20

337 38 2
                                    

Bayan ya gama shiryawa ya fito daga part dinshi kai tsaye parking lot ya nufa dan sauri yakeyi yana da abubuwan da zai yi yau da yawa,akwai files din da wani campany ya kawo masu da yake so ya duba gashi Kuma daddy yace su same shi a office yau amma ya Kira dan rainin wayon nan baya dauka,ga kuma maganar da sukayi da manir yana jiran feedback dinshi tsaki yayi tare da kunna motar mai gadi ya bude mai ya fita daga gidan.

Gidansu khalifah ya nufa bai damu da shiga da motar ciki ba a waje yayi parking ya shiga cikin gidan suka gaisa da mai gadi,kam ya nufi part dinshi sallama yayi ya shiga ba'a amsa mashi ba,alamun ba kowa a parlorn guri ya samu ya zauna tare da daukan remote domin cenza tasha.

Bayan mintuna 15 sai gashi ya fito a shirya cikin suits masu kyau kallon Abdallah yayi yace "good morning Mr C.E.O with what do I owe this early morning visit"ba tare da ya bashi amsar tambayar shi ba yace"baka ga kirana bane?

"Na gani mana ina tunani kiranka ne na sameka a nan" tashi yayi daga zaunen yace "ok seems like ka riga da kasan cewa daddy yana neman mu so let's getting going I have things to do"
Ya fada yana fita daga parlorn ba tare da ya amsa shiba yabi bayan shi suka fita zuwa harabar gidan,har khalifah zai shiga tashi motar sai Abdallah yace" kazo mu shiga tawa ina da maganar da zamuyi da kai" kulle motar yayi yabi shi suka nufi wajen gidan inda yayi parking motar,yaja suka fice daga unguwar a kalla yayi mintuna talatin kafin yayi magana har sai da khalifah ya fara gajiya da jiran shi yace

"Dude can you please talk to me kafin mu isa office,ka dai san cewa muna da aiki a office yau Kuma we have a meeting da investors din nan"

"Allow me to take my time mana Ina tunanin ta inda zan fara ne"ya koma yin shuru kamin ya sake cewa"zaka iya tunana washe garin ranar da na dawo,dana raka ka gurin wani lecturer a makarantar su Salim toh ranar na hadu da ita"

"Dama na san cewa akwai wani abu da kake boyewa cause tun randa muka tafi school din nan da Kuma randa kaje ka yiwa little daddy shopping na san cewa akwai wani abu but you refuse to tell me,kamar ba danuwanka nake ba,Koda bamu hada jini da kai ba Abdallah na tabbatar bayan Mami da daddy nafi kowa kusanci dakai amma....."har zai cigaba Abdallah yayi saurin katse shi

"Kai danuwa nane kog naki koh naso ba mutanen dake da alaka ta jini kawai ne yanuwan juna ba khalifah,kai ne kawai ka dauki maganar a baibai wallahi zan iya ranstewa cewa yarinyar bata ma san ina yiba,I was just trying to come to the root of the matter kamin na sanar da kai,but na lura abun yaci tura and the problem is I can even face her in gaya mata cewa ina sonta ba cause ina ganin yarinta a jikinta sosai and she's also a pampered girl"

"Wannan ba shi zai hana kaba akwai dai wani abu,or are you scared of rejection? Ya tambaya da wasa murmushi yayi yace"no am not kawai dai na kasane"

"Ohhh is that why you have being meeting manir to discuss about it while ni gani nan this shows that am of no use koh"dafe kanshi yayi tare da samun gefen titi ya tsayar da motar "this is exactly abunda yasa naki gaya maka you worry too much,Kuma ba wai dan ba zaka iya yin komai akai bane ya sani naki fada maka,I just feel is the best and you also have things to do with your life shiyasa"

"Hmmm naji but karka sake mun haka at least you can tell me sai mu san yanda zamu fito mata,but karka damu we will come up with a plan, cause ba macen da zata ga danuwa na bataji tana sonshi ba"ya fada da zolaya "you aren't serious Allah"Abdallah ya fada tare da tada motar suka wuce.

