19

286 38 2
                                    


Dadadare hanifah ta tasa manir a  gaba sai ya gaya mata abunda suke boyewa,yace ba zai fada ba sai data mai dadin bakin tukuna ya fada mata,taji dadi sosai amma Kuma wani gefen bataji dadin dayake neman zubawa zulfa'u kasa a ido ba,ko makaho ya duba ya san tana sonsa amma shi yayan nasu yayi kamar bai san tanayi ba

*******
Kowa yana zaune akan dining table ana cin abincin dare mutum daya ne kawai babu kuma an san cewa ba dabiar sa bace haka,amma sanin halin shi da akayi ne yasa ba wanda yayi niyar neman shi,sunyi nisa a sosai a cin abincin tukuna ya shigo su daddy da uncle tukur ya gaida tare da iyayen shi mata,kan yaja kujerar da take kusa da momy ya zauna

"Rufaida zubawa yayanki abinci"momy ta fada "toh" ta amsa tare da tashi ta dauki plate ta zuba mai iya wanda ta san yayan nata zai iya cinyewa,ta ajiye a gaban shi tare da saka mai spoon.

Yace "ruda(sunan da small daddy ke kiranta)kin dawo kenan" tace "eh yaya" yayi nodding kanshi daga nan ya fara cin abincin,sai da yayi rabi a abincin sa kan daddy yayi gyaran murya ya dubi Abdallah yace

"Kuzo ku sameni a office gobe kai da khalifah we have something to talk about" ya amsa mai da zasu zo daga nan su daddy da uncle's suka koma parlour su ummi ma suka bi bayan su ya rage daga Abdallah sai rufaida da zulfa'u akan table din, Shima bai wani dade ba yaxo parlorn ya yiwa su Mami sai da safe ya wuce

Bin bayan shi tayi da kallo,na biyu kenan ta rasa meyasa ta kasa cireshi a ranta duk da walakancin da yake mata dan ba zai ce mata bai ganta a zaune ba tsabagen miskilanci ne kawai,bayan ta gama ta tashi ta nufi gurin su Mami'n don taya su fira

********
Kira ne ya shigo wayarshi daya ga wanda yake kiranshin sai yayi dariya tare da daukan wayan "hello manir yanzu fah nake tunanin kiran wayanka sai gashi ka kirani"

"Ahh toh bari na kashe wayan sai ka kira tunda har kayi niya"manir ya fada da zolaya, dariya sukayi gaba dayansu daga nan manir yace" ranka shi dade koh za'a mun alfarma a sameni a office gobe akwai maganar da zamuyi"mujahid yace

"Mezai hana kuwa dama I also have something to tell you so ba damuwa zan zo insha Allahu"yace"toh ranka shi dade godiya nake a gaida mun da maman illham da Kuma Ammin mu"murmushi mujahid yayi

"Ban san yaushe na samu ranka ya dade a sunaye na ba but zakayi bayani gobe Ammi kuma kana da nurmbernta kunfi kusa so good night a gaida mun da small daddy"ya kashe wayan ba tare da ya jira yaji me zaice ba

Ajiye wayan yayi ya cigaba da aikin da yakeyi a laptop din shi dan bai koma aiki ba so yana so ne kamun ya koma ya tabbatar da cewa, all his materials for lecturing are ready,yana cikin hakane hamida ta shigo parlorn daka ganta ka san cewa daga wanka tafito,kayan bacci ne a jikin ta masu kyau tazo ta zauna a kusa dashi kamshi mayukan ta kawai take amma fah ba turare.

Mayukan ma ba laifi suna da kamshi mai dadi amma shi oga yafi son ta saka turare amma ina,kanta ta aza akan bayashi tare da sakalo hannunta ta gaban ta kwantar da murya tace

"Abbanmu it's bed time not working time this is 9:30"cire hannunta data saka a nashi tare da janyota jikin shi ya mata kiss a goshi yace"kin tabbatar ba lokacin aiki bane koh Kuma kina bukatar wani abu ne uhhhm"kara shigewa jikin shi tayi tace"toh mijina nake so a kusa dani koh ba zan samuba?

