AUREN SIRRI EPISODE 84

238 12 0
                                    

AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO





Page 84

Da sallama a bakinsa  ya shiga office din Dr saira , yayinda nablah ke biye dashi abaya tamkar wata sabuwar halitta  sannan ta maida kofar office din ta rufe ta karasa shigowa ciki sosai .

zaune suka iske doctor saira sanye cikin kayan aikinta na cikakkiyar doctor idanunta manne da farin medical glass ..tana ganinsa ta fad'ad'a fuskarta da murmushi Tare da Dan   Mikewa  tsaye kad'an  tana gaishe shi tana mai  nuna masa gurin zama da hannuta.

ya zauna yana mai amsa gaisuwarta fuskarshi ba yabo ba fallasa ,sannan ta yiwa nablah dake rakube a gefe tsaye nuni da kujerar zama  .

Nablah ta zauna   tana d'ari  d'ari  cike da  natsuwa tana karewa office din kallo saboda yau shine karo Na farko data taba shigowa irin wannan hospital din na masu hannu da shuni ,kai har ma  da  office din gabadaya, Hk   kawai ta tsinci kanta da jin wata irin mummunar fad'uwar  gaba.

batare da wani bata lokaci ba deeni ya shiga yiwa doctor saira   bayanin abinda yake tafe dashi ,akan so yake ta duba masa   lafiyar yarinyar da yazo daita .

Doctor tayi murmushi  tana kallon shashin da nablah ke zaune kanta a sunkuye  tana wasa da yatsun hannuta,a natse  ta soma tmbyrta abinda ke damunta 'cikin harshen turanci.

nablah tayi tsuru tsuru da idanu ta kasa cewa komai sai da doctor saira ta sake maimaita tmbyrta sannan muryarta a sanyaye tace "babu abinda ke damuna fa , Kuma ni lafiya lau nake babu inda kemin ciwo  .

Deeni ya juyo ahankali yana kallon Dan  karamin bakinta da take tsukeshi a duk sanda zatayi  mgn .

A Dan fusace Yace" ke banson iskanci ki sanar mata da abinda yake saki zafin jiki ba wai ki tsaya kina wani  batawa mutane lokaci ba ..

A dake itama tace "to babu abinda yake damuna sai kuma  nayi karyar ciwo .

Yaja tsaki yana cizan gefen lip's dinshi    kana ya cigaba da magana
" doctor karki sake tambayarta  ke dai ki duba min lfyrta kawai .

Doctor saira tayi murmushi duk da batasan matsayin yarinyar gareshi ba ,Amman sai taga sunyi matukar dacewa da junansu .
tace "Ok sir sai dai  mr DEENI baza'a yi haka ba ,ciwon nan  ajikinta yake yakama mu D'an ji wani abu Daga bakinta first  so that a San ta inda za'a soma duba lamarin .

DEENI yayi shiru tare da d'auke kanshi bai sake tsuma musu baki  ba sai ma  phone dinsa daya Ciro