15

336 40 5
                                    

Fuhutu da jiddah ne a tsaye tun dazun suna kallon abunda yake faruwa tsakanin ma'auraten biyu jiddah tace "what was that all about ?

"Naga dai tare dake muka shigo yanzun nan so how will I know?ke dai ki wuce ki kai little gida kamar bacci yakeji"ba tare da tayi musu ba tace

"Toh shikenan bye sai Friday koh tunda interval din na kwana biyu ne"Kai kawai ta kirgiza mata ita kuma ta koma mota taja ta wuce,numfashi fuhutu ta sauke ta shiga cikin gidan da sallama ammi ta amsa mata,tare da tambayan ta ya  exams tace Alhamdullilahi,mamaki cikata ganin har da zainab a zaune Kuma ta san cewa yanda yaya ya dinga hargowa dole suji tace

"Ammi bakuji Yaya mujahid yana fada a waje bane? murmushi tayi tace"naji mana auta me kike so nayi ne?tace "ba komai"ta san cewa tunda har Ammi bata tankawa fadan  nasu ba to bata so ta shiga rigimar ne.

Ammi kuwa a zuciya tace ta yaro kyau take bata karko,mezai sa na shiga fadan dana da matar shi matukar ba susuka sakani ba idan zasu shekara sunayi ba zan nuna na saniba,sabida idan nayi magana yanzu hamidah zata dauka ina goyon bayan dan nawa ne ba ita ba,so is better na saka masu ido kawai idan lokaci yayi zanji meye masalar.

"Auta ya exams?zainab ta tambayi fuhutu,kusa da ita ta zauna tace "exams mun gode Allah yaya abu" dariya tayi "yau kuma yaya na samu kenan, waya baki wannan jakar mai kyau haka?sai lokacin ta tuna da sakon da Mamu ta bata zuwaga Ammi tace"hmmm gidansu maman little daddy mukaje matar yaya manir gurin dauko little shine mamanta ta bamu nida jiddah kowa dai daya"

"A lallai an gode kuwa Allah ya saka mata"Ammi ta fada " Amin kuma tace zata kiraki wai ta sanki sosai kawaye neku sabida kun hadu ma a calfornia kamin auren Yaya mujahid har sunanki ta kira"Ammi ta rike haba " tunda ta kira sunana ta sanni kenan toh ina jiran kiran nata, sai ki tashi kije kice abinci yana kan dining kowa yaci ke kadai kika rage"

"Toh Ammi "ta fada tare tashi ta dauki hand bag dinta ta mikawa zainab dayar jakar tace "ki duba ki gani meye a ciki ina zuwa"ta nufi dakinta .

*******
"Wai me wannan mutum yake nufi ne tun dazun muke jiran shi amma yaki yazo wallahi idan na gaji am getting out of this place"ta da fuska a yatsne

"Da kuwa mun jira shi dan mu zai amfana ba Shiba" wadda take kusa da ita ta bata amsa rai a bace,yanda ta tsani yarinyar bama gaskiya bane ta cika yanga da yawa ga nuna isa.kallonta tayi tace

"Please ba dake nake magana ba karki sake sa mun baki a magana na"sannan ta dubi kawarta "eesha tashi mu tafi dan Allah I need some fresh air"ta kuwa tashi tabi bayanta suka koma wani gurin suka zauna

"Ga gajiya ga yunwa gaba daya sun game mun wlh"dariya eesha tayi tace"toh muje mana mu nemo maki abun da zakici mana"

"No barshi kawai idan dan walakancin nan yazo ya gama abun da zai mana sai mu tafi"daga nan ta fiddo wayanta daga cikin Jakarta tana dubawa eesha kuwa shuru kawai tayi ta maida dubanta a gurin da suka bar yan anjin nasu kar malamin yazo basu saniba.

Da malamin yaxo suka tashi sukaje gurin shi tunda ya ganta yake washe hakoran shi kamar maye,koni kaina sai da ya bani haushi,ita kuwa kallon arziki ma bata mai ba jira kawai take ya fadi mai zai fada tayi gaba.

Bayan ya gama masu bayanin abunda yake so suyi ta juya ta wuce wanta da eesha a bayan,cikin ranta sai tsine mai takeyi dama abunda zai gaya masu kenan ya tsaida su haka,ba zai iya gayawa class rep dinsu yayi announcing a class ba ko a rubuta a notice board.

So kawai yake su kara yin wani sati daya a makarantar nan bayan sauran department duk sun gama abun da sukeyi ko yaushe kaga dama ka iya tafiya kasar ku koh kuma garinku,yanda ta matso ta koma Nigeria ba ma gaskiya bane shekara daya kenan rabonta da naija sai da azo mata visiting tsaki tayi ta shiga mota eesha taja suka nufin gidan gidansu.

********
A zaune yake a daya daga cikin gujerun dake aje a gurin shaqatawar kanshi gaba daya yayi cagi,ya rasa taya zai bullowa hamida ta gane cewa shi mabukaci ne baya so koh kadan matarshi tayi nesa dashi.

Ya san cewa ta sani kawai tana sone ta fifita tata bukatar akan tashi ne yana cikin haka manir yazo,ya buge shi cikin wasa yace
"Wai meye ke damunka ne mujahid?ajiyar zuciya yayi "wlh wani babban abu ne ke damuna,hanida ce ake buki gidan su shine nace ba zataje ta kwana ba zata dinga zuwa ne tana dawowa amma yarinyar nan taking ta fahimceni"

"Toh kai meyasa ka hanata zuwa ta kwana ba kace gidansu bane ka barta mana sati daya ne ta dawo"dariya bakin ciki yayi "ka fahimceni mana manir kai namiji kuma kana da mata ya kamata ka gane yanayin da nake ciki mana idan suka kake na fito fili na bayana maka abunda ka riga ka sani toh shikenan"

Murmushi yayi "aa mujahid na san da wannan amma fah daurewa zakayi kar ace kullum ita ke yin kokari gurin faranta maka, kai bakayi kayi tunanin maganar mana" iska ya furzar "toh shikenan naji zan duba amma wlh auren nake so nayi kwanan nan kamin na koma calfornia"manir me zaiyi idan ba dariya ba

"Kar kasa na fara tunanin kai harijine"girgiza kanshi yayi "idan akwai abunda ma yafi haka to nine shi daga Allah nidai enough of this me zakaci a kawo maka?

"Amma dai Allah ya maka albarka ka san gwauro ne ni kwanan nan matar tawa hajiya ta kwace mun ita,inaga nima auren nan zanyi" harara ya banka mai yace"na fika sanin matarka bata nan ai kuma ba dai hanifah zaka wa kishiya ba inaji ina gani" dariya yayi yace "sannu baba"

Daga nan sukayi ordern abincin suna ci suna fira har wani lokaci tukuna suka fito daga gurin kowa ya kama gaban shi

________________________________

Wace ce wannan data matsu ta dawo nigeria?
Mu hadu a shafi na gaba

Thanks for reading 🙏
Vote
Coment
And
Share

Marmiee❤️

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now