Zare jikin shi yayi daga nata ya kashe laptop din tare da maiyar da ita akan side chair table dake gefen kujerar da yake zaune,duk tana kallon shi daga nan ya kwashe wayoyin shi ya tashi tsaye ya dubeta tare da bude hannuwan shi yace "am all yours now " murmushi tayi tare da tashi itama,taja hannun shi zuwa cikin bedroom

"You need to take your bath first koh?ta fada tana zaunar dashi kan gado,daga mata kai yayi alamun eh tunani yake a ranshi abunda zaiyi ya dace koh bai dace ba,hamidah tana da kyau da tsafta,tana da biyayya idan taga dama sabida wasu lokutan bata da mutunci koh daga nan zuwa cen,dan har shi zata iya zabgawa rashin mutunci,amma wlh yana son jiddah yarinyar tun tana karama take burge shi,gashi ta zama cika kiyar budurwa idan baiyi sauri yayi maganar ba za'a iya mai kafa,gata Kuma da tsafta ga kamshi a koda yaushe dan duk lokacin da suka hadu tazo giftawa ta gurin shi ko Kuma yake mata magana toh sai yaji dadaden kamshi jikinta ta lallen da ya gani a hannuwanta ranan shi ya kara ingiza shi ya fada sonta.

"Abbanmu"hamida ta fada da dan kara,ya dan firgita "me kake tunani ne Wai wata biyu kenan cikin na uku da muka dawo najeria,bayan sati daya ka fara tunane tunanen, you're always in your thoughts na dauka kawai abubuwa ne na rayuwa amma yanzu na fara zargin wani abu dan Allah ka gaya mun gaskiya meke damunka"ta fada cike da zargi

Tashi yayi ya karbi towel din da take mika mai tare da yin murmushi yace"ummin mu you worry too much ba fah abun da yake damuna kawai wani aikine yakeyi a nan dana matsu mu gama,mu koma calfornia so kari damu ok?" Sauke numfashi tayi ta daga kanta ba dan ta yarda da abunda ya fada ba,ya mata kiss a goshi ya wuce bathroom

Ita ta san cewa akwai abun dake damunshi amma ta kasa gane koh meye shi,tunda basu da matsala a zaman aurensu idan ba lokacin da suka samu misunderstanding ba na zuwanta gida bukin kanwarta shima koma data dawo ai sun sasanta junansu,ita dai ta fara jin wani iri abu a game da wadan nan kananun tunane tunanen da yakeyi Allah dai yasa lafiya

Ya dade sosai a gurin wankan kan ya fito,ya fitowa ta taya shi goge jikin shi ta taya shi shafa mai tukuna ta miko mashi kayan baccin shi ya saka suka kwanta sai bacci,asuba ta gari

************
Tunda asubahi bayan ya dawo daga masallaci,yake kiran khalifah a waya amma yaki ya dauka abun har ya fara bashi haushi ace wai kana ta kiran mutun a waya yaki dauka,tsaki yayi tare da jefar da wayan kan gado ya cigaba da shiryawa cen sai wayan tayi ringing aikuwa da sauri ya dauka ba tare da ya diba sunan ba

"What the hell wai meke damunka ne nake ta kiranka kaki ka dauki wayane khalifah?ya fada cike da fada,ai kuwa a tsorace tace"Yaya nice" kwantar da murya yayi kaden "kice wa"ya fada tare da duba wayan sunan wadda ya gani ne ya kara harzuka shi tun kamin ta amsa yace "idan magana zakiyi dani ki sameni a side dina bawai ki dinga Kiran wayana ba,you are keeping it busy ina da important call to answer"ba tare da ya tsaya jin me zata ceba ya kashe wayar tare da yin tsaki ya cigaba da shiryawar shi.

Kuka ta fashe dashi mai tsuma zuciya ina ma zata iya cire shi a ranta data huta,amma ina kamar kara mata sonsa akeyi ta yiwa kanta alkawari cewa ba zata taba gajiyawa ba sai tasa ya sota kota halinyaya ne bata damu ba indai har zata samu nasara ya zama baya ganin kowa sai ita.

___________________________
Ina kwanan ku

Na san nayi laifi a mun hakuri dan Allah

Godiya nake

Vote
Share
Comment
And
Follow

                  Mairo❤️



Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now