8

378 33 0
                                    

MARYAM❤(marmiee)

Bari mu leko su Abdallah

Kiran sallah ne ya tasha shi daga baci, a gurguga ya tashi ya shiga toilet ya dauro alwala ya wuce masallaci dake a gaban gidan nasu a cen ya hadu da daddyn shi yamai sannu da dawowa,sai da gari ya fara wayewa bayan ya gama azkar dinshi tukuna ya shiga gida sanin cewa idan ana weekend koh kuma hutu ba'a saurin tashi a gidan shi ya sashi komawa site dinshi,kan gado ya fada yaja duvet ya rufe jikinshi sabida har yanzu da sauran bacci a idonshi.

Sai 11 na safe ya tashi yayi wanka ya shirya a cikin kaftan mai kyau yasa hula akai ya fito, side din mami ya nufa, da alama itadinma bata dade da tashi ba sabida yaga sai yanzu yan aiki suke gyara parlour nata,gaida shi sukayi ya amsa da fara'a a fuskarshi tare da tambayarsu inda mami take sukace tana bedroom dinta kofar yanufa yayi knocking tare da yin sallama,sai da ta bashi izinin shigowa tukuna ya tura kofar.

Zaune ya tadda ita kan kujerar mirror tana daura dankwalin kayanta,a kullum mamaki yakeyi yanda take kokari gurin gayara kanta duk da cewa tanada irinshi a matsayin danta,idan ka ganta ba zaka taba cewa ta haifeshi ba sabida yanda take maintaining jikinta, baby face dinta yake kara boye shekarunta ba abunda wata budurwar zata gwada mata idan ba kuruciyaba,he has always been proud to call her his mother.

"Mamu good morning" ya fada yana samawa kanshi mazauni akan daya daga cikin chair din dake cikin bedroom din "morning dear an tashi lafiya? "Lafiya qalau" ya amsa duban shi tayi tace "kaje ka gaida baban naku kuwa" yace "eh mun gaisa tun a masallaci", "yayi kyau ni zan wuce kitchen sabida yau na makara banyi saurin tashi ba ina so muyi setting table kamin kowa ya fito gashi kuma 12 ta kusa" ta fada tana tashi tare da nufan kofar dakin, shima tashi yayi yabi bayanta yana murmushi yace "toh mamu bari na gaida mutanen gidan", "toh" kawai tace ta nufi hanyar kitchen din shikuma ya nufi dayan side din.

Side din momy ya fara shiga itama kusan yanzu ta tashi sabida a kofar bedroom ya hadu da ita,murmushi tayi mai tace "son sai ina haka wannan gayu tunda sasafa"murmushin ya mayar mata yace "momy good mornig kuma ba inda zani karkisa mutana suji su dauka ko bana gayu ne dama" ya fada a shagwabe ai kuwa me zatayi idan ba dariya ba tace "no son that's not what i mean kowa ma yasan you always lookout every day but na yau is a little bit different u know" smiling kawai yayi baice komai ba cause shi kadai ya san abunda ya tuna..

"Abdallah" momy ta kira shi tana kallon cikin kwayar idon shi,duk da ba ita ta haifeshi ba amma ta san halinshi sarai,sun shaku sosai da Abdallah kallon shi kawai idan tayi zata iya gane akwai wani abu a ranshi

"Son what are you hiding" ta fada tare da daukan wayar ta dake kan side table dake cikin parlor sannan ta nufi main family parlor na gaba daya gidan shi kuma yana binta a baya yace" am not hiding anything trust me"
"Hahaha we shall see toh idan tayi tsami maji" tare suka shiga parlor kai tsaye dinning room suka nufa anyi setting komai su kadai ake jira,da yake duk yaran gidan suna skull so gidan gaba daya yayi shuru daga daddy sai uncle Tukur sai,su umma ne kawai a gidan da kuma shi,da yake uncle yakub ya tafi Mexico gurin wani aiki so baya gari..bayan sun gama gaisawa ne umma ta dubi momy tace

"Ke da dan naki ne haka" murmushi tayi tace "bari kawai kin san idan yara basa nan son shagwaba yake muna" tabe baki mamu tayi tace "kunfi kusa ai sai kiyata biye mai yana maidake warinshi" dariya uncle Tukur yayi yace "mamu are u jealous of my son" murmushi kawai tayi daga nan daddy yace "enough of the talks muce abincin mana inada meeting" daga na akay serving kowa ya fara cin abinci..

