Tallah

218 24 8
                                    

RAKIYAR SO!

Bismillahi rahamani rahim

~My story is totally fictional so please any resemblance to someone's past or current life then it's a coincidence~



1️⃣

Ke wace irin jahilace da ba zaki iya yin abun da aka saka ki ba every single day sai na dinga maimaita maki abunda zakiyi for Allah's sake haba" ya fada cikin fushi,ita kuwa koh a jikinta idan da sabo ta saba da irin wadan nan bakaken maganganun da yake mata.

"Kayi hakuri"kawai tace ta kwashe kayan breakfast dindata aje a kan carpet ta maida su kan center table din dake bakin gadon ba tare data tsaya jin abinda zaice ba ta nufi kofan fita daga dakin a tsawace yace

"Come back here"ta dawo tare da neman guri ta tsaya  kallonta ta yakeyi cike da tsana "who the hell is going to seave me?tai shuru bata amsa shiba kawai sai ta nufi abincin ta fara zuba mai iya wanda ta san zai iyaci,then ta koma inda take tsaye tsaki ya buga

"Get out of my room before I kick you out"ya fada a hasale ita kuwa cike da natsuwa ta fita daga dakin,bai san lokacin daya saki heavy sights ba,duk wanda ya sanshi yasan shi ba mai yawan magana bane amma tunda yarinyar nan tazo gidan nan she does nothing but makes him talk,wanda hakan sosai yake saka shi ciwon kai duk rayuwar shi mutanen da yake sakewa yayi magana dasu daidaiku ne sai gashi wannan tana neman zautar dashi

Kadan yaci abincin kusan za'a iya cewa tsakurar shi kawai yayi,wanka ya shiga a gurguje ya shirya,dan zuwa gurin training wayanshi ce tayi ringing gani wadda ke kira ya dauka yace

"Hey girlfriend"tace

"Hey boyfriend am outside fah ka shirya kuwa?

"Of course yes gani nan fitowa"ya fada tare da kashe wayan kayan da yake bukata ya dauka ya fita daga dakin,living room din gidan hajjace da momma a zaune suna kallo gaba daya hankalinsu yana kan tv,kamar kullum cikeda miskilanci yayi sallama duka suka amsa mai

"Chuchu fita zakayi ne?momma ta tambaye shi

"Yes am going for training"ya bata answer kamar bayaso tace "toh Allah ya tsare take care of yourself"

Yace "I will" tare da pegging dinta "hey" yacewa hajja yana daga mata hannu tsaki tayi tare da juya fuska alamun bata so,kuma tasan dacewa ganin damane yasa ya mata magana dan wata rana koh kallo bata ishe shiba juyowar da zatayi ta ganshi a gefenta "yadai amaryata" ya fada kamar bashi bane yayi maganar ta kara juya fuskanta yace "nidai ba shagwaba nace ki munba gaisawa zamuyi"

Azafafe tace "toh bana son gaisuwar dolene?

"ina kuwa ya zama dole matata tunda ba kya so zan tafi amma fah sai kin mun addua tukuna"

ita bata cemai komai bata kuma sake kallonshi ba,momma kuwa ikon Allah kawai take kallo da taga dagaske yakeyi baxai tafin ba gashi taga wayanshi sai kara take yana kin dauka sai tace

"Allah ya tsare ya bada sa'a ya saka a rage miskilanci and be a good boy"

"That's my grandma Allah ya karba and bye for now"ya fada yana fita da sauri daga sitting room din

"Ke kadai ce maganinshi hajja"momma ta fada tana dariya "ehmmm mijin nawa hukuma ne sai da dabara Allah dai ya shirya mana yayanmu akan tafalkin addini"

"Amin ya rabbi hajja"daga nan suka cigaba da kallon da sukeyi.

*******
"What took you so long ne wai?wata farar yarinya kyakyawa yar kwalisa ta tambayeshi bayan ya shigo motar murmushi kawai ya mata ba tareda ya amsata ba,duk da cewa tasan halin abokin nata na rashin magana amma hakan yana sosa mata rai sosai ko dan yana childhood friend dinta ne hakan ke damunta oho

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now