21

304 35 4
                                    

Koh mintuna talatin batayi da komawa dakinta ba, jiddah ta shigo gidan cikin sauri tace"bestie let's get going inah Ammi? fuhutu ta tashi ta dauki gyalenta tace"tana dakinta of course"

"Toh muje na gaida ita kafin Yaya ya kama mu"fuhutu ta tabe baki"ai we took permission before going,ba zai hana mu ba"ba tare da ta amsa taba taja hannunta suka nufi dakin Ammi da sallama jiddah ta shiga dakin dan fuhutu tace ba zata shiga ba"Ammi Ina kwana"ta fada tana rusunawa"lafiya qalau hauwa'u an tashi lafiya,ya hajiyarku?tace"lafiya qalau Ammi"

"Yayi kyau dan Allah hauwa'u kar kuyi dare kinji karki biyewa auta kin san kin fita hankali ok?tace"ba zamu dade ba"tace toh a dawo lafiya" daga nan ta tashi tafita,fuhutu ta karbi motar taja suka tafi,salon suka nufa jiddah tace"Ina ga nima ya kamata na gyara kaina,duk ya wani cunkushe"fuhutu tace"kanki akeji yarinya"daga nan suka cigaba da tafiya suna hirarsu abinsu.

Bayan sun isa salon din suka fita suka nufi ciki,daga gani kuwa an saba dasu sosai a gurin dan sai faran,faran ake tayi dasu,basu suka gama ba sai gurin karfe biyu, jiddah tace "muje gidan aunty hanifah muyi wanka dama na fito ma da wasu kayan,suna mota " fuhutu ta kyalleta tace"lallai bestie a shirye kika fito kenan"tayi dariya tace"sosai ma kuwa" daga nan suka bar harabar salon din.

Koh da suka isa gidan hanifah ance bata gida, little daddy kawai ne da nanny dinshi,wanka sukayi da Kuma sallah kamin mai aikin gidan ta kawo masu abinci,bayan sun gama shiryawa sai suka tsaya jiranta,sai wuraren hudu da rabi har sun fara bacci kamin ta dawo.

"Aa lallai mutanena yau kune a gidan nawa ai na dauka koh kun manta hanya ne" hanifah ta fada cikin zolaye, jiddah tace"aunty hanifah bama son zolaya kinfi kowa sani cewa hanamu fita akayi ai da tuni kin ganmu a gidanki dan kinsan muna zuwa idan da lokaci"tace"ai kam nanny tace kun jima da zuwa"ta fada tana duba fuhutu

"Eh mun jima Kuma yanzu fita zamuyi aunty"tace"ina kuma zaku maraice ya gabato,kuda da ma kuka fito daker so kuke kuyi wani laifin koh"jiddah tace"ba zamuyi ba insha Allah yanzun nan zamu dawo dama shopping zamuje da kuma zaga gari kadan ba wani abu ba"hanifah tace

"A dawo lafiya kardai ayi dare idan ba haka ba,ba zan kare ku ba idan wani abu ya faru"fuhutu tace"ba abun da zai faru sai alkhairi a shirya mun daddy dashi zamu"tace "ok bari yanzu za'a kawo shi"daga nan ta tashi ta fita.

*********
"Rufaida Wai shirin ne har yanzu kamar wadda zata canza fata,dan Allah ki fito mu tafi kinga lokaci yana tafiya kafin umma tayin changing mind dinta,ta hana ni fitan nan"rufaida dake gaban madubi a tsaye tana shafa mascara a idonta tace"sister zulfa na gama mana Kuma naga su sister hafsat da mamah basu shiryaba,da yake jiya dadare suka dawo bayan sun sauka a Lagos State sunyi kuana daya,so koh hutawa basuyi ba zasu fita yawo yau zulfa'u tace

"Shi wai dole ne sai mun tafi dasu the last time I checked ba mota daya bace a gidan nan so idan zaki zo mutafi toh idan Kuma ba zaki ba I can go alone it's not a problem"ta fada tare da fita daga dakin,ganin haka yasa rufaida daukar dankwalinta da yake kan bed ta biyo bayanta Koda suka fito mah already suna waje suna jiransu koh kallon gafen kannen nata batayi ba suma kuma ba damuwa sukayi ba dan idan da sabo sun saba da halinta.

Motarta ta nufa wadda aka riga aka wanke mata walkiya kawai takeyi,bayan ta shiga ta kunna AC tare da saka waka,glass ta sauke tare masu hannu alamun su shigo su tafi rufaida ta shiga gurin mai zaman bazan,su mamah suka zauna a baya su uku taja motar da gudu suka bar gidan,labari kawai sukeyi a tsakanin su bata tanka suba titin take kallo,mall ta nufa dasu parking tayi kowa ya fito suka shiga ciki kowa ya dauki shopping cart dinshi suka fara daukan abubuwan da suke so, zulfa'u kuwa ta nufi gefen turaruka tana cewa suyi sauri if not idan ta kare tafiyarta zatayi.

**********
Bayan sun isa mall din suka shiga ciki fuhutu tace "jawo Carter din dan kinga ina rike da little"jiddah ta harareta tace"gani yar aiki koh wallahi gara maki dauki naki dan bazan daukar miki ba"ta fada tare da janyo shopping cart daya tayi gaba fuhutu tace"zaki gani sai na rama"tai mata qwalo tace"ki rama din" ta wuce abunta sukabi bayanta ita da little daukan abubuwa kawai suke tayi har suka zo gurin turaruka,zubawa kawai sukeyi a cart kamar ba da kudi ake siyaba, daidai jiddah ta saka hannunta zaka dauki wani turare da take ta nema sai Allah yasa yau ta ganshi daidai lokacin taji wani hannu kan nata,tama dauka fuhutu ce amma data juyo taga ba ita bace.

Yarinyace yar gayu wace ba zata wuce shekarunta ba sai wani cika takeyi tana batsewa tsayuwa tayi tana kallon ikon Allah, fuhutu madai sai kallon su takeyi
Kowa da hannun shi kan turare yaki ya sauke har zatayi magana sai taji yarinyar ta cewa jiddah"excuse me please turaren nake so" ta fada rudely jiddah tace"ban gane turaren kike so ba, what do want me to about it?ta tambaya itama a yanda ta mata maganar,ta gyara tsayuwa tace"ina son turaren ne shiyasa nace maki haka kuma na rigaki daukan turaren so please get your hands off it sauri nakeyi don't waste my time"jiddah zata bata amsa kenan fuhutu tace"and what if she didn't give you,what will you do?da dan karfi alamun ranta ya fara baci.

_________________________





Ta ina zan fara ne wai amun hakuri 🙏dan Allah
Bana jin dadine shiyasa banyi update ba kwana biyu
So barkan mu da sabuwar shekara Allah ya hada mu da Alkhairin dake cikinta nagode

Vote
Comment
Share
And
Follow





                   Mairo❤️

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now