14

324 40 12
                                    

Da kyar ta yarda tace zata rakata din bayan jan aji da komai, da suka gama cin abincin sai suka nufi mota da yake driver ne kawo fuhutu makaranta so bata zo da mota ba, jiddah taja motan ta suka fita daga school din

"Inda zamu ma baki fada mun ba kawai sai Jana kikeyi "bata tare da ta kyalleta ba tace "saidaki zanje yi mana "hararan ta tayi

"Namana kuwa ba na ci bane,idan kika Kai ni su da kansu zasu maidani"bata sake ce mata komai ba ta cigaba da tukinta har suka kai gidan,horn tayi maigadin ya fito har zai tambayesu gurin wanda suka zo sai yaga jiddah

"Hajiya ina wuni " ya fada ya rusunawa jiddah ta ba'ata rai "wai ba nace ka daina ce mun hajiya ba,ka kuma daina rusuna mun ka girmeni fah koda kuwa baka haifeni ba" tashi tsaye yayi tare da sosa kanshi "ayi hakuri hajiya"girgiza kanta tayi tace ya bude mata gate tunda ta lura ba zai iya dainawa ba.

Bayan sun shiga tayi parking suka fito, fuhutu sai yaba kyaun gidan takeyi dan wannan kam yafi nasu girma ba kadan ba,ta dubi jiddah tace"bestie wai ina ne nan na fa fara tsorata"

"Ke cool down dan Allah gidan su aunty hanifah ne fah" ta zaro ido tace "haba kin san lokacin da ake neman aurenta banxo ba, lokacin data haifi little daddy ma kin san nayi tafiya" jiddah tace "yeah I know all those things muje ciki nazo daukan little daddy ne ma" daga nan suka nufi cikin gidan sallama sukayi ba wanda ya amsa,sai kawai suka shiga.

Shigowansu yayi daidai da zuwan little daddy a guje da Abdallah a bayan shi yana cewa"come on little one ka tsaya kaci abinci mana am going out"turus yayi ganin mutane a tsaye a cikin parlorn ,kallon kallo suka tsaya yi a tsakanin su, daga baya yayi gyaran murya yace "sannunku ku zauna mana, ina zuwa na kira matan gidan"ya fada kamar baya son yin magana.

Daya daga cikin gujerun suka samu suka zauna,bayan sun zauna ne suka kwashe da dariya jiddah tace"wai kin ga fuskan ki some minutes ago kuwa kamar wadda tayi sata aka kamata"dariya tayi tace "bari kawai shi little daddy ma da yayi causing abun ya fita abun shi"suna cikin maganar ne mamu ta shigo parlorn da fara'a a fuskan tan

"Aa jiddahn hajiya kece a gidan namu"rusunawa sukayi "mamu ina wuni"

"Lafiya qalau ku tashi mana"tashi sukayi daga rusunawan suka zauna mamu ta dubi fuhutu tace "wannan kamar yar gidan lubna yakub koh " a kunyace fuhuta tace "eh ita ce"

"Ai kuwa ga kamar nan na gani fuskarku daya,rabona da lubna tunda muka hadu a calfornia auren yayanku mujahid"murmushi kawai fuhutu tayi daga nan jiddah tace "mamu little daddy nazo dauka "

"Dama na san cewa ba abun da zai kawoki gidan nan sai danki tunda hanifah bata nan"kanta ta dukar "aa wlh mamu ba haka bane"dariya tayi tace"toh naji bari a shirya shi sai ku tafi dama munyi waya da baban shi ya gayamun, hanifah kuma tace nan da kwana biyu zasu dawo koh?tace "eh mamu"

"Toh shi kenan ina zuwa"ta tashi ta fita parlorn , mintuna kadan mai aiki ta kawo masu abinci ta ajiye kan dining tace "hajiya tace ga abinci kuci" suka ce a kosha suka amma sai da mamu tazo ta saka su sukaci bayan sun gama ne suka ce mata zasu tafi,tasa aka dauko masu little daddy an shirya shi yayi kyau da karamar trolley dinshi na kayan wasa da kuma na makulashe,ta kuma basu manya manyan jaka kowa daya daya,godiya sukayi tace

"Bana son haka fah,ba godiya a tsakanin uwa da yayanta fuhutu kicewa mamanki zamuyi waya sabida idan ban manta ba ina da numbern ta,zumuncin mune da yaja baya ku gai da gida ayi driving a hankali kuma"suka amma da "toh"daga nan ta musu rakiya har bakin motar ta masu Allah ya tsare suka fita tare da daga mata hannu.

***********
Abdallah kuwa bayan ya fice daga parlorn murmushi yayi tare da sauke ajiyar zuciya,ji yake kamar an sauke mai wani katorn duste a kai ,yarinyar da yake tunanin ina zai ganta itace tazo har cikin gidan su,lallai Allah mai iko sai kuma ya tuna da kallon da yaran suka dinga mai kamar sun ga aljani ya kwashe da dariya,daga nan ya nufi bangaren mamu da sallama ya shiga parlorn ta,ta dago daga abun da takeyi ta amsa mai tare da cewa

"Yaki yaci abincin ne koh?dama na san ba ci zaiyi ba wasa kawai yakeso yayi dashi"

"Yaki yaci gujeguje kawai yaje sani kin yi baki ma suna main parlor" tashi tayi daga zaunen da take tace "baki kuma?yace "eh jiddah ce kanwar manir"

"Allah sarki na san da zuwanta kuwa manir din ai ya kirani yace bai samu numbern ka ba"

"Allah sarki"kawai yace ita kuwa ta fita daga parlorn ta nufi main one din,shima dakin shi ya nufa dama yana niyan fita ne ya tadda ana rigima da little daddy akan yaci abinci amma yaki sai wasa yake dashi,shine yace zai bashi da kanshi amma abun ya faskara,car key din shi ya dauka ya fita daga gidan.

**********
"Kin san Allah idan kika fita daga gidan nan ranki zaiyi mugun baci"ya fada a tsawace kallon ai kuwa yau ake yinta ta mai tace

"Wai abban mu mekake nufi dani ne sati uku kenan da dawo wan mu, kace ba zan koma gidan mu ba a nan zan zauna i didn't not complain yanzu kuma ana bukin junior sister na kace ba zanje gida na kwana ba, for what?kowa fah na cen ni kadai ce bana nan haba a ina aka taba haka?

"Hamidah kina da hankali kuwa ni kike daga wa murya?toh nace ba zakije ki kwana ba yini kawai na yarda kiyi,idan ba haka ba you aren't going anywhere kinji na gaya maki"ya juya a fusace ya bar dakin baya son musu a rayuwarshi amma hamidah ta tsiro wannan halin sai ta dinga yin abu kamar ba wayaya ba.

________________________________



Thanks for reading 🙏
Vote
Coment
And
Share

Marmiee❤️

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now