17

302 40 4
                                    


Sai daya tsaya sallah tukuna ya shigo gidan gurin karfe goma part dinsu ya nufah Allah Allah yakeyi kar abunda zuciyar shi ke gaya mai ya zama gaske sabida da alama ba kowa a ciki direct dakinta ya nufa,ya tura kofar ya shiga ciki a kwance ya gansu ita da ilham sai bacci sukeyi abun su , ajiyar zuciya ya sauke tare da matsowa kusa dasu ya dubi fuskar hamida tayi jajawur sabida kuka sai kawai yaji ta bashi tausayi.

Sai da ya kara mintuna kadan tukuna ya shiga tada ita ai kuwa tana bude ido ta ganshi ta daure fuska yace"tashi magana zamuyi"tashi tayi ba tare da tace mai komai ba yace "zo nan ki zauna"ya nuna mata kusa dashi ta taso ba musu

"Ummi meyasa kike so ki sauya haline sabida kawai nace ba zaki gidanku ki kwana ba uhmmm,kin san bana so kiyi nisa dani koh?kamar ba zata amsa ba tukuna tace

"Ai sati daya ne kawai zanyi ba wata daya ba kuma ai zaka dinga zuwa tunda kaima gidanku ne ai"

"Gidan surukan nawa zan dinga zuwa ba dare ba rana haba mana, ki bari kawai na dinga kaiki ina dawo dake kinji"ta make kafada alamun bata yarda ba

"Toh ba komai gobe sai ki shirya na kaiku"ai kuwa ba san lokacin data rungume shi ba har dasu kiss sauketa yayi akan kafarshi yace

"Idan wannan ake so amun to a biyoni dakina yanzun nan sai in san cewa da gaske akeyi" murmushi tayi tare da girgiza mai kai shi kuma ya nufi nashi dakin domin yin wanka.

Har ya kwanta bata shigo ba ya ma dauka ba zata zo ba sai gashi ta shigo, kusa dashi ta kwanta tare da ajiye kanta akan kirjinshi,ta fara mai magana shi kuwa daga uhmm sai aa yakeyi,har labari yazo ya cenza nima sai na kwashi inawa inawa na gudu

*********
Bayan sati daya

Washington Dulles international airport America

A zaune suke a cikin VIP na airport din kasar America kowace ka kalla kyakyawa ce ta bugawa a jarida,kallo daya zaka musu ka gane cewa natsasu ne,kowace harkan gabanta takeyi daga ganin su yan gida daya ne sai dai kowace da nata kyau da Allah ya mata.

"Amma abun nan da mamaki kwanakin nan flight yana delaying sosai"dayadaga cikin yan matan ta fada, ashe dai suna jin hausa

"Allah kuwa is just getting too much na san sis zulfa'u ta isa naija by this time mu kadai muka rage"karamar cikin su ta bada amsa duk suka kwashe da dariya

"Mamah ba kya jin magana koh ba tace mu daina kiranta zulfa'u ba,karki sake taji wallahi"wada aka kira da mamah tayi tsaki tace

"Naga ai sunan dasu daddy suka saka mata kenan koh?kuma wallahi ko a gabanta ne sai na fada"

"Nima dai shina gani zulfa'u zan kirata ba wani zulfa mutum sai shegen jiji da kai"

"Wallahi hafsa ba ruwana naga dai abun da take so a kirata dashi kenan then do as she wants mana"mamah taja hafsa suka bar yayar tasu a gurin,suka nufi jirgin sabida anyi announcing zai tashi

"Dama ku bakwa son gaskiya"ta fada tana binsu a baya,da suka shiga kowace ta samu guri ta zauna mintuna kadan ya tashi sai mun hadu a Nigeria

Idan baku manta ba hafsa da hasinah, suke biwa aunty hanifah,salmarh (mamah)kuwa kanwar zulfa ce wato dukan su kannen Abdallah ne kenan
*********
"Kai fah ni hakuri na ya kare aure nake so nayi cikin shekarar nan am not getting any younger haba" kallon shi khalifah yayi

"Toh wai waye ya hanaka kayi auren koh yau kaso yin aure zamu daura maka shi,kuma a iya sanina kana da wace take sonka kaine kawai kake mana yawo da hankali"

"Wa kake nufi ne? Abdallah ya tambaya"zulfa'u mana kana da wata bayan ita ne? yarinyar nan tana sonka amma sai walakanci kake mata ko dan zumunci ai ka aureta"

"Naga dai kaima ba auren kayiba,kuma idan da kara kamar yanda take kanwata haka take a gurinka toh ka aureta mana,ka wani dameni da maganarta"

