11

352 39 2
                                    

Sati uku kenan da dawowar shi daga India, sannan a cikin sati ukun nan sau biyu ya ganta ya kasa cireta daga cikin ranshi mamaki yakeyi yanda yarinya karama ta wuce da tunanin shi, yana zaune a office ne yana aiki sai kawai tunaninta ya fado mashi, khalifah da yake ta mai magana yaki amsashi sai kawai ya samu guri ya zauna yana kallon ikon Allah.

Daya ga tunanin ba mai karewa bane sai ya tashi ya isa gurin dispenser dake cikin office din, ya dauki kofi ya cika shi da ruwa ya zo kusa dashi yace"dude" yaga ba amsa ya koma maimaitawa yaga ba amsa sai kawai ya daga ruwan ya zuba mai akai, ai kuwa ya fargita sosai, dago kanshi yayi yaga wane takadiri ne ya mai haka duk da ya san cewa mutun daya ne zai iya.

"Khalifah wai meye hakane?"ba zaka iya mun magana bane sai ka zuba mun ruwa a jiki" dariya khalifah ya cigaba dayi ba tare daya bashi amsa ba,kanshi ya jijina ya nufe dakin dake cikin office din domin ya cenza kayan shi da ba dan khalifah bane da wallahi kowaye sai ya dandani gudarsa yau.

bayan wasu yan mintuna ya fito a shirye da alamu ma wanka ya sake sabida yanda yake haske da kamshi, kujerar shi ya koma ya zauna tare da jawo laptop yana dubawa ba tare da yace komai ba shima khalifah bai tanka mai ba hasali ma wayar shi ya dauka yana dannawa.

"Waya aka kawo ka kayi operating a nan ne koh kuwa aiki aka kawo kayi? Yaji Abdallah ya fada a fusace, ajiye waya yayi yana mai kallon banza yace "maida wukar mallam bani na kar zomon ba ajiya aka bani, sannan meye ruwan ka da aikina a company nan kai ka daukeni aiki ne? Da kake wani ce mun ba waya aka kawo ni nayi operating ba da yake kai tunani aka kawo ka kayi koh?

"Ban gane tunani aka kawo ni nayi ba?"ba aiki ka tarrar dani ina yi ba?

"Aiki kam ka keyi toh kayi sauri ka gama, ni kaga tafiya ta idan ka kare ka sameni koh kuma mu hadu a gida"ya fada yana daukar wayarshi tare da ficewa ya bar mai office dinshi,ajiyar zuciya Abdallah ya sauke ya san cewa gaskiya khalifah ya fada tunanin yakeyi tun dazun bai wani yi aiki sosai ba tun da yazo office yau.

Agogon dake manne a bango ya kalla uku da rabi daidai kenan lokacin tashi yayi mintuna tallatin kawai suka rage, toilet ya shiga ya dauro alwala sannan ya kashe laptop dinshi ya dauki car key da wayoyin shi ya fito yace wa secretary dinshi, zai wuce idan akwai files din da baiyi signing ba ta ajiye mai su akan table gobe idan yazo shine abu na farko da zai fara, tukuna ya fice direct office din khalifah ya nufa baya ciki sai kawai ya fita farfajiyar company nin daya daga cikin messengers din dake gurin ya kira ya bashi key din motar shi da wayoyin shi kuma ya nufi masallaci.

A kofar shiga masallaci ya tadda khalifah, so tare suka shiga bayan an gama sallah ne suna takowo Abdallah ya dube shi yaga baya da niyar mai magana yace "wai fushi kakeyi ne koh meye? "Idan ma shine naga ai ni ya kamata nayi fushi ba kai ba nida aka zubawa ruwa a jiki"

"Toh ai sai kazo ka rama,ko kuma kayi fushi kamar yanda nayi" Dariya yayi ya bugi kafadar shi"dadina da kai akwai saurin hawa wallahi idan ba haka ba yanzu me nace? Tsaki yayi tare da yin gaba abun shi, aikuwa me Abdallah zaiyi idan ba dariya ba, daga muryarshi yayi yace

"Toh yaya khalifah sai mun hadu a gida"mutanen dake a wajen company kallon su kawai sukeyi dama sun saba ganin haka a tsakanin yanuwan, motar shi ya nufa yana murmushi already an saka mashi wayoyin shi a ciki, sai kawai yabi bayan motar khalifah direct sai gida.

A waje yayi parking sabida zai sake fita, knocking yayi maigadi ya bude masa suka gaisa ya wuce ciki, little daddy ya tarrar a compound din gidan yana ball, tsaye yayi yana kallon yaron kayan dake jikin shi masu kyau dasu,shi mutun ne mai son yara shi yasa yanzu a koda yaushe ba yada wani tunani idan bana aureba sabida lokaci yayi daya kamata ace yana da iyali.

Yaron bai lura da uncle din nashi ba sai da ball dinshi ta gangara gurin kafafun Abdallah, yana daga ido ya ganshi ai kuwa ya danno da gudu yana "oyoyoyoyo"shi kuwa Abdallah dukawa yayi ya bude hannuwan shi yana zuwa ya daga shi sama suna juyawa,sai dariya sukeyi abun abin sha'awa da sukayi mai isar su sai ya tsaya yana sauke numfashi

"Amma dai daddy akwai nauyi dubi har na gaji daukar ka da nayi anya ba Wani abu mamu ke baka ba kana ci kai daya"

"Wani abu kam nake bashi kamar yanda na baka kana karami"yaji muryar Mamu tana fada a bayan shi, murmushi yayi "Mamu ina wuni? "Lafiya qalau ya aiki? "Alhamdullahi mun gode Allah"

"Toh daddy come down uncle yaje Yayi wanka kaji? Mamu ta fada tana mika mai hannu aikuwa yace ba zashi ba sai Abdallah yace ta barshi kawai ya nufi part dinshi dashi, a parlor ya sauke shi kan center carpet ya kunna mai cartoon.

Shi kuma ya shiga bedroom kayan shi ya cire, ya daura towel, direct sai toilet shower ya kunna yayi tsaye ruwan yana zuba daga kanshi har kasa,ya dauki mintuna 20 a haka kafin ya fara wanka, bayan wasu mintuna ya fito daure da towel daya kuma a hannu yana goge jikin shi.

A gurguje ya shirya ya fito parlor, small daddy ma already yayi bacci sai ya dauke shi suka fita,main parlorn gidan ya nufa yayi sallama suka amsa mai tukuna ya shiga

"Dama bacci yakeji tun dazun amma yaki yayi sai wasa" Mamu ta fada tana dariya

"Wallahi kuwa cartoon na barshi yana kallo koh da zan dawo bacci ya dauke shi"

"Miko mun shi nan naje na kwantar dashi yayi ko na rabin hour ne tunda marace yayi "mika mata shi yayi tare da ce mata zai fita sai ya dawo, Allah ya tsare ta mai ya wuce yana cewa.

"Ki gayawa su Momi cewa na dawo, na sake fita idan na dawo akwai labari"

Rai a bace tace "ok nice ma na zama yar aiken ka koh?"to ba zan fada ba kaje ka gaya mata da kanka dan rainin wayo kawai"

Dariya sosai yayi da bai sake ce mata komai ba ya wuce abun shi, yana akan titi tunani yakeyi ta ina zai fara idan da hanifah tana nan da gurin ta zaahi, yana cikin haka ne ya tuna da Manir sai kawai ya dauki waya yayi dialing numbern shi, ringing biyu tayi ya dauka ban san me suka tatauna akai ba naga Abdallah yana murmushi tare da kashe wayar.

--------------------------------------------------



Thanks 🙏 for reading

Mairo ❤

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now