18

317 35 4
                                    

Vote



Wani iska mai dadi ne ya bugota daidai lokacin data saka kafarta daga matakalar jirgin,jin take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a gida,tafiya take jaye da trolley dinta a hannu,dayan hannun kuma tana rike da karamar fashion bag mata,da ta fito daga VIP ta nufi parking lot din airport din domin taga wanda yazo daukarta

"Oyoyo sis zulfa'u na"rufaida ta fada tare da rungume zulfa,ita ma ta rungume ta firdausi tace "zulfa an dawo lafiya"zulfa ta amma mata da"lafiya qalau Yaya fidodo are you the only ones that come to pick?ta tambaya "eh"suka amsa a tare

"I thought zaku zo tare da su Mami da Yaya Abdallah" dama sun san cewa sai ta tambayi Abdallah firdausi tace "this not the time to ask questions,kizo mu tafi gida tukuna" daga nan driver ya dauki trolley dinta yasa a booth suka shiga motan yaja suka nufi gida

Ta matsu ta ganta a gida ko zataji sanyi,addu'a takeyi Allah ya hadata da rabin ranta ya zaman to da shigarta dashi zata fara haduwa,aikuwa addu'arta ta karbu dan lokaci daya motarsu da ta Abdallah ta shiga gidan,bata gane motarshi ba da yake wace yake daita dah ta sani so ta dauka wani ne ba shiba,bayan anyi parking ta fito a natse ta nufi cikin gidan ba tare da ta kalli motar da ta shigo gidan tare da tasu ba,har zata saka kafarta cikin parlorn sai taji firdausi tace

"Yaya Abdallah ina wuni?ai kuwa da sauri ta juyo dumin bawa idanunta abincin da suka dade suna nema,tsaye kawai tayi tana kallonsa kamar wata statue,gaba daya ya cenza mata kamar ba shiba ya amsa da "lafiya qalau fido yaushe kuka dawo daga lagos tace "Yaya shekaran jiya ne " nodding kanshi yayi yace "yayi kyau ya jikin naki"ya tambaya "da sauki" ta amsa mai

Daga nan ya fice daga gurin ya nufi bangaren shi a gajiye yake,kuma sunyi da manir cewa zasu hadu so he has to freshen up quickly baya so wannan opportunity ya wucesa,is better tun yana da dama yayi amfani da damar tashi.

Ita kuwa ji tayi kamar ta fasa ihu,ta lura bai ma san da ita a gurin ba koh bai san ceawa yau zata dawo bane, hawaye ne ya tara mata a ido

"Shiga ciki mana zulfa me kikeyi a tsaye a nan? firdausi ta tambayeta murmushin yake ta mata tare da shiga cikin parlorn aikuwa tana hango su momy ta tafi da gudu ta rungume ta,tare da fashewa da kuka

"Ke dan Allah daga ni karki karya mun kafa kina abu kamar wata baby"momy ta fada tana tura ta gefe,kara fashewa tayi da kuka tace"dama nasan you didn't miss me tunda baku zo dauka na daga airport ba"

"Who said so?munyi missing dinki sosai ma taso kizo nan"umma ta fada tana dariya,ta tashi ta tafi gurinta tace"gidan nan da kike gani mu kadai ne a ciki kin ga waccen,ta nuna rufaida tafiyar ta tayi gidan firdausi ta barmu mukadai sai yayanku Abdallah,kinga now that you are back the house won't be lonely anymore koh"

jin sunnan Abdallah ya sata jin dadi ta girgiza kanta tare da yin murmushi Mami tace "enough of the talk's kije kici abinci ki huta sai kizo ki bamu labarin school kinji" tace "toh Mami" ta tashi ta nufi dakinta.

Gaba daya an gyara mata dakin nata an cenza mai tsari,ya mata kyau sosai,kayanta ta cire ta saka towel ta shiga bathroom domin yin wanka,ta dade a cikin tukuna ta fito,bayan ta shafa mai ta nemi kaya masu kyau cikin akwatin da tazo dasu saka,sun mata kyau sosai tukuna ta kwanta a gado domin hutawa,koda aka aiko rufaida kiranta,tace sai tace tare dasu daddy zataci,sabida ta tabbatar da kamin su daddy su dawo shima Abdallah ya dawo

