32

342 51 14
                                    


Not edited
Vote

oh ni hamida na shiga ukuna wannan wace irin musibahce aka kawo mun gidana toh wallahi bazan yarda ba" cike da hargowa taxo ta fincike jiddah daga jikin shi ta nunata da yatsa tace "ke karamar yar bariki ki kiyayeni wlh ba zaki lalatamun yataba inaji ina gani dan ubanki bakiga yarinya a gurin bane ko gidanku ba'a muku tarbiy...." bata gama rufe bakinta ba taji saukar mari tasssssssss

"Kar in sake jin kin zagi iyayenta koh da wasa bacemun da gani" har zatayi magana yace "shhhhh bana son hayaniya ki tafi kawai"a fusace taja hannun illham suka bar sitting room din,ita kuwa jiddah tunda ta maida ta gefe tayi tsaye kamar gunkin tana kallon ikon Allah guri ta samu ta zauna ta dafe kanta hamidah naso ta kureta amma da yardar Allah ba zata taba samun abunda takeso ba,cike da kwarin guwa ta sake tashi ta rike shi suka nufi part dinta

Har ta tayashi cire kayan shi don ya shiga wanka bata kalli idon shiba,shi kuwa so yake ta kalleshi ya bata hakuri dadai yaga tana kokarin turashi toilet da gaske ba tare da tace mai komai ba sai ya shiga kokarin cire mata kayanta itama don shiga wankan tare,hadiye abun ya tsaya mata a makoshi tayi daker tace "yaya bana so jekayi kafito lokaci yana wucewa"yace

"Tare nake so muyi" nisawa tayi tace "ni na riga da nayi nawa kamun kazo"

"Toh baxanyi wankan ba since ba zaki kalleni ba" shima ya fada cikin tsigar da tayi magana yana kwaikwayonta,data ga dagaske yake sai ta zauna a kujerar da take kusa da ita tana sauke numfashi,hannuwanta ya rike yace "look at me" batare da tayi masa musu ba ta kallle shi yace "nasan kina hakuri amma ki dada akan wanda kike dashi kinji wata rana sai labari,the only thing da nake so shine ki cigaba da bata girmanta kamar yanda kikeyi a kullum ok?

Ta mai shaking kanta tana murmushi yake shi kuma ya harareta,tana ganin hakan ta gane abun da yake nufi sai tace "insha Allah i will do as you say nagode,so aje ayi wanka koh"ta fada tana tashi tsaye tare da sauri turashi toilet taja mai kofar "it's not fair" taji muryar shi daga ciki murmushi kawi tayi ta tanufi kitchen dan yin dan abunda ba'a rasa ba kafin ya fito wanka

************
"Ba fa wasa nake maki ba wlh marina yayi a gaban yarinyar nan wai ni,har ni namiji zai mara akan kishiya bazata sabu ba wankan kuturu da sabulu ina" ta fada tana kara ciki jikinta sai mazari yakeyi

"Ke da Allah yimin shuru meyasa baki yiwa wanda ya mareki wannan hargowar ba sai ni kin wani zo kin cika mun kunne,ki natsu mana nuyi magana shiyasa a kullum kike kwafsawa, gaba daya kinbi kin haukace sabida yarinyar da bata kai ta kawo ba"latifah ta fada cike da bakin cikin halin abokiyar tata,ajiyar zuciya kawai tayi ta kafawa latifah ido

"Wannan magana da kike gani ba karama bace idan ba rainaki zatayi ba Allah tsina,tun da wuri ke nemawa kanki solution idan ba haka to kuwa ki shirya mutuwa kwana kusa,kin dai ga ya fara dukanki akanta to ina ga ta samu ciki ai sai ki zama yar aikinta na yita gaya maki kizo muje na kaiki gurin wani gwaska aikin shi kamar yankan wukane kinki waike gaki ta kwari toh ai sai kiyita zama anayi bake it's non of my business"latifah ta fada hankali kwance tace

"Nidai gaskiya duk bata kai ga zuwa gurin wani gwaska or what ever you call it ba,kawai abunda nakeso ki bani wanda koh makiyinta zaiji tausanta.

"Ai ni banga kina shirin mata wani abu bane shiyasa na zura maki ido"

"Taya ma zakice haka bayan kulli yaumin maganar da nake maki kenan,na rantse na gaji gaba daya ya cenza mun kamar ba mijina ba"latifah tace "toh ai ke dince dama gadai ki nan ga iya kwaliya,ga iya saka kaya idan aka hangoki daga nasa sai kiyita daukar ido amma da anzo kusa dake sai zance yasha banban"hamidah tace

"Me kike nufi"

"Kinfi kowa sanin abunda nake nufi bude idonki da kyaue kigani latifah ce a zaune ni bana boye-boye gara na gaya maki,kin san Allah duk abun da yake faruwa a gidan nan da kuma wanda zai zo ya faru nan gaba toh kece silar sa"

"Ki fiddani a duhu mana na kasa ganewa"hamida ta fada a tsarge "ina nufin kinyi contributing sosai akan kishiyar da aka maki,taya xa'ayi ace mace har mace bata son saka turare I don't care yanda zaki dauki maganar but it high time da zaki yiwa kanki karatun ta natsu koda na kaiki gurin wani aka baki wani abun dan kiyi amfani dashi to alquran naci amanar mujahid sabida bazance kina wariba but at last ya kamata ki dan dinga saka koda sprey ne but no kinki"

"Mstwww"taja tsaki wai duk wannan ne kike jan zancen da tsawo haka,dan Allah ki manta dashi muyi abunda zai fidda mu" hamidah ta fada ba tare da ta dauki maganar ta latifah da muhimmanci ba

"Ki dai fitar da kanki dan ni ba abunda ya shafe ni, wlh dadi ma naji da Allah yasa aka miki kishiya"hamidah tace "dadi fah kika ce?

