6

381 37 0
                                    

Not Edited

Ammi ce ta shigo dakin ta tadda su suna surutun su basu ma san cewa ta shigo dakin ba ta dube su tace "ku dai abun fada baya Kare maku.., dariya sukayi gaba daya fuhutu tace "toh Ammi so kike mu zama kurame,tace aa kuyitayi dama zuwa nayi nace maki yayanku sun sauka yazid da Ahmad sunje su dauko su da fatan everything is ready,dariya fuhutu tayi tace

"Na san cewa ba zaki zo haka kawai ba Ammi sai saboda yaya Mujahid" ammi ta dan bata fuska tace "bana son rainin wayo fah auta kuma ki fito idan da akwai abin da ba'a gyara ba sai ayi daga nan ta juya ta fita ba tare da ta tsaye jin amsarta ba ta kyalle Jiddah tace "kin ga tashi mu fita kar muyi laifi sabida yanda Ammi takeji da yaya koni bata yiwa haka na fada Ina daukar gyalena dake kan gado

Keni gaba daya bana ganin laifin Ammi dan tana jin dadin danta zai dawo wlhi nima dai nayi missing din shi koh dan fada da yake mana idan yana gari" duban ta tayi tace "toh kuwa sai ki shirya dan kin sani idan yana gari bama fita yawo da yawa"

"Kanki akeji nidai tashi mutafi koh"fita sukayi daga dakin zuwa palour ta diba dinning table taga everything is set sai kawai suka cigaba da zama a palour fuhutu ta dube Jiddah tace wai ya Abdul ? Jiddah ta dube ta tace "hmm munyi break up jiya dafe kirjinta tayi ta zaro Ido tace u are kidding right?harara tayi mata tace

"Why would I be? wallahi dagaske nake, guy din is not serious tun yaushe nake cewa ya turo amma yaki Abbu har magana ya mun akan shi nace aikine ya mai yawa toh sai jiya na kara mai maganar shine yace mun wai shi bai tashi aure yanzu ba ni kuma nace bakomai Allah ya hada kowa da rabon shi"

Fuhutu ta mata kallon tausayi tace "but bestie da kin bashi second chance maybe zayi surprising dinki, kuma ma naga laifinki ne sabida ya dade yana cewa ki bari ya turo kikaki" murmushin bakin ciki tayi tare da cewa "ba zaki gane bane he's not serious Allah ai tunda yanzu na tashi ba sai ya turoba amma yaki wannan yana nuna cewa tun faro ba serious yake ba,shi abinda kawai yasa a gaba shine chilling mu dinga fita yawo every blessing day haba dan Allah idan ma abinda yake so kenan ai sai ya aureni muyi mai dalili koh? Amma yace aa toh me kike son namai fisabillilahi ta Ida maganar da hawaye a idonta

A take fuhutu taji hawaye ya wanke mata Ido tare dajin tsanar Abdul lokaci daya sabida halin daya saka bestin ta baiwar Allah zatayi magana kenan sukaji tsayuwar mota a harabar gidan da sauri suka share hawayensu suka tashi suka nufi waje tsaye sukayi suna jiran fitowar wayan dake cikin motar...

Yaya Ahmad ya fara fito sannan yazid yafito shima rike da baby(Elham) a hannunshi sai kuma wata kyakyawar mata farace amma daga gani ta hada da mayuka sabida farin ya zarce hankali ba zata wuce tsarar Zainab ba,tana da kyau iya nata..jalabiyace a jikinta mai kyau.

Jiddah zunguri futuhu tace "bestie rufe baki mana" harara tayi mata tace"ba dole na bude bakina ba"dariyace taso kama Jiddah amma ta daure tace "ni dai mu karasa mu gaidata kar muyi laifi"aikuwa Kamar sun sani sai ji sukayi ance "ku baku iya gaisuwa bane koh kuma gani kuke kun girma kunfi karfinku gaida mutane? aikuwa Kamar mazari haka jikin Jiddah ya dinga rawa dama tun suna yara itace tafi tsoron yaya Mujahid,wani bakin cikine ya kama fuhutu ganin yana musu fada a gaban matar shi.

"Yaya ina wuni andawo lafiya? Jiddah ta fada kamar wacce take koyon magana,juyowa yayi ya dubeta tare da kura mata ido na wasu minutes kadan kamin yace

"Dadah (sunan da yake kiran jiddah tun suna yara)yaushe kika koyi ranshi kunya kamar auta?tun dazo muka zo amma Kuk'a tsaye kamar wasu gumaka ya muku kyau,ke kuma ya fada tare da nuna fuhutu tunda baki iya gaisuwa ba sai kije boot ki kwaso sauran kayan dake ciki.

Duban shi tayi tace "to yaya ai Kaine daga zuwa sai masifa bestie zo muj'e tace tare da jawo jiddah.

"Ba ind'a zata ke kadai na sak'a, ya juya ya dube jiddah yace shige mu tafi idan ba zata yiba ta barshi.

Idan muka koma ta cikin gida kuwa Ammice a zaune tana cewa yaya yaxid "ina mutan California" yace "suna waje yanzu zasu shigo" tace"miko mun kishiyata mu gaisa mana mun dade bamu ga junaba" ta fada tana mikawa yaxid hannu, dariya yayi tare da mika mata ita.suna cikin haka sai ga su jiddah sun shigo itah da mujahid da Aunty hamida a bayan shi.

___________________________

I don't even know where to start🙏like am so, so sorry dan Allah ayi hakuri for not updating for long now but insha Allah I will update as fast as possible from now on don't forget to

Vote
Share
Follow
And
Comment

                      
                  

                   Marmiee ❤️

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now