28

470 50 2
                                    




Kuyiwa Allah da annabi kuyi voting,kuyi commenting,kuyi following

A gurguje

"I really don't know what your husband saw in this girl na lura gaba daya ta tafi da imanin shi"latifah kawar  hamidah ta fada daidai fitowar Jiddah daga part dinta mugun kallo hamidahn tabi Jiddah dashi kamin tace

"hmmm toh ba munafurci bane da iya kissisina wlh  i just hate this girl,bata da wani aiki daya wuce ta badewa mutane hanci da kamshin turare kala kala,idan tana tsaye a kusa dake jin kike kamar company din turare ne a gurin and her hands are always having henna designs ai ina ganin karuwanci a gidan nan"

Latifah tace "kuma gashi karamar yarinyace amma harta iya irin wadan nan abubuwa haka,ya fah kamata ki tashi tsaye dan yanda nake ganinki gaba daya baki dauki duka abubuwa nan dakika lissafa mun a bakin komai ba,you better take action tun kan tazo ta kwace maki miji kinaji kina gani"tace

"Toh ni ya zanyi wlh yarimyar ji takeyi kamar bani a cikin gidan nan,idan ma nayi wani abu sabida ranta ya bace koh kallo na batayi sai daima ta mun murmushi toh irin wannan taya ma zan sa tayi fada dani balle har na cacasata"

"You always disappoint me Allah sai ki dinga yi kamar ba kawata ba kema kinsan da nice da irin situation dinnan da baza ma ta shigo ba bare har nazo ina neman hanyan dazan korata waje"latifah ta fada tana yamutse fuska nisawa hamida tayi tace

"Bazaki gane bane ita yarinyar alakace mai karfi tsakanin danginta da nashi mahaifinshi ne fah ya bashi aurenta kinga kuwa fitar ta a gidan nan abu mai wuyane ni yanzu fatana ma bai wuce na dinga musguna mata ba har sai ta bar gidan nan da kafafunta"

wata ashariya latifah ta danno tace "hausawa sukace abokin barawo barawone amma yau na karyata zancen nan,gaba daya halinmu ba daya ba iskancin ki bai kai nawa ba,ba kece kike yiwa uwar miji biyayya ba toh gashi an hada baki da ita an maki kishiya,bari kiji na gaya maki ba alakace dasu ba koh kanwarsa ce uwa daya uba daya ya aura karshen alakar kenan toh wlh sai na fidah ita keni kishiya kota wuccin gadice bana so"

Dariyace ta kubucewa hamidah tace "toh meyayi zafi naga dai kishiyar nan ni ake yiwa,meye kuma abun tada jijiyoyin wuya"tabe baki tayi tare da tashi tsaye tace

"Ki dai san abunyi kamun kisha mamaki dan yanda nake ganin yarinyar nan,nan gaba sai ta tsone maki ido ke harni sai ya shafa kinga tafiyata sai munyi waya ba sai kin rakani ba"

Bayan tafiyar latifah sosai ta zauna tana tunanin abubuwan da suka tatauna ita fah ba wai tana so ta mata wata babbar mugunta bane,kawai dai so take a musguna mata ta kuma saka mata tsoronta yanda koh sunanta taji sai hankalinta ya tashi.da taga tunanin ba zai amfana mata komai ba sai ta tashi ta shiga ciki dan ta duba ilham data kwantar a daki tana bacci kamun su dawo balcony

********************

Tafiya takeyi kamar bata so har tazo gurin shi,gaba daya jinshi yake kamar wani sarki a fadar shi,a kusa dashi ta zauna tare da sada kanta kasa murmushi yayi yace "ina kika tsayane tun dazun"kamar ba zata amsa ba sai tace "wanka na shiga tara da dauro alwala"

Yace "yayi kyaue so do you have a place in your mind that you will love to visit here(kina da wani guri a ranki da kike so ki ziyarta a nan)"ta daga kanta yace

"mena gaya maki last time about nodding your head for me"tayi shuru sai shima ya kyaleta ba tare dayace komai ba suna cikin haka ne wayanta yayi ringing da yake a kusa shi take sai ya dauka ya miko mata sunan data gani a wayan ne yasa ta sakin murmushi bazata,shi mamaki ba take bashi dan yanda takeji da fuhutu bama gaskiya bane koh fushi takeyi ta mata zanceta yanzu zata warware

"Hello bestie na"ta fada cike da jindadi sakin baki kawai yayi yana kallonta yarinyar daya gama yiwa magana yanzun nan tana amsa mai daker shine yanzu harda dariya shifah baya son kunyar na a gidan shi,yafi son ta sake su dinga cin soyayyarsu

Fuhutu tace "ba wani nan kinje kin kashe wayanki gaki dadi miji kin manta dani 1month kawai ina ga shekara guda"

"Dan Allah kiyi hakuri wlh ba laifina bane nima sai last week tazo hannuna kiyi hakuri" ta fada sigar lallami tace "naji ya kike ya amarci ana nan anata sabga koh" gabanta ne ya fadi tayi shuru batace komai ba fuhutu ta kwashe da dariya tace

"an cinye bakin kenan hohoho wayyo dadi kashe ni,your silence says it all dear Allah ya bada zuri'a dayaba dan nasan yayah ya riga da yayi shooting shot dinshi"dariya ce ta subuce mata tace

"Allah ya shiryaki autan Ammi nidai sai anjima yana kusa dani we will talk later"jiddah ta fada kasa kasa ba tare da ta tsaya jin abinda zatace ba ta kashe wayan tana smiling daure fuska yayi tare da gyara zaman shi yace

"Come sit here"ya fada yana nuna mata kafafun shi"ido ta zaro daga baya kuma ta langabe kanta cike da shagwaba tana mai magiya akan ya kyaleta a inda take

"Kin san Allah idan baki zoba sai na ba'ata maki rai"ya fada a hasale tashi tayi tazo tamai tsaye a gaba,juya fuskan shi yayi kamar bai san da ita ba da taga ba sarki sai Allah,rufe idonta ta kamar wacce zata zauna kan kaya ta danguara mazauninta a kan kafafun shi tare da fashewa da kukan shagwaba

"Shhhhhhh ya isa haka nan tsoronki yayi yawa,just cool down ba abunda zan maki ok? Ya fada tareda rungume ta.

******************
"Waye ke sa matata dariya haka ba kakautawa"Abdallah dake shigowa bedroom din ya fada tace "who else khairi idan ba jiddah ba"

"Ta kunna wayan kenan"ya fada yana mata kallon kurullah tare da zama gefenta"tace "eh ta kunna,me kallo keso?yace

"Abunda ya gani"

"Toh kuwa sai dai ya barwa Allah"ta fada tana dariyar mugunta



I take god beg wuna
Make wuna
Vote
comment
Follow

Mrs umar❤️

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now