya mujahid yayi yace

"ai kam Kayi dabara  niyata nace na fasa dan akwai Wani tsoho da akayi sannarwa a Wani massallaci danayi sallah jiya cewa yana neman yarinyar dazai aura yayi ta hudu da ita kaga kuwa idan na bashi auta ai na taimaka mai koh" toka Abdallah ya sha yace "wata autar dai zaka bashi babban Yaya amma ba tawaba ai idan kaga ban aureta ba toh bana numfashi a doron kasa jinta nake har cikin jinina,kai gani  nake na fika kusanci da ita koh a hakan ma"dariya sosai mujahid yayi  yace "a gaban surukin naka kaki wannan maganar koh ka dauka khalifah ne a tsaye"

Daidai lokacin Jiddah ta fito da gidan kanta a kasa take tafiya tana boye hannuwanta dake dauke da Jan lalle dan ta san cewa yanzu haka hannuwanta yake kallo gaba daya sai ta tsargu karasowa tayi ta dubi Abdallah tace " Yaya Ina wuni?

"Lafiya qalau Bestien mu tana ina ne ?ya tambaya yana duba bayanta Jiddah tayi kamar bata fahimceshiba tace "wa kenan?fuhutu dake fitowa tace "Haba bestie meyasa kike son sashi sai ya fadi sunan bayan kinsan ni yake nufi"dariya tayi ba tare da tace komai ba ta nufi motar mujahid daya riga ya shiga ita yake jira,itama ta nufi ta Abdallah suka bi bayansu.

Wakar joe boy ceke a cikin motar wato "am beginning to fall in love" ba Wanda yake magana a cikin su haka suka yita tafiya,juyowa yayi ya kalleta "dadah na zaman kurame mukeyi ne?ya tambayeta cike da zolaya murmushi tayi ta sada kanta kasa "na rasa gane kanki idan kina tareda auta sai kiyita zuba kamar parrot amma idan kika zo gurina sai kimun shure, nifa am getting jealous nafison idan nayi magana a dinga amsa mun kinji?ya fada cikin natsuwa wayar shi tayi ringing my wife ya gani a screen din wayar

Sai da ya kalli Jiddah kamin ya dauki wayan "wifey"ya fada cikin kwanciyar hankali gaban jiddah ne ya fadi Allah ya shaida ya sani wata rana mantawa take da cewa yana da aure harda ya'a daga ganin yanda yake yiwa fuskar shi ta san cewa,magana mai zafice ake gaya mai maganar da yayice ta karshe ta kara tabbatar mata da abunda take zargi

"Kin san Allah hamidah idan baki kiyayeni ba ranki zaiyi mumunan baci,nace maki zanzo next month bayan an daura aure,illahm kuma ki kaita asibiti idan kuwa kika sake kika dawo nigeria then trust me when i say keda calfornia har abada"ya fada tareda kashe wayar shi  juyowa tayi ta kalle shi huci kawai yakeyi kamar wanda yayi gudun fanfalake

"Yaya kayi hakuri" ta fada tana wasa da gyalenta take yaji wata natsuwa ta shiga jikin shi murmushi kawai ya mata wanda daka ganshi zaka gane na bakin cikine

*************
"Kinji abin da yaya ya fada?ba tareda ya jira amsarta ba ya cigaba "wai zai bawa wani tsoho aurenki a maimakona"ta yamutse fuska " tsoho kuma?

"Eh mana"dariya tayi tace "kaima kasan ba zai yuwu ba it's never gonna happen so kwantarda hankalinka" yace

"Hankalin nan nawa kullum cewa akeyi ya kwanta bayan ni nasan cewa bazai taba kwantawa ba sai na ganki a gidana a matsayin mata ta tukuna then my mind will be a rest"

"Insha Allahu kuwa I'm going to be your wife nan da wata daya so worry not,Otherhalf naga kaman su yaya sun mana nisa fah"murmushi yayi "meye abun azarbabi a ciki we will catch up with them yanzun nan"ya fada yana  fizgar motar

*********
Fuskarta gaba daya ba annuri ba abunda takeyi sai harare harare,tunda salmah ta gaya mata cewa wadda Abdallah zai aura zata zo take baza ido taga ta inda zata fito,gaba daya ma ta matsu a gama wankin amaryan taje tayi abun dake gabanta,rauda ce a gaba suna biye da ita a baya bayan sun iso ne Abdallah ya kirata yace tazo ta shiga dasu gidan su kuma sukayi gaba.

Kurawa mutanen da suke bayan rauda ido tayi tana son tuna inda tasan su, da yake kuma sunada nisa dasu sai da suka matso kusa tukuna ta tantance suwaye "bala'i"ta fada a ranta cike da masifah abunda ta dade tana neman shine yazo ya sameta har gida,su kuwa gaba daya basu ganeta ba sabida makeup dinda tasha gaba daya ta cenza rauda ta kallesu tace "toh ga amaren" salma tace "sannunku Anuty fuhutu koh"ta fada tana nuna fuhutu daga mata kai tayi tane murmushi

"Yauwa ke kuma jiddah"ta fada tareda kallon Jiddah "eh" ta amsa "nayi kokari kuwa dan fuskar ku kawai zan iya shaidawa the last da kuka zo ga yaya zulfa"ta fada tana taba zulfa'u da hannu sabida yanda taga ta kura masu ido ba qaftawa

Kallonta Jiddah tayi take gabanta ya fadi kallon sani take mata,ita kuwa fuhutu ba abunda taji sai da salmah ta dan kara taba ta kamin tace "sannunku"a dakile fuhutu tun daga nesa ta gane cewa batada mutunci dan haka jiddah ce kawai ta amsa gaisuwarta da nan suka samu guri suka zauna


—————————————-
Zulfa'u dai ta ganesu fuhutu
Fuhutu dai bata gane zulfa'u ba
Jiddah kuwa tana yiwa zulfa'u kallon sani
Mu kasance tare a page na gaba
Sannunku mutanen arziki ina godiya sosai
da votes da kuma comment Allah ya saka da alkhairi nagode
Karku manta
Vote
Comment
Share
And
Follow
Taku har kullum

                            Marmiee❤️

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now