"Yo dadi mana da kin samu wata shegiyar karuwa da bata da imani ta saka maki miji a lungu tana mai abinda ba kyayi da sai kin yabawa aya zakinta aradu"latifah ta fada tana shekewa da dariyar mugunta harararta kawai hamidah tayi saboda bakin ciki "me kika maidani ne wai zamuyi maganar dake gaban mu koya?

"Mezai hana uwargidan mujahid maman illham"ta fada tana mata shakiyanci,daga nan suka  cigaba da tataunawa

*******
"Yaya nextweek zamu fara exams"jiddah ta fada cike da rigima bai kulata ba har ta saka ran samun amsa ya cigaba da harkar gaban shi,da taga dagasken yakeyi bazai amsaba sai ta tashi ta nufi bedroom dinta "ina zaki" ya tambaya a ranta tace hohoho akace gaba da gabanta aljani ya taka wuta a zahiri kuwa tace "kwana nakeji kuma inaso naje nayi karatu for my exams"

"Exams my foot come on zonan maimakon kiyi tunanin yanda zaki farantawa mijinki rai maganar exams kikeyi,ai na san abinda kike yiwa Autar Ammi kike son gani bawani abu ba"fuskarta ta kawar gefe tareda gyara tsayuwar

"Ba dake neke magana ba?ta tunzuro bakinta kamar zatayi kuka tace "lokacin bacci yayi fah yace "ai na fiki sanin haka zo nace" kamar bata so ta karaso kusa dashi "kin daina tsorona koh?ya tambayeta  tare da janyota ta zauna kusa dashi "hmmmm zanyi maganinki ne,so let's be serious maganar exams dinki auta ta kirani tace yaushe zakizo nace mata cikin satin nan and am sorry ban gaya maki ba  she was sick harda kwantar da ita akayi"

Nan take hankalinta ya tashi harda hawaye yace "o my god dalilin daya saka naki gaya maki kenan,kuka ba dan nasan shi zakiyi idan ba haka ba ce maki fah nayi she was sick ba she's sick ba"ya fada dafe dakai murmushi tayi dan dariya ya bata yace "wlh ki daina mun halin nan naki abu kadan kuka ga shegen tsoro"

"Toh ai kaine"ta fada a shagwabe "nine nayi me?ya tambaya yana tsare ta da ido tare da taba ta da taga yana kokarin ya wuce gona da iri sai ta rike mai hannu tace "nidai yayah yaushe zan tafi"

Idanun shi ya lumshe ya sake budewa yace "ba nace next week ba me kuma kike tambaya"

"Toh next week which day? A zafafe yace "kinsan Allah Dadah (sunan da yake kiranta tana yarinya idan baku manta ba)ki rabani da tambaye tambayen nan koh ranki ya bace,i said next week koma wace ranace ai gani zakiyi"idanuwanta suka ciko alamun kuka zatayi yace "kuma idan naga hawayen mutum saina zane shi"

************
Tsaye tayi a bakin kofa ta kasa shiga bedroom din ta kuma kasa barin gurin,duk da yasan cewa tana tsaye a bakin kofa sai ya kyaleta sabida baya so ya takura ta,dan ya lura yana da aiki babbar a gaban shi dole ya saka mata soyayyar shi a ranta idan da bai damu ba yanzu ya damu matuka Allah shaida ne cikin fuhutu ya saka shi jin shima yana so ya samu wanda zai kira nashi,sannan ya lura har yanzu akwai son yayanta a ranta fatan shi kawai Allah ya bashi sa'ar yin abinda ya kudurta,da taga tsayin bashi da wani amfani sai kawai tayi sallama ta shiga ya kuwa amsa mata

"Zo zauna mana kin tsaye a bakin kofa kamar ba gurin mijinki kizo ba"ya fada a natse satar kallonshi tayi cike da mamakin kalaman shi,shi kuwa ya dauke kanshi kamar ba shi yayi maganar ba sai yanzu ta lura kusa duk halinsu daya da Abdallah.



Rokona a kullum shine ayi voting da kuma comment matukar zakuyi to ina tabbatar maku da bakuda matsala dan updates zanta maku wlh dan koni kaina a matse nake na gama littafin nan na fara maku wani,duk da haka kuma ina godiya da votes dinda kukeyi amma fah nafi so ya linka nada

Vote
Comment
Follow
And
Share
Taku har kullum

Mrs umar faruku❤️

Wassallam

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now