Bayan an gama ne daddy da uncle Tukur suka tashi zasu fita, gaba daya suka biyo su domin yi musa rakiya,daga nan su umma suka dawo parlor suna hira da hirar ta ishe shi ya dube su yace "nima na fita mamu sai na dawo" duban shi mamu tayi tace "dan Allah ka tsaya na shirya mijin nan nawa ka kai shi gidansu maman shi tace zata fita kuma dashi take so ta tafi"komawa yayi ya zauna tare da cewa "toh ina jira dama tunda nazo bamu hadu da itah ba"tashi tayi ta shiga cikin daya daga cikin dakunan dake cikin palour dan yiwa daya daga cikin masu aiki magana domin suzo gyara gurin da akaci abinci, daga nan ta wuce side dinta domin shirya daddy..

Ba'a jima ba ta fito dashi an shirya shi yayi kyau sosai, tasowa yayi ya Karbe shi tare da yiwa mamu sai ya dawo direct parking space ya nufa,daya daga cikin motocin ya dauka range rover black tasha wanki sai kyalli takeyi, horn yayi maigadi ya bude mai ya fita yana daga mai hannu..

Gidan hasinah ya wuce,yayi horn maigadi ya lako daya ga Abdallah ne sai ya koma ciki ya bude mai gate ya shiga bayan ya rufe sai yazo gurin motar yana jiran ya sauka ko kuma ya sauke glass sabida yana so ya gayamai cewa matar gidan bata nan,shi kuwa dayaga kamar yana so ya mai magana sai ya fito ya mika mai hannu suka gaisa

sai maigadin yace "matar gidan fah bata nan", bata nan kuma?toh ina ta tafi" ya fada cike da mamaki sabida idan bai manta ba mamu ce mai tayi tare da Abubakar(daddy)zasu fita,maigadin ne ya katse mai tunani daya ce "ai tare da maigida suka fita", "OK" kawai yace tare da juyawa ya koma mota.

wining glass ya mikawa mai gadi kudi shi kuwa yayita godiya,baya yawan zuwa gidan amma duk randa yazo toh kakarshi ta yanke saka'a domin yasan zai bashi kudin,shiyasa duk yazo yakeji kamar kasa ta bude ya shige don dadi

Gate din aka sake bude mai yafita,da fitar shi ya samu guri akan hanya yayi parking,sannan ya fido wayarshi yayi dialing numbern hasinah,bugu biyu yayi ta dauka tace "yaya ina wuni ", "lafiya qalau nazo gidanki bakya nan, "Allah sarki yaya wlh ina gidan su Manir ne,hajiyarsu ce zamu tafi umara tare shine muke shirye shirye, " ok toh ki mun kwatancen gidan sai nazo sabida tare da small daddy nake"kwatance ta mai shi kuma ya dauki hanyar unguwar,nambobin gida ya dinga dubawa har ya iso wanda tamai kwatance,bakin gate yayi parking,sannan ya juya wancen side ya dauki daddy suka fito.

Gate din ya nufa yayi knocking aka bude,sallama yayiwa mai gadi tare da mai bayanin gun wadda yazo gani,shi kuma maigadin ya shiga gurin kiranta tare suka fito,"yaya shigo mana ka tsaya a wage"ta fada tana karbar Abubukar(little daddy) daga hannunshi,murmushi kawai yayi tashiga gaba yana binta a baya har cikin wani parlor mai kyau dashi,ya samu daya daga cikin kujerun ya zauna yayin da ta shiga ciki ta kawo mai abun tabawa ta kuma gayawa mutanen gidan yayata zai shigo su gaisa.

Tana rike da tray ta shigo parlor da Manir a bayanta,a side table din da yake kusa dashi ta ajiye,yayin da ya tashi sukayi musabaha tareda mai jagora don su gaisa da hajiya bayan sun gaisa ne suka dawo parlor hira ta kaure tsakaninshi da Manir gashi dama Abdallah ba baya ba idan ya samu wanda tasu tazo daya.

Thanks
Vote
Share
Comment
And
Follow

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now