35

179 18 4
                                    

Not edited

Cike da jin dadi jiddah ta isa gurin fuhutu ta rungumeta "oyoyo my one and only besty wannan surprise haka"ta fada tana karbar khalid daga hannunta, a yatsine fuhutu ta gaida Anty hamidah tana yiwa yarinyar da take ganin ba tada bambanci da zindir wani hasabibin kallo,kin amsata tayi itama kuma bata damu ba,kan fuhutu ta zauna hamidah taja hannun yarinyar sun fice sai bayansu su suka gani, hamidah kuwa sanin cewa matukar ta tsaya to kuwa dramer da fuhutu zatayi zai ninka na jiddah ne yasa taja hannun kanwarta sukayi gaba.


"Who is she?ta tambaya a zafafe alamun taji zafin yanda suka tafi suka barta ba tare data sauke masu ruwan bala'in da takeji yana taso mata ba,dariya jiddah tayi tace

"ke dan Allah manta dasu dan yau take sallah gurina,shine zaki zo baki gaya mun ba koh a bakin yaya ban samu labari ba"

"Ni nace karya gaya maki i wanted it to be a surprise"

"Ai koh gashi kin mun ya hanya?

"Lafiya qalau Alhmdllh wata seminar yazo yi shine nace sai yazo dani dan tunda ban taba zuwa ba,Ammi ma tace tana gaidake har da yaya zainab ma taso zuwa but ciki ya hana dan Due date dinta ending of this month ne so it's in possible for her to travel.

"Allah sarki kice na kusa na zama momy for the second time"

"Ai kuwa kin kusa kan ki sauke mana third one din ba"

"Hmmmm"

Haka dai sukayita firarsu har akayi sallar la'asar da suka sauke faralli ma dawo sukayi,suka cigaba daga inda suka tsaya su hamidah dai anki a dawo parlor sai gurin karfe takwas mujahid ya shigo gidan a dabe ya samesu a kasa sai labari suke suna kwashewa da dariya.

"Yau California tayi bakuwa dan duk garin nan sai yasan autar Abba tazo kin wani saka mun mata a gaba kina mata surutu"mujahid ya fada yana shigowa parlor bakinta ta turo gaba

"Haba yaya bama itace ta cikani da surutu ba nice na cikata,

"Sosai ma kuwa dan halinki na sani mun ma godewa Allah da bakinki ba babba bane da abin yafi haka"

Dariya duka suka saka a tare shigewa yayi daki ya barsu,zungurar jiddah fuhutu tayi tana mata ido

"Menene?

"Tashi mana ki bishi"

"Bazan tashi ba ai na mai setting abincin shi dazu da mukaje yin sallah so ba saina tafi ba"

"Hahaha yarinya bakida sense dama haka kikeyi ko kuwa yanzu kika fara?come on tashi kije ki dawo miji ya kwaso gajiya baki san abinda yake ciki ba,shin lafiya lau yake baya da damuwa oho kin wani zo kin baje wlh tashi kije karya kara mun wani sharrin yace nina rikeki"

Dariya jiddah tayi "halin nan dai har yanzu ba'a cenza ba koh in an girma asan an girma fah"

"Kanki akeji"

Tana shiga dakin ta tararar mujahid din ya shiga wanka,kayan daya cire ta dauka taje ta saka a washing machine din dan indai a dakinta yake bata bari mai wanki yayi ita take abunta,koda ta dawo ta tarara ya fito yana shafa mai

"Sai yanxu aka ga daman zuwa guri na?da yake yaruwa tazo na zama abun tausayi sai yanda akayi dani"dariya ya bata ta kuwa dara

"Allah sarki yaruwa dama tace sai ka zargeta tasan halin yayanta kenan sosai"

"Bawani nan nidai a tabbatar an cigaba da bani kulawa yanda ya kamata kar a tauyen hakki"

"Baban ilham yana da hakki a kaina ne?tafada cike da zolaya

"Shi kuwa yake da hakki a kanki"

"Toh Allah ya bani ikon saukewa yanzu ka shirya sai na baka abincinka koh"

"Dafatan dai feeding dina za'ayi?

"Why not" ta bashi answer dramatically

Ranar daka kalli fuskar jiddah kasan cewa tana cikin farin zuwan fuhutu yafi komai sosai take jinta cikin annashuwa,bayan sun gama cin abincin ya dubeta so yake yaji ta bakinta akan abinda hamidah ta gaya mai kan ya yanke hukunci dan ta kirashi a waya tana cewa ta fita ta bar illham a gida ta dawo ta sameta tana kukan yunwa kuma ta tambayi Grace ta tabbatar mata da bataga an bata abinci ba.

Yasan cewa jiddah ba zata taba musgunawa illham ba a bayan idon shi kuma yana da tabbacin yau idan akace ya mutu yabar illham a hannunta toh sai tafi samun kulawa da tarbiya nagartaciyya a hannu jiddah fiye gana mahaifiyarta,duk da akace baka shaida dan adam toh shi kam yana da ita akan jiddah kaso casain cikin dari ma kuwa dan haka sai ya fasa tambayarta.

"Hope am save wannan kallo haka"

"You're not save dan an kawo mun karar ki"

"Da nayi me?

"Sata"

"Sata kuma? Allah ya kiyaye nikam banayi,ban taba yiba and bazan fara akan ka ba"

"Ai kuwa kin shayi kuma har yanzu kina kanyi dan kin sace mun zuciyata"ya fada yana rike zuciyarshi dramatically tare da fadawa kan gado,murmushi tayi cike da kunya.

"Yaya wllh....."

"Wallahi me?Haka dai suka yita hirarsu cike da farin ciki,sosai take mamakin shi wata rana dan yanda take tsoron shi adah kamar dodoh

Bayan tafiyan jiddah fuhutu ta tashi ta koma part din jiddah dan ta duba khalid data bari yana barci,can cikin barci taji kamar motsin mutum a falon tunanin ta jiddah ce ta dawo sai kawai ta share dama bacci takeji,da taji motsin yayi yawa sai tace bari dai ta duba gilmawar mutum ta gani aguje mamakine ya kamata dan tasan ba jiddah bace toh waye koh dai yayane yazo daukan wani abu,tunanin data sakawa ranta kenan tayi addu'a taje ta kwanta.

Da asuba jiddah ta shigo tada fuhutu dan tayi sallah ta samu ta riga da ta tashi

"Ashe kin tashi?

"Eh na tashi shine jiya akaki zuwa a mana sai da safe koh"

"Na shigo fah kuna barci"ta amsata cikin sauri dan tasan zata iya kureta indai fuhutu ce,duk laifin yaya ne shiya hanata fitowa gashi yaja zataji kunya,ita kuwa fuhutu hankalinta ne ya kwanta jin cewa jiddah ta shigo kenan ita ta gani jiya .


*****************

Nace gobe sai ga update bayan kwana goma 🤣🤣🤣
Wlh na zama lazy kwanakin nan

Ayi hakuri ga aikin gida ga sana'a ga kula da miji abubuwa da yawa suke sai a hankula😞😞😞

Wa kuke tunanin ya shigo part din jiddah?🤔

Da wace manufah taxo koh yaxo?👽

Mrs umar

Jazakallahu khairan🙏

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now