AUREN SIRRI EPISODE 83

274 21 16
                                    

AUREN SIRRI
    


AYSHA A BAGUDO




Page 83


Ganin yadda Ya fige motar da gudun maseefa  Yasa kukanta ya K'aru , hankalinta yayi matukar  tashi tsoro tattare da fargaba ne sukayi nasarar   lullube duk wani  ilahirin jikinta, abubuwan da yake mata sun fara isarta Amman ta rasa yadda za'tayi dashi.

takaicin haka Yasa ta kife kanta bisa cinyoyinta tana sake risgar kuka mai cin rai da  suma zuciyar ma'abocin sauraro .

Daidai jankode first get taji  ya Dan sausauta gudun motar tare da daukar hanyar Aja
  tafiya kad'an  sukayi  ya soma al'amun tsayawa  ya gangara gefen titi yayi parking, tare da  zuba mata rikitattun idanunshi kawai yana kallonta  da sauraran yadda take risgar kuka da iyakacin karfinta.

jin kukan nata yake har cikin zuciyarsa yayinda gefe daya kuma ya dinga ji  tamkar ana diga masa ruwan dalma ne a kirjinshi , yana jin yadda sound din kukan nata ke fita da karfi har da shesheka .

runtse rikitattun idanunshi yayi tare da dafe daidai saitin zuciyarsa da tafin hannushi sakamakon yadda yake jin  zuciyarsa na bugawa da karfe ...

bai jin zai iya yi mata magana a yadda yake jin kansa Dan hk ya barta tayi kuka mai isarta sannan ahankali  yaji  ta soma yin  shiru  tana jan numfashi da kyar da sauke ajiyar zuciya.


Jin ta daina kukan Yasa shi bude rikitattun idanunshi, ya   Ciro hanky agaban aljihun rigarsa ya goge fuskashi wanda ya jike da gumi sharkaf tsabar tashin hankali daya tsinci kanshi ciki .


Ahankali ta dago kanta ta maida gefen titi tana kallon motocin dake giftawa time to time ...

gyara  zamansa yayi da kyau yana fuskantarta ahankali ya Dan matso   kusa daita tamkar zai shige  jikinta  Yasa hannunsa duka ya mtaso daita yana mai  juyo da fuskarta yana kallon kwaryar idanunta batare da yace mata komai ba . kawai taji  ya hau  goge mata Hawayen dake   fuskarta, yana cigaba da  kallonta had'e da yin  nazarinta..


Sannan ya hade tafin hannushi cikin nata yana kokarin fixgota jikinshi taki yarda ta makale jikinta da kujerar ta soma kokarin cire hannuta cikin nashi ,Yayi saurin sake damke hannunta cikin nashi sosai ta yadda ba zata iya kwacewa ba.

wani irin zafi yaji jikin nata ya sake d'auka fiyye da sanda suka baro gida  ,kuma yana jin yadda da zafin  ke fita yana  shiga jikinsa tare da ratsa kowane shashi Na jikinshi  , ya kai hannushi gefen wuyanta "nan ma zafi yaji  tamkar garwashin wuta hankalinsa yayi maseefar  sake tashi sosai , wani  irin abu ya dinga ji   mai kama da so.. yana masa yawo a sansar  ajikinsa tare  da kokarin kawowa zuciyarsa farmaki take duk wani kuzari dake jikinshi ya nema ya rasa ..

Tambaya ya jihowa zuciyarsa da ruhinsa kar dai ya kamu da soyayyar yarinyar ne, batare da ya shiryawa  hakan ba ?
"Kai hakan ma ba zai ta'ba yuwa ba , take kuma wani part Na zuciyarsa ya shiga  karyata hakan .

yasan ya taba son auren zeenat .. kuma koda ummi ta hanashi aurenta alokaci, bai tsinci kanshi 'cikin wannan tashin hankali da yake ciki ba ..

Wani irin sanyi yake ji ajikinshi tamkar ana masa wanka da ruwan sanyi akan yarinyar, duk wani bugawar da zuciyarsa zatayi ,tana yi ne akan yarinyar , mamaki ne fal ya cika zuciyarsa "to me hakan yake nufi dashi  ?
Ya tmbyi kanshi .
"Wayyo Allah"
ahankali ya shiga furta hasbunallahu wani'imal wakil yana yi yana sake  nanatawa

da kyar ya samu ya dinga fizgo  numfashi yana fitarwa ,ahankali   da sauri ya saki hannuta dake sarkafe da nashi  yayi  reverse ya dauki  hanya zuwa 'cikin gari ..


Tafiya sukeyi tamkar wasu kurame babu mai cewa Dan ,uwansa qala kwanensu da abinda ke damun shi ,sosai  ya lula  duniyar tunanin yadda yake jin yarinyar akasan zuciyarsa gabadaya Gani Yayi tana neman mamayeshi da komai nashi ,yayinda ita kuma haushin kasancewarta tare dashi guri daya  Yasa ta rasa walwalarta da sukuni...

Dan ko kallo bai isheta ba ,dan tunda ya tada motar ta kuma maida fuskarta gefen titi .

shi kuma ya cika fammm tamkar zai hadiyi zuciya  ganin halin ko inkula data nuna masa.
Cikin sanyi jiki  ya sake  Ciro hanky ya goge fuskashi Dan wani irin gumi ne ke karyo masa duk da AC dake motar aiki ,sannan  ya maida hankalinsa Ga tukin da yake ..


