16

332 48 5
                                    

Ta jima sosai a dakin kam ta dawo parlorn ta nufi dining don cin abinci har ta gama zata tashi sai ga yayan nata ya shigo ta hanyar kitchen"yayah ina wuni?ta gaida shi "lafiya qalau fuhutu ya exams da fatan ana karatu koh"tace "eh anayi"

Daga nan suka karasa parlorn tare ya gaida Ammi ta amsa mai zainab ma ta gaida shi ya zauna a kasa kusa da Ammi "wai Ammi ina diyanki maza suka shiga ne?
"Toh ni yayanmu taya zan sani na daiji kamar yazid yace yana da exams shi kuwa Ahmad ban san inda ya tafi ba,neman su kakeyi ne?

"Aa kawai na tambaya ne tunda muka gaisa da safe har yanzu karfe biyar ban gansu ba shiyasa"tace toh shikenan daga nan kowa ya maida hankalin shi akan tv da yake aiki.

Da gudu suka shigo gidan ko wanne yana sauri ya riga dayan shigowa parlorn suna kawo tsakiyar dakin suka ga yayan mahaifiyarsu ai sai suka natsu, atare sukace "Uncle ina wuni?

Dariyace ta kama fuhutu ta san dama duk rashin jin irin na mufid toh idan yaya mujahid yana guri bayayin shi,kallon su yayi yace"lafiya qalau ina maman taku?ya tambaya.

Anty mufidah da take shigowa da mustapha a hannunta tace"gani nan wa yake nemana"ta fada tana murmushi shima murmushin ya mayar mata "sannu Anty babba ya gida da kuma maigida"ta rike baki.

"Aa yaya inka bani girman ina zani dashi ka dai barni a haka"ta nuna su fuhutu"wa ya nan kawai da sauran biyun da nake da a bayana jinake kamar na tsufa idan na hada da kai sai Yaya kenan" sai kowa ya kwashe da dariya dama Anty mufida dramer queen ce ta karshe ta iya bawa mutane dariya

Daga nan ta gaida Ammi tace daga gurin bukin suna suke shine suka ce bari suzo su gaida tsohuwa mai ran karfe.

"Lallai ma yanzu nice na zama tsohuwa koh mufida?nida naka jin kaina kamar yau aka haifeni"su mufid suka kwashe da dariya Ammi ta dubesu tace "yan rainin wayo wa kuke wa dariya?

"Dama zuwa nayi idan da qubewa a gidan nan a bani na zaga gaba daya central market babu"fuhutu tace"Aunty yaushe kika fara shan miyar qubewa Kuma?

"Ai kin san idan tani ce wallahi ba zan ciba abbansu ne yakeso"Ammi tace "akwai kuwa fuhutu shiga store ki ebo mata kinci albarkacin abbansu da ba zan baki ba" cin dariya tace "Allah ya huci zuciyarki Ammina tuba nake"ta dubi miskilin yayan nata tace "Yaya mujahid ina sis hamida da baby ilham ko sun fita ne?

Sai yanzu ya lura cewa bai ganta a parlorn ba sabida idan har tana gida to a parlor take zama su sha fira tare da Ammi Allah dai yasa ba fita tayi ba bayan yace kar ta fita.

"Tana cikin gidan ina ga dai aiki takeyi"ya amsa mata"Allah sarki  wa zai ebo mun qubewar ne wai sauri fah nakeyi banyi abincin dare ba"fuhutu tayi sauri ta tashi ta nufi kitchen gurin debo mata qubewar.

*******
Da suka iso gida eesha ta sauka ta bude gate,sannan ta dawo taja motar cikin bata ma ida tsayar da motar ba ta fita kallo kawai eesha ta bita dashi,ta gyara tsayuwar motar tabi bayanta

Da sallama ta shiga parlorn nasu,bata sameta a ciki ba ta san tana dakinta sai kawai ta wuce nata itama,bayan duk sun gama abun da sukeyi sa suka dawo parlorn eesha tace

"Zulfa wai me yake damunki ne kwanakin nan duk kinbi kin koma wata iri,hope all is well with you?ajiyar zuciya ta sauke kamar ba zata amsa ba.

"hankalina ne gaba daya ya tafi gida wallahi sati dayan nan daya rage ji nake kamar na gawo shi yamun tsawo da yawa"

Dariya ce tazo wa eesha ai kuwa tayi abunta tace"kin san Allah banyi tunanin akwai abinda zai iya saki marairaice haka ba,kin ganki kuwa?

"Yaya Abdallah ne ya shiga zuciyata kwanakin nan duk na matsu na tafi gida na ganshi ,idan ma na kirashi yanzu baya daga wayana"

Idan baku manta ba zulfa'u (zulfa) cousin din Abdallah ce wato diyar momy da uncle tukur, ga wanda ba gane ba ya koma chapter 4 ya karanta zai gane.

"Toh taya ma zai daga wayar taki tunda bakida jan aji tunda na sanki shekara daya kenan ba ranar da bakya kiranshi haba zulfa ba dole ya maki walakanci ba ki dinga danne zuciyarki akan shi mana"

"Ba zaki gane bane tunda na tashi na san kaina nake kaunar bawan Allahn nan Kuma bana jin zan iya dainawa"ta fada hawaye na zubowa a idonta eesha sakin baki tayi tana kallon ikon Allah ba abun da yake sa zulfa kuka irin maganar Abdallah

Fata take ta ga Abdallah nan a zahiri duk da ta ganshi a hoto, matsowa tayi kusa da ita ta shiga lalashin ta har tayi shuru da na suka sake fita don neman abinda zasu ci

*********
"Wai menene tun dazun ka cikani da surutu,ka barni inji da abun da yake damuna mana, wayace da na riga dana saya mai  sai inga abun da zakayi" ya fada hankali kwance.

"Kamar yanda nace duk ka saya mai zan gayawa Daddy toh wlh hakane yanzu gurinshi zani"Abdallah yace"sai ka tashi ka tafi mana na rike kane,tunda na lura ka daukeni kamar bare kai kadai ne yayan Salim" ya fada rai baci khalifah ya bude baki zaiyi magana kenan ya dakatar dashi

"Dan Allah ka fita kawai bana son hayaniya please"tsaye ya tashi yace "ba zan fita ba sai kazo ka fitar dani kuma kai kafi kowa sanin cewa kafini kusanci da Salim so kai ka sani idan kai Yaya shine koh ma kaninsa ne amma duk kukayi abun da baya da kyau sai na gaya maku gaskiya dan wannan almubazaranci ne"

Abun dariya ma ya koma bawa Abdallah yanda ya hakikance sai fada yakeyi,wai suna almubazaranci da kudi kura mai ido kawai yayi ba tare da yace komai ba,kanshi ke ciwo ba zai iya da rigimar khalifah ba .

"Ok amsani mane ba zakayi ba toh shikenan"ya tashi ya fita tare da rufe kofar da karfi kamar zai balleta,girgiza kanshi kawai yayi yaci gaba da abinda yakeyi

______________________________

Ina godiya sosai da comments da votes a kara kaimi dan Allah,ina so na gama littafin da wuri amma bana ganin votes da comments dinku

Thanks 🙏

Vote
Share
Comment
And
Follow

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now