24

356 41 3
                                    

                 A gurguje

Not edited
Bayan wata biyu

Bayan wata biyu din nan abubuwa sun faru ciki kuwa har da saka ranar auren jiddah da Yaya mujahid,fuhutulkhairi da Abdallah, Adamu da saleemah(mahmah kenan), zulfa'u kuma da khalifah hehehe nima dai abun ya bani mamaki wai mace da suna isah namiji da suna hajara.

Mujahid yaje ya samu daddy mahaifin jiddah ya gayamai cewa yana son jiddah zai aureta,shi kuma yace idan da kara ai bashi ne zai bashi fuhutu ba daddynsu ne yakeda wannan alhakin,mujahid ba haka yaso ba dan da niyarshi sai ya gama tsayar da maganar auren tukuna Ammi zata sani amma yanzu idan yaje gun daddy neman auren jiddah ai kamar gurin Ammi ne,kuma matukar ta sani toh hamidah ma sani zatayi shikenan Kuma asirin shi ya tonu  haka dai ya daure yaje ya sami Hamidah cikin lalama zai mata bayani amma Ina taki ta saurare shi.

Yaci amanarta kawai take cewa bakaken maganganu kuwa na safe daban na rana dama tun baya biye mata har ta fara kaishi kull,ya dinga taka mata burki dan yaga abun bai tsaya akan shiba har Ammi yiwa takeyi,bayan yaje ya samu daddy da maganar sai yace mai bakomai indai zai iya yin adalci a tsakanin su toh bashi da matsala zasu tatauna za daddyn jiddah duk yadda suka yanke zasu sanar dashi,haka dai akayi tayi aka bashi ita ya biya sadaki aka sa bukin zuwa wata hudu bayan sun gama exams din shiga aji uku.

Jiddah ta rasa abunda takeji dadine koh fargabar auren mai mata,gashi tunda suke da aunty hamidah kallon arziki baya hada su,idanma ta gaida ita sai taga dama take amsawa balle har ace wai auren miji daya ya hadasu harda zama gida daya toh sai ya kenan,wata rana har addu'a take ina ma itace autar Ammi wato fuhutu da bata tsoron fada da kowa ma indai kaki kama mutuncinka,nidai nace haka zaki mamatse ki zauna da ita.

********
Abdallah kuwa bayan ya kira manir sai yace mai ai ya yiwa yayan fuhutu magana yace bakomai amma idan ya shirya Kuma dagaske yakeyi toh yaje gurin daddyn su ayi magana,ya kuwa tafi shida khalifah suka kai gaisuwa da zasu suka tafi da kudin gaisuwa da kuma turare daddy ya tarbesu da kyau kuwa tambayes cewa ita fuhutun ce tace yazo,yace aa neman izinin zuwa ganinta da kuma aurenta yakeso,daddy bakomai ya dinga zuwa din idan suka daidai zai gayawa yan uwanta da kuma magabatanshi komai sukace za'a sanar dashi.

Mujahid kuwa ya Kira fuhutu ya bata shawara yace"autan Ammi"tace"na'am

"Shekararki nawa ne yanzu"tamai kallon mamaki dan tasan cikin gidan nan kowa yasan age din dan uwansa"tambayarki nakeyi fah"tace"am 20"

"Which means ke ba yarinya bace yanzu akallah kinyi hankali da zaki zauna a wani guri ba tare da iyayenki isn't it?he asked ta daga mai kai"wani ne yazo neman aurenki"cikin kidima ta kalle shi"aurena kuma yaya when and how?the last time I checked ban sauraren kowa balle har nace mai yazo gidan mu,it can be possible bani yakeso ba"ta fada a tsorace cikin sauri.

"Calm down baby sis you don't need to freak out,abokina ne kuma yayan matar manir ne so you got nothing to fear trust me,he will take care of you bazai cutar dake ba"kara zaro ido tayi tana so ta kara gasgata abunda taji tace"Yaya kace wayeshi?ta tambaya

"Yayan maman Little ne"ya bata amsa na shiga uku ta fada a ranta idan dai ita mai hankalice to ya kamata ta gane cewa ba kowa Yaya mujahid ke nufi ba face Abdallah dan shi kadai ta sani as yayan aunty hanifa da tayi shuru yace "so ki kwantar da hankalinki you will get to know him the guy is nice,idan ma kuka tatauna kika ga bai maki ba koh yayi something bad ni dakaina zan rabaku ok?and kinga zainab bukin ta in 2weeks  coming ne so gidan bazai maki dadi ba,itam jiddah kin san an tsayar da ranar bukin mu nan da 4months so is better,kema ki samu gurin zama mai kyau" fada yana tashi daga balcony din ya nufi cikin gida.

Haka dai tayita tunanin yadda zata mai walakanci amma da yazo sai ta kasa,cikin abinda ba gaza sati biyu ba suka shaku sosai idan ka gansu zaka dauka cewa sunyi shekara koh shekaru ma tare,da idan akace mata waye Abdallah zatace wani miskilin mutum da mai girman kai da Jan aji zata ma iya rantse cewa yana da son mata,amma data saba dashi sai taga ba haka bane yana da saukin kai sosai idan ka fahimce shi

Shima Abdallah kusan hakance ta faru ya dauka zata mai fitsara ne amma ina, lafiya lau suke muamalarsu gata da shagwaba kamar yarinya idan tayi abu wata rana koh little ba zaiyi ba balle rufaida,ga da banzan fada matukar aka fada mata ba daidai  ba toh sai ta fada maka mai zafi itama tukuna hankalinta zai kwanta bayan shi ba wata matsala

Mami ji take kamar zata jawo ranar bukin dan mafalkinta ne ya zamo gaskiya na son ganin Abdallah yayi aure,momy ma sosai taji dadi dan dama abunda takeso kenan yayi niyar auren koh zulfa'u zata fidashi daga ranta,amma Ina kamar kara mata sonshi akeyi har data koma makaranta ma duk sukayi waya da momy sai ta tambayi yayan nata.

ganin haka yasa momy ta kara tunawa abbanta maganar da sukayi kwanaki ta Adamu daya Kira zulfa a waya yace tana sonshi tace aa bata son shi,gashi Kuma khalifah ya matsawa Abdallah akan maganar zulfa'u sai kawai ya fadawa su abba,daddy yace tunda hakane an bawa khalifah zulfa'u shi kuma Adamu an bashi saleemah(mamah)kenan,ganin cewa duka yaran yayansu ne kuma ba bambanci a tsakanin su yasa suka yanke wannan hukuncin ba tare da sun nemi shawararsu ba.

Da aka fadawa zulfa'u cewa an mata miji haukar da tayi tafi ta lokacin da taji cewa Abdallah zai aure wata ba itaba,sabida niyarta zata zauna takiyin auren inya so daga bayan ai za'a sashi dole ya aureta amma da taji cewa khalifah ne zata aura ba Adamu ba sai tayi wani tunani ai idan ta aureshi kamar ta auri Abdallah ne.

Hasbinallahu

Duniya ina zaki damu ni kam nace Allah ya rabamu da zuciyar da bata daukan kaddara,wannan tunanin ne yasa taji sauki ta daina damuwar kanta,shi kuwa adamu sosai ma yaji dadin musanyawar da kayi dan yasan cewa koda ya auretan kamar yanda yakeso ba zaiji dadin zama da itaba so wannan ne yafi zama alkhairi, saleemah kuwa bata damuba indai zai barta tacigaba da karatunta.

_____________________________

Anzo gurin kenan hahaha wa yaga jiddah da hamidah a gida daya

Me zai faru idan zulfa'u ta gane cewa fuhutuce wadda yayanta zai aura

Idan kuna so kuji wadan nan amsoshi to kuyi abun daya dace wato

Vote
Comment
Share
And
Follow

Godiya nake

                    Mairo❤️

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now