A bakin wani big super market yayi parking ya fito ya kulleta acikin motar ya shiga ciki .

tun Daga shigowarsa work's din gurin suke gaida shi 'cike da girmamawa , wasu ya amsa, wasu kuma ya D'aga masu hannu kawai .

hatta manage gurin biye yake dashi abaya suna tattaunawa ahankali ta yadda babu mai jinsu ..

Kaya  ya zaba wayanda zasuyi  amfani dashi  ya fito, manage gurin na rike da ledodi guda biyu daya mai girma daya Yar karama ,deeni   ya bude motar ya shiga ya  zauna tare da  karbar  ledar dake rike a hannun manage ya ajiye a sit din baya ,ya Dan kalleta kadan yaga fuskarta a hade tamkar hadari har lokacin taki sakin fuskarta haka kawai ya tsinci kanshi da jin faduwar gaba .

gabansa ya shiga dukan dakan uku uku.
  ....karamar ledar ya sake amsa ya cilla mata bisa cinyarta batare da yayi mata mgn ba.

Ta zabura ta Mike zaune tana gyara zamanta Daga Dan kishingidan datayi tana kallonsa  , bai bi takanta ba  ya d'auke kanshi gareta shima ya tamke fuskarshi sosai fiyye danata  , ya tadda motar  ya hau  kwalta bai damu  da yadda manage din ke Daga masa hannu ba yana masa fatar a sauka lfy  ..karatun alqur'ani mai girma ya kunna  Kira'ar SUDAIS cikin suratul  ra'ad .

Da wani irin kallo take binsa dashi 'cike da tarin maseefa  Amman sai ta samu kanta da shan jinin jikinta sakamakon hango yadda Ya hade rai babu halin aikata abinda tayi Niyya ,Ga kuma karatun alqur'ani mai girma daya soma  ratsa sansar jikinta  ta koma ahankali ta lafe lamo..  a kujera
ta Dan Daga kanta sama idanunta a lumshe tamkar mai jin bacci ..tana jin yadda sautin  karatun ke tashi itama tana bi cike da natsuwa .

Ya Dan juyo ya saci kallon Dan karamin bakinta dake motsawa sannu sannu .

Can taji ya rage sautin karatun  ya soma waya cikin harshen turanci wanda yake yinsa 'cike da kwarewa tamkar yaren  uwarsa da ubansa  ..

Cikin sanyi muryarsa taji yana cewa " kina office ne  ?
Ita dai batasan  abinda Na cikin wayar yace ba" ok ganinan  zuwa yanzu  wata yarinya zan kawo ki duba min lfyrta ,sannan ya ajiye wayarsa ya cigaba da tuki .


A harabar wani katanfarin special hospital yayi parking ya kashe motar ya juyo da dubansa gareta ,tare da tsura mata Rikitattun idanunshi ,jikinta   yake kallo musamman tsaitin inda ta buge kana ya maida idanunshi kan kyakywar fatar  fuskarta,
idanunta sun Dan  kumbura sbd kukan datayi .
fuskarta tata tayi fayot daita ,Amman duk da haka bai hana sihirtaccen kyauwunta fitowa ba ,kuma tayi masa kyau sosai .

lumshe idanunshi yayi ya Dan kamo lips dinsa na kasa   yana ciccizawa ahankali ahankali  sai kuma ya saki Murmushin tare da tura yatsun hannushi cikin sumar kanshi yana shafawa  a zuciyarsa ya furta mutun mai kyau ako wani hali ya kasance mai kyau ne domin kyawunsa bai boyuwa ..


Ta tsargu da kallon da yake mata sbd idanunshi dake yawo ajikinta Ahankali ta bude shanyayun idanunta da suke a runtse tana dubansa dasu  jin  yayi parking kuma  idanunshi na cigaba da  yawo ajikinta ..

wata uwar harara ya watsa mata tun kafin tayi challenging dinsa  tare da d'aure fuska tamkar bashi ta kama yana kallonta ba.
itama sake  hade ranta tayi tamau tare da turo  karamin bakinta ta ja mugun tsaki .... Ahankali kuma ta furta "aikin banza kawai malam...

Ba zato balle tsammani taji saukar  rankwashi a tsakiyar kanta
dafe gurin  tayi tana kallonsa da shanyayun idanunta.

Idanunta suka soma kawo  ruwa Ya murde mata kunne da karfi ,
ta saki kara mara sauti sannan ya buge mata bakin tsiwa  ,ta kama bakinta da hannuwata duka tana mai zuba masa shanyayun idanunta wanda suke zubda hawaye .


A hassale yace" ki duba cikin wannan .. yana  nuna mata ledar dake saman cinyarta  akwai hijab ki ciro ki suturta jikinki  dashi ,sannan ki fito Dan bazan iya fita dake  da wannan shigar   Yan isaka ba ,
Kisa   mutane su  dauka nima haka nake ..

Ba musu ta hau bude ledar tun Bai kara mata wata izayar ba wasu  dogayen hijabai tagani  colours biyu , dinki zamani masu shegen kyau da daukar hankali, duk da ranta a dakugule yake  Amman hakan bai hanata jin dadi ba,dan sai daukar idanun suke da gani ma ba dinkin Nigeria ba ,Dan yafi mata kama dana kasashen larabawa.. ta zira ajikinta ta fito tana gyra zamansa da kyau ..


Yana gaba tana binshi a baya duk inda suka gilma  sai kallonsu mutane ke yi ,yayinda ake ta gaidashi 'cike da girmamawa wanda har itama bata tsira Daga samun nata gaisuwar ba ,Kai tsaye office din. Doctor saira Jack ya nufa daita ....






MMN SUDAIS CE

AUREN SIRRI Where stories live. Discover now