7

400 37 2
                                    

Marmiee-suleeman

Suna shiga hamida ta nufi Ammi ta rungume ta tare da cewa"ina kwana Ammina? Mun sameku lafiya? "Lafiya kalau hamida ya gajiyar hanya? " Mun gode Allah" ta fada tare da zamewa ta koma kasa kusa da Ammi ta zauna. Shi kuwa gogan namu tsaye yayi yaki karasowa, da yaga ba wanda ya kulashi sai yace "toh bari na juya tunda ba wanda yaji dadin ganina a gidan nan"

Fuhutu dake shigowa cikin parlor dauke da akwatuna tace a ranta "wa zaiji dadin ganinka ka dawo da mugun hali" wucewa tayi ciki don ta ajiye masu akwatunan nasu a dakin da ya zamo masaukin su a duk lokacin da suka sauka a gidan, su Ahmad kuwa dariya sukayi sabida sun san cewa ba dasu yakeyi ba.

Ammi kuwa bakomai ya hanata kyale shiba sai sabida kunya dake tsakanin dan fari da uwarshi, ita dai a duk lokacin da baya kusa daita sai taji ta damu amma idan yazo sai taji bata iya nuna mai kaunar da take mai a matsayin danta na fari.

Murmushi tayi, ta cigaba da wasa da baby (Elham)ba tare da tace komai ba,da yaga bata ansashi ba sai ya wuce dakin da aka ajiye masu akwatunan su, kayan shi ya cire don yin wanka ya daura towel ya shiga toilet.

A parlor bayan ya wuce hirace ta barke dariya kawai ke tashi, Ammi da taga ya dade bai dawo ba tace "hamida tashi kije ki duba shi yazo kuci abinci lokaci yana wucewa" tashi tayi tace "to Ammi bari na dubo shi" tana wucewa zainab tace "nifa na fara kishi da yayah Allah, sabida duk gidan nan anfi jidashi, abinda Ammi take mai koh auta bata yiwa" ta fada tana tunzuro bakinta.

"Ki bari kawai yaya abu idan baya kusa nice da kujerar auta amma idan ya dawo saukeni akeyi ya zauna akai" fuhutu ta fada kamar zatayi kuka, dariya akai gaba daya Ahmad yace "Ammi kin daiji abunda auta ta fada ya kamata a dinga mata adalci", wallahi kuwa ya kamata sabida nima dai bazan boye ba kishi nake da yaya sai wani pampering dinshi akeyi kamar wani yaro bayan yayi aure harda diya" ita jiddah dariya suke bata,

Ammi kuwa koh kallo basu isheta ba wasa ma takeyi da kishiyarta daga baya dasuka isheta da tsokana cewa tayi "duk wanda yake kishi da yaya toh ya bar gidan bata son sa ido, ai kuwa me jiddah zatayi inba dariya ba sai yanzu tayi magana tace "kun daiji an koreku" hirar daice suka cigaba dayi.

Tana shiga ta tadah ya fito daga wanka yana goge jikinshi da towel,karba tayi daga hanunshi tace "abba kawo na tayaka" sake mata towel din yayi ba tare da yace komai ba, ita kuwa ta san fushi yakeyi da ita sabida tace kwana biyu kawai zatayi a nan bayan kwana biyun gidansu zata koma, ita dai bataga abun fushi a nan ba sabida ba yanda za'ayi ace tazo nigeria zatayi fiye da wata biyu ace bazata kwana a gidansu ba koh da sau daya ne, ya kasa ganewa lalaba shi kawai takeyi amma abun ya fara bata mata rai haba sai kace shi kadai ne da dangi.

Tana goge mai jikinshi ta taya shi shafa mayukan shi ta sake jawo daya daga cikin akwatunan ta bude ta dauko mai kananan kaya polo shirt ce red da wando baki, ta taya shi sakawa dama already yanada takalma a gidan sabida yana yawan zuwa gida duk bayan wata biyu, dubawa tayi a cikinsu ta bashi wasu designed loafers masu kyau da sukayi matching da kayan shi yasaka.duban shi tayi tareda yin murmushi a ranta tace masha Allah koh ba'a fada ba tasan mijinta kyakyawane"now u are good to go" ta fada tana aza hannunta a kirjinshi

Yace "are you sure? Cause I can see there's something you didn't do" bayan shi tazo ta kwantar da kanta da yake ya juya mata bayane yana kallon mirror tace "what is left behind da baka saka ba Abba? Murmushi yayi tare da daukan wata qwalba mai bala'in kyau daga kan mirror ya daga sama.

yace "this is left behind ummi" dagowa tayi daga bayan shi ta kalli qwalbar daya daga sama, murmushi ya kwace mata tace"oops na manta ne Allah" yace "nasani shiyasa ta tuna maki"karba tayi daga hannunshi turaren ne mai kamshi sosai ta fesa mashi a ko'ina na jikinshi,har zata ajiye ya karba zai fesa mata ta girgiza kai tace "no Abba mutafi su Ammi suna jiran mu kuma kaga lokaci yana hucewa" ta jawo mai hannu suka nufi kofah.

