10

330 42 8
                                    

faizaya this chapter is dedicated to you thank you so much for the votes and comments am grateful

__________________________________
√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√

Fuhutu kallon kodai nayi gamo ne take mai yayin da jiddah take mai kallon me crush yakeyi a gidan mu yana zuwa dama, amma ya akayi ban taba ganinshi ba, shi kuwa tun dazun data shigo yake kallonta mamaki yakeyi bai taba ganinta a gidan hanifah ba dama Manir yana da Alaka da yarinyarnan ne ko ya abun yake,koma dai yayane shi dadi ma yaji daya sake ganinta dama addua yake Allah ya hadashi da ita sai gashi abun ma yazo da sauki.

Kowa yana jiran yaji sun gaidashi amma sunki, duk sun kura mai ido sai kallonshi suke kamar wasu gumaka" ba kwajine wai ku gaidashi mana aa"Hajiya ta fada a fusace kallon juna sukayi ko wacce tana yiwa yar uwarta kallon kinga abun dana gani," ina wuni?" suka fada a tare "lafiya qalau"ya amsa a takaice daga nan suka tashi kamar wasu munafukai suka bar parlorn.

Dakin jiddah suka shiga,da gudu fuhutu ta haye gadon ta qudun dune tana sauke numfashi ita kuma jiddah ta samu guri ta zauna"bestie wannan kamar crush dina koh? "

Harararta tayi tace "ban saniba ni zaki tambaya bakida ido ne? dariya tayi "toh meyayi zafi fuhutuna haba mana daga tambaya sai cibe ya zama kari"shareta tayi bata sake cewa komai ba ita kuwa jiddah toilet ta shiga ta sake wanka tazo ta cenza kaya tana gama sakawa kuwa hanifah ta shigo tace "kuzo mu tafi ko kar lokaci ya tafi" tashi sukayi ko wacce ta dauki gyalen ta suka fito, har yanzu yana nan bai tafi ba har jiddah zata sake zama a parlorn fuhutu taja hannunta tana cewa

"Muje waje mu jirasu su fito"ta kuwa bita kamar wata wawuya sai da suka isa gurin mota tukuna ta kwace hannunta"meye haka ne wai kika jani kamar wata yar"tace "an jawoki din me zai sa ki koma zama a cen ba wani jan aji sallon ya raina mu ko?"data lura cewa fada takeji sai ta kyale ta bata ce komai ba, suna cikin hakane suka fito gaba dayansu yayi sallama da Hajiya suka shiga mota suka fice shi kuma ya nufi bakin gate inda yayi parking motar shi ya shiga yayi gaba.

Ba su suka dawo daga kasuwa ba sai da akayi sallan magariba sabida go slow da yayi yawa,kowa a gajiye yake jakukunan ma a mota suka barsu sai da maigadi da masu aiki suka shigo dasu, sallah suka fara da nan sukaci abinci fuhutu suna zaune a living room suna fira wayar fuhutu tayi ringing (BESTY BRO) ta gani a screen din a ranta tace sarkin matsala idan kowa bai kiraba na tabbatar shi zaiyi dauka tayi ta kara a kunne tun kan tayi magana yace

"Kina ina ne baki dawo gida ba tun dazun"tace "ina gidansu jiddah fah" yace "toh gani nan zuwa nazo na daukeki" bata da daman musu sai kawai tace "tau" ya katse wayar ta dubi jiddah"Yau bawan Allah nan ya dawo amma har ya taso mutane a gaba" tana fadan haka jiddah ta gane wa take nufi cigaba da firarsu sukayi anata wasa da dariya da yake hanifah a gidan zata kwana, sallamar da sukaji bakin koface ta katse masu hirarar da sukeyi.

Bayan sun amsa ne ya shigo living room din gaba daya gaida shi sukayi ya amsa yana yiwa kanshi mazauni a daya daga cikin kujerun "ina Hajiyata ne wai ko bata gidan tunda taki ta kirani taji yanda nake toh ni gani na kawo kai na tun daga California sabida ita"ya fada yana dariya, Hajiyace ta shigo tana rike bakinta tace "muryar wa nakeji kamar ta senior, yaushe ka dawo baka fada mun ba"ta fada da mamaki a muryan ta.

"Aa fah Hajiya koh dai tsufa ya fara kamaki ne? Kin manta cewa tun last month na gaya maki cewa zan shigo nigeria"yace ya na dariya "hakane fah manatawa nayi amma dai yanzu yaushe ka dawo? "Tun jiya jirgin mu ya sauka a lagos sai da safen nan muka shigo nan"guri ta samu ta zauna tace "Allah sarki an dawo lafiya, ya kishiyata kuma da mominta ina fatan duk lafiya koh? Yace "Alhamdullahi Hajiya mun gode Allah "

Ta dubi jiddah tace"daukowa yayanki ruwa mana baku san abun daya dace bane har dake fuhutu "har zata tashi yace karta damu dama fuhutu yazo dauka daga nan ya tashi ya nufi kofa,ita kuma ta dauki gyalenta ta biyo bayan shi yace da Hajiya yaushe jirginsu zai tashi tace next week insha Allah yace bakomai da sauran lokaci kenan daga nan suka masu sallama suka wuce gida.

A hanya ba wanda yake yiwa wani magana wakace kawai ke tashia matse take su isa gida sabida taje ta sake wanka, da taga shurun yayi yawa sai ta fitar da wayarta daga cikin jaka yayi daidai da kiran wayarta da akayi murmushi tayi ta daga wayar tace "Aunty mufidah ina wuni" tace "lafiya qalau auta kina tare da senior kuwa inata kiran wayar shi bata zuwa shine na kira Ammi tace mun baya nan yaje ya dauko ki daga gidan Hajiya"tace "Allah sarki gashi na bashi wayan ne?

"No tunda driving yakeyi bari ku isa gida, ki gaya mai idan kuka isa ya kirani please" kanta ta girgiza kaman tana ganinta tukuna ta kashe waya ta dube shi tace "yaya aunty mufidah ce tace wai tayi ta kiran ka baya zuwa shine tace idan ka isa gida ka kirata"

"Toh"kawai yace ya cigaba da tuki har suka isa gida, masallaci ya nufa ita kuma ta shiga gida ba kowa a parlorn sai kawai ta wuce dakinta tayi wanka ta saka kayan baccinta wayanta ta saka a charge, daga nan ta nufi parlorn a dining ta tadda su suna shan kayan fruits jan kujera tayi itama ta zauna aka cigaba da fira har mazan suma suka dawo daga masallaci suka jonasu

__________________________________
√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√√

Long chapters are actually so boring so let's stop here,ina godiya sosai da votes dinku Allah ya saka duk da dai ba wasu masu yawa bane amma ina godiya sosai

Share
Vote
Comment
And
Follow
Thanks 🙏

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now