Ni kuwa nace iska yana wahalar da mai kayan kara

***********
"Kai fah ni tun dazun na fito inata kiranka baka dauka it's getting late fah" a wayar akace

"Ka tafi gidana kawai mu hadu gani nan zuwa am coming back from work shiyasa" tsaki yayi tare da kashe wayar ya nufi gidan shi,maigadi ya bude main ya shiga ya samu guri yayi parking ya fito ya jingina a jikin motar ganin haka mai gadin ya karabo kusa dashi yace

"Yallabai hajiya tana ciki"murmushi yamai yace "na sani ba ita nazo nema ba"

"Toh"kawai yace tare da komawa bakin aikinsa,bayan mintuna kadan sai ga manir din yazo,kin kallon shi yayi shi dariya ma yake bashi yace "idan ka gama tsayuwar you can come in,naga dai gidan ba bakon ka bane da zaka wani tsaya a waje,na lura so kake mutane suce I don't respect my in-laws"ya fada tare da shige wa cikin parlorn bakin

Shi kuwa Abdallah koh amsa shi bai yiba,yabi bayan shi suka shiga parlorn,ya samu guri ya zauna "ina zuwa bari na shiga gidan na fito"manir ya fada yana niyan tashi Abdallah yace"ba inda zaka ka tsaida ni tun dazun and now you're finally here Kuma Wai kace mun kana zuwa, come on sit down let's talk" ya fada tare da maida shi gurin da yayi niyan tashi

"Kanwarka fa zan gayawa kazo"manir ya fada jicin zolaya ,tsaki yayi "kanwar tawa yau na fara ganinta ne please ka natsu muyi magana" ya fada a hasale "ina jinka"

"Dama zuwa nayi ka kaini gidansu yarinyar nan,she's been on my mind all this while,in Kuma ba zaka kaini ba ka mun kwatance sai inje ni kadai,i really want to get married to her as early as possible"kura mashi ido yayi na wasu yan mintuna ba tare da yace komai ba,cen kuma ya kwashe da dariya.

Bakin ciki kamar zai kashe Abdallah wato abun dariya ma ya maida shi,fushi yayi tare da tashi zai bar parlorn manir yayi saurin riko shi yana gimste dariyar shi yace

"yanda kaki bayani ne yake bani dariya, magana kake kamar an tabbatar maka cewa gidansu ba'a mata miji ba"aikuwa nan taka gaban shi ya buga yace "a yanda na ganta,bana tunanin an mata mijin,my heart will never fall in love with someone that is not meant for me"ya fada cike da gwarin gwaiwa sai daya bawa manir tausayi yace

"Wai khalifah ya san da wannan maganar kuwa? Yace"ai daya sani shi zai fini damuwa akan abun,so he has no idea kawai dai yanzu ka gaya mun abunda zamuyi"manir ya danyi shuru na yan mintuna kamin yace

"Eh to kaga fuhutu kanwata ce jini ne kawai bamu hada da gidansu ba amma,we all grow up together zumuntace mai karfi tsaka nin mu dasu,so tunda kamun maganar kamar kayiwa mujahid ne babban yayansu,do not bother your self gobe insha Allahu zan kira mujahid in gaya mai duk yanda yace toh zan kira ka" ajiyar zuciya yayi tare da yi mai godiya

Sannan suka fito daga cikin parlorn manir yace "dan Allah ka tsaya na kira maka maman daddy ku gaisa idan ba haka ba wallahi rigima zata mun duk na gaya mata cewa kazo gidan nan" har Abdallah zai bashi amsa sai gashi ta fito tace "lah Yaya yaushe kazo?har manir zaiyi magana Abdallah yayi saurin tararshi yace "yanzu na wallahi kuma zan wuce dama sako nazo karba gun manir"

Kallon tuhuma ta dinga musu kamin tace "ok zulfa'u ta dawo koh?ta tambaya tana kallon yayanta kallon daya mata ne yasa ta gane bai san ta dawo ba ta rasa gane wace irin rashin jituwa ne ke tsakanin yayan da kanwarshi tace "zulfa'un mu nake magana Mami ta kirani not more than 1hour ago cewa ta dawo,saura su hasinah wai jirgin su sai dadadare zai sauka a Lagos"

"Allah sarki maybe bayan na fito ne ta dawo ban saniba"dama ta san maganar ba zata wuce haka ba daga nan ya musu sallama ya tafiyar shi.

______________________________

Vote
Share
Comment
And
Follow

                  Mairo❤️









Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now