Shi kuwa mujahid a kullum mamaki yake yanda za'ace mace bata son saka turare, hamida ta daya daga cikin matan da basu damu da turareba ba wai zaice tana wari bane aa batayi amma shi yana daya daga cikin mazan da suke son kamshi sosai,yana so yaji mace tana kamshi yafi son duki juyin da mace zatayi a duniya ace kamshine ke fita.

But sai Allah yazo ya bashi matar da bata son turara ita dai da tayi wanka ta shafa mai sure ne kawai ya zama dole tasa a hamutan ta amma bayan shi bata son mu'amala da duk wani abun mai kamshi tana da turaruka birjid a gida amma basuda amfani,tun yana kawaice na rashi nuna mata har ya fito ya nuna mata ga abinda yake so amma taki ta cenza ido kawai ya saka mata yanzu.

Ammi ta daga ido da dube agogo dake manne a bagon palor mai kyau tace"lokaci yana wucewa fah auta jeki ki kirowo yayanku", "toh" tace tare da tashi domin itama dai ta gaji da jiransu har ta kusa kaiwa dakinsu sai gasu sun fito hanunsu sarke da juna suna hira kasa kasa da alama abun dariya suke magana akai yanda suketa dariya sai suka bata sha'awa amma daya autar Ammi masifaface sai,,

tace " yaya ance kuyi sauri kuzo ku kadai ake jira" dayake ya san halin kanwar tashi ga kuma rashin jituwar dake tsakanin tada hamida,sabida ya bata haushi sai yace "munce ku jira mune?bamu ceba sabida haka baza mu zoba sai munga dama koh ummi" ya fada yana kallon hamida tace "eh" ai kuwa fuhutu ta suke hararar su tayi tare da juyawa tayi tafiyar ta tana cewa "kar kuzo mana ku kwana a nan jarababu kawai " murmushi kawai yayi suka biyo bayan ta.

Ta shigo parlor tana ta cika tana batsewa da yake kowa yan halinta kuma sun san bata yawan yin haka sai idan yayansu yana gari sabida basa shiri sosai dashi, suna mugun son juna cause she's his favorite among his siblings amma kullum basa wuni daya sai sunyi fada,ita bata ganin abu ta kyale indai bai mata ba shikuma duk tayi magana sai ya gwaleta.suna shigowa kowa ya tashi aka nufi dining table dayake kaidah ne a gidan duk wadda ta dafa abinci ita zatayi serving amma yawu kam fuhutu tayi breaking rules, cause zamanta tayi taki tashi Ammi tace "tashi kiyi serving mana auta kin wani zauna" baki ta kunburo tace " hannuna ke ciwo"
"Allah ya shirya"daga nan ta dubi zainab tace "abu jeki kira mun mairo tazo tayi serving " har zainab zata tashi jiddah ta rike mata hannu tace

"Barshi kawai ni zanyi" tashi tayi ta dauki plate Ammi ta fara zubawa sannan yaya sai ta sakawa sauran dama kanta tukuna ta zauna "Allah yayi miki albarka"Ammi tace "Amin ya rabbi Ammina... Daga nan sai kowa ya fara cin abinci amma fah akwai mutun guda daya kasa daukan koda spoon ne.

Mamaki yakeyi dama haka take da kyau kokuwa bai taba lura bane, daka ganta zakaga mace mai tsafta yanayinta kadai ya isah ya fada maka hakan da tazo kusa dashi kuwa jin yayi kamar nufashin shi zai dauke sabida kamshi dadaden turarenta, hannuwanta kuwa yan chas dasu gashi sun sha lalle ja'a sai walkiya sukeyi, fuskarta fayau ba kulliya amma haka bai hanashi ganin kyaunta ba gashi tanada jiki mai kyau wanda duk namijin daya gani zaiyi sha'awar ta zamo abokiyar rayuwarshi, duk da kayan da tasa ba masu nuna tsiraici bane atampa ce mai kyau aka mata doguwar riga daga sama har kasa stone work ne sai tasa gyalen da yayi matching da kayan amma hakan bai hana lafiyayun hips dinta fitowa ba, wanda hakan yasa yaji kishinta har cikin zuciyar shi.

Waye ya kasa cin abinci?
mujahid koh
Yaxid
Koh kuma
Ahmad
Wacece wannan da aketa wasawa haka?
Kubiyoni domin jin amsoshinku

🙏 Thanks

Share
Vote
Follow
And
Comment

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now