27

374 45 0
                                    

VOTE AND FOLLOW

Har akayi wankin amaren aka gama bata kara ce masu komai ba suma kuma basuce mata ba hirar tsakaninsu da salmah ne kawai sai yan matan amaren dake gurin ciki kuwa harda eesha kawar zulfa'u bakin ciki kamar zai kasheta,taso tayiwa fuhutu wani abun amma sai taga ba abun sauri tunda kamar a gida daya zasu zauna tasha alwashin sai ta rama abunda fuhutu tai mata dan ita idan fuskarta ta mara toh ita rayuwarta zata mara,har dai data rabata da namijin da tafi so a duniya,nikuwa nace an haddu da andace dan itama fuhutun ba bayaba.

Bayan sun dawo gida sukayi sallar isha fuhutu ta gama waya da Ammi kenan jiddah ta shigo tace "kin san Allah sistern Abdallah gani nake kamar akwai inda nasanta"fuhutu tace wacce a ciki salmah koh mararar mutuncin?jiddah tace "ashe kema kin lura bata da mutunci yanda ma ta dinga mana kallon raini abun sai wanda ya gani"tsaki fuhutu tayi tace

"Ai kuwa kanta zata raina ba kowa ba dan ba'a daga mun yatsa ban karyashi ba"fuhutu ta fada tana yamutse fuskanta dariya Jiddah ta sheke da ita tace " kidai yi ahankali da yanda nake ganinta wata rana zata iya tsareki a gida ta maki dan karan duka"

"Amma dai kinci amanata bestie....wai harni zan tsaya wata yarinya ta mun duka ban fasa mata kaiba ,ai karya ne sai dai mu daki juna wlh"ta fada tana nuna kanta

"Nidai na gaya maki be carful"tsaki fuhutu tayi tare da juya mata baya

**********
Kwanaki suna ta tafiya yau saura sati daya bukin su jiddah wanda yayi daidai da sati biyu da tarewar su zulfa'u ba tana iya kokarin ta na ganinta kyautata mai amma har yanzu akwai burbushin son Abdallah a ranta wanda bata tunanin zai barta nan kusa,amare kuwa sai gyara ake sha gurin Hajiya bangarorin uku gaba daya shiri sukeyi gani nake ba wanda yakai ango mujahid zumudi kodan yanda Hamidah ta takura mai kwanakin nan,gafen Abdallah kuwa abun ma haka

"Ango,Ango,ango kasha kamshi"Abdallah ya fada cike da zolaya "toh ai ni na tsufah yanzu tunda har nayi sati biyu da angoancewa"khalifah ya fada yana murmushi

"Really so abun ma gar alfahari akeyi dashi kenan,ni gani ma nayi duk ka cenza ka zama wani kato dakai lallai zulfa ta dauki training dinda su Mami suka mata kenan"

"Yanzu dai kanka akeji koh dama ba ramame bane ni balle kamun gorin jiki,ai kaima zakaji yadda akeji you only got one week for you to get rid of bachelorhood so get ready"khalifah ya fada yana tashi tsaye "ni zan tafi gida salim yace momy tana son ta ganni so sai munyi waya koh"shima tashi tsaye yayi yace

"Aa wlh tare zamuje rabona da ita tun bukin ka gara naje na gaida ta kar tayi fushi dani so let's go together"

"Ok"
Daga nan suka fitoh tare kowa ya shiga motarsa suka nufi gida.

**********
"Wata sabon gani yanzu nake cewa Maman little tunda ka samu Jiddah ka manta dani"manir ya fada yana dariya mujahid yace

"Ina kuwa zan manta da uban amaryata ni na isa ,i wont try that ai wlh Kayi hakuri abubuwa ne suka mun yawa"yace

"Karka damu i understand"

"Ok so ya little da maman shi da kuma aiki"mujahid ya tambaya

"Lafiya qalau Alhmdllh"

"Naga kwana biyu bamu gaisa ba shine nace bari nakira mu gaisa,don't you think we are supposed to hangout a little bit before the nikkah ?"mujahid ya fadah Manir yace

"Of cause why not kawai kasa rana da time da za'ayi"

"toh bakomai zamuyi waya dai anyhow my regards to my boy nagode sosai"

"Bakomai zaiji" Manir ya fada daga nan sukayi sallama tare da kashe waya

Bayan ya gama wayan Ammi ta shigo parlorn ta samu daya daga cikin kujerun ta zauna tare da duban shi a natse tana nazarin shi ta lura gaba daya jinshi yake kamar yanzu aka haifesa sabida auren nan da zaiyi kuma har yanzu bataji yace matar shi zata zoba.

Gyaran murya tayi tace "yayansu baka mun magana game da hamidah ba fah koh ba zata zoh bane?ta tambaya a natse tana kallon shi,baya so ya batawa matar shi suna koh dan halin da tayi kamun ta yarda da auren shi so sai yayi saurin cewa

"Aa wlh tayi niyan zuwa da yake ita ke watching duk abubuwan dake faruwa a company,kuma kinga ba zai yuwu a bar wanda ba na jini a cen ba it's not possible so shiyasa nace ta zauna kawai,ya fada yana kallon kasa,tabe baki tayi kamin tace

"Toh shikenan Allah ya tsare"yace

"Amin"

Daga nan suka cigaba da hirarsu ta uwa da da'a Yazid ne yayi sallama ya shigo yace "aa tataunawa akeyi ne mother and son?ya tambaya cike da zolaya Ammi tayi kamar bataji ba mujahid yace " you came in ba gaisuwa ba komai kazo kana saka mana baki" marairece fuska yayi yace "but ai nayi sallama so what is the need of greeting kuma" Ammi tace

"Yazid"yece

"Yes Ammi"

Tace"the last time I checked yanzu ka shigo gidan nan so please go inside and freshen up sai kazo kaci abinci ina so nayi magana da yayanku ne"tashi tsaye yayi tare da daukan jakar shi yace "who am i da bazanyi obeying order dinki ba kar naji naushi yanzun nan"ya fada yana kallon mujahid Ammi tace

"Just go" dismissively ba tare da ya kara cewa komai ba ya haura sama yana murmushi Ammi tace "ina ta kiran wayan Zainba numbernta baya zuwa I think they are on the plan"

"I think so dan munyi waya da mijinta da safe yace mun yau zasu taso yau" ya fada yana tashi tsaye "zan fita Ammi sai na dawo"tace

"Toh a dawo lafiya Allah ya kiyaye"

"Amin"ya fada tare da fita daga parlorn



Gaba daya kwanakin nan nawa nakeji sosai wlh siyasa bana posting ayi maneji da wannan
Not edited
PLEASE COMMENT AND VOTE

#Marmiee _Suleiman#

MRS UMAR

Fuhutulkhairi Where stories live. Discover now