***********

Yau ta koduri aniyar cewa sai ta fita, sun riga da sunyi waya da fuhutu so they came up with a plan of how to go out su dan ji dadin rayuwar su,so bayan ta gama breakfast taje tayi wanka ta saka kayan zaman gida, sai data tabbatar da cewa hajiya da daddynta suna zaune tare a parlorn tukuna ta shiga ta zauna,ta fara mutsu,mutsu daddy yace

"Mamana da magana ne?naga kamar bakin ki yana so ya fadi wani abu, tell me now what is it?sai data dago ta dubi hajiya ta koma sauke kanta kasa kamin tace"daddy dama Ina so inje shopping ne kuma hajiya ta hana ni zuwa and I really need to go get somethings at the mall"

Tun kamin daddy ya amsata hajiya tace"kaji mun wannan yarinyar da munafurci ba fa nice na hanata fita ba yayansu mujahid ne ya hana su fita ita da autan hajiya"daddy yace"ahhh to lallai kuwa tunda yayanku ya hana sai kuyi zaman ku,kikira yayanku manir koh driver ki mai list yaje ya karbo maki abubuwan da kike so"kamar zatayi kuka tace

"Wallahi daddy ba zai siyo mun yanda nake so ba kawai kace inje i promise I won't stay long Allah"yace "toh shikenan you can go amma fah kar kiyi dare" ai kuwa da gudu tazo tayi hugging din shi tace"Thanks daddy"sannan ta koma da gudu tayi dakinta

daddy ya dubi hajiya tace"ni gani nake kamar mujahid ya son yarinyar nan"tace "ai kuwa tun ba yau ba,sabida idan zan iya tunawa tun ta karama yake sonta kawai dai a lokacin da zaiyi aure yaga bata girma bane shiyasa amma tunda har ya aza dokar karya bari ta fita duk da ba ita kadai ya kafawa ba sabida kar a zarge shi but you can see it all over him cewa sabida ita yayi hakan kawai abunda nake gudu hamidah bayan shi ba suda wata matsala,kuma kamar ita yarinyar bata san yana sonta ba"daddy yace

"Duk ma dai ya abun yake Allah yasa ya zama alkhairi ,matar shi ba zata iya hana komai faruwa  ba addu'a kawai zamu masu"daga nan ya tashi ya dauki office bag dinshi ya wuce office,hajiya ta mai a dawo lafiya.

Bayan ta shiga dakinta ta dauki waya ta kira bestien ta,tana dauka tace "an barki ki fita kenan koh? fuhutu ta tambaya"of course yes sai ki shirya mu tafi karfe 10:00 zan fito"ta bata amsa excitedly

"Yeeeh kice today will be fun kenan?,let me get ready by 10:00 din sai mu fita ina so mu tafi saloon kafin muje mall"

"Toh shikenan bye"

"Bye

********
Bayan ta aje wayanta ta shiga toilet domin yin wanka,bayan ta fito ta shirya,riga da wando ta saka ta aza maron din jallabiya mai design,bata damu da tayi kwalliya ba ta nufi dakin Ammi sallama tayi ta shiga,a zaune ta tadda ita ta duba wasu takardu da alama na yan makaranta ne.

"Autana ya akayi? Ammi ta tambaya tana ajiye papers din hannunta kusa da ita fuhutu ta zauna tace "Ammi please zamu fita by 10:00 nida jiddah we ain't gonna stay long I promise"Ammi tace"niba ruwana kijeki gayawa yayanku idan yace ki tafi sai kije"ta marairaice fuska tace

"Naje side dinshi basu tashi ba kuma kin san idan yana baccin safe ba'a tashinsa,ni kawai kice na tafi idan ya fito ki gayamai kuma ma daddy yace jiddah ta tafi ni kadai na rage"

"Ahh tunda shi daddy ya bari hauwa'u ta fita toh kuje kawai amma fah kar ayi dare kinji koh"ta amsa mata da "we won't insha Allah" daga nan ta koma dakinta tana jiran jiddah tazo su tafi

______________________________

Ina kwanan ku mutane na da fatar kun tashi lafiya


Vote
Share
And
Comment

                       
                           Mairo❤️

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now