"Idan kun bani mezai hana na aureta,amma ai kai take so wai na tambayeka mana,wacece wannan ma da kakeso haka har da kake kawo auren kamin karshen shekarar nan,an nema maka aure ne ban saniba? khalifah ya tambaya dan dan uwan nashi ya fara bashi mamaki

"Zaku dai je ku nemo mun aurenta nan da wata daya insha Allahu,ka tashi mu tafi gidan if you're through with your questions "Abdallah ya fada tare da tashi tsaye ya dauki hularshi dake kan table din ya saka,ya nufi kofar fita daga office din,shi kuwa khalifah ko motsi bai yiba

"Idan ka tashi fitowa ka jawo kofar kacewa secretary tazo ta rufe da kyau,sai mu hadu a gida"ya fada a lokacin da yake fita da office din ya san abin da khalifah yake nufi da zaman da yayi,wato bazai fita ba sai ya gaya mai abunda yake boyewa shi kuma baya da wannan lokacin

Idan baku manta ba hafsa da hasinah yan biyu ne,Kuma kannen Abdallah ne su suke biwa hanifah,saleemah(mamah)kuwa kanwar zulfa ce,so gaba daya dai siblings din Abdallah ne su

**********
Fuhutu ce a kwance kan daya daga cikin kujerun parlorn abun duniya duk yabi ya mata yawa satinsu daya kenan da kare exams,zaman gidan duk ya isheta Yaya mujahid gaba daya ya sasu a gaba ya hanasu fita ita da jiddah,a satin nan sau daya ta san ta fita shima dawowar su hajiya ne da Aunty hanifah daga umarah da sukaje dauko su daga airport sai kuma washe gari da sukaje tare da Ammi.

A nan ne ma Ammi da Mamin Abdallah suka hadu,ashe abokai ne tun na kuruciya,yayin da Mami take gayawa Ammi cewa sai da su fuhutun suka wuce ne taga ashe batada numbern shiyasa bata kira ba,tana cikin tunane tunanen tane wayarta dake kusa da ita tayi kara,koh bata duba ba ta san jiddah ce sai kawai ta daga wayar

"Hello"ta fada a kasallance, jiddah ta kwashe da dariya tace"sai ba Yaya mujahid ba,daga shi sai Abba kadai ke bada umurni Kuma abi rashi fitan ne yasa kike magana kamar wata mararar lafiya?ta fada tare da koma fashewa da dariya

"Naga dai fitan nan bani kadai aka hanawa ba to meye abun dariya harda ta mugunta,na dauka satin nan zai tatara ya koma, tunda Aunty hamida ta dawo daga gidansu amma Yaya Ahmad kawai ya koma sabida makaranta, Allah shaidane na gaji da zaman gidan wallahi am tired"

" Bari  kawai bestie har ni kuwa yasa a ciki,dana dauko key zan fita sai hajiya tace ba yayanku ya hanaku fita ba,kamar zan kuwata nakeji"dariyace ta kwubuce masu gaba daya daga nan kuma suka shiga wani labari daban

*********
Momy,umma da Mami ne a zaune a cikin parlorn sun fira,sai ga firdausi da rufaida sun shigo da sallama,suka amsa masu

"Wai sai da taje ta dauko ki daga gidanki? Mami ta tambaya, murmushi tayi

"Aa dama ina da niyan zuwa nan gidan sabida yaune su zulfa'u da hasinah zasu dawo koh"

"Amma ai da kinjira sun dawon kamin kizo ke da bakida lafiya,ba a wasa da sabon ciki fah musaman naki da yake da matsaloli idan daddyn ku ya ganki yanzu wallahi fada zai maki"umma ta fada, dariya momy tayi tace

"Haba ya isa haka mana kun wani sawa diyata baki firdausi zo nan ki zauna"ta tashi kuwa ba musu ta tafi ta zauna kusa da ita tace"mace mai ciki wanda baiyi kwariba ba a son tana yawan sintiri kan hanya kinji" tace "toh"

"Yawa kije akwai abinci a dining table kice sai ki kwanta kamin su dawo kinji"ta tashi kuwa ba musu ta nufin dining din

"Toh ni ba zakice naci abincin ba"rufaida ta fada a shagwabe Mami tace"toh kema kije kici shikenan koh"

"Yawa Mami na"ta fada tare da bin bayan firdausin,momy ta girgiza kanta tace "Allah ya shirya" suka amsa da"Amin" gaba daya.

________________________________

Sannunku
Vote
Share
Comment
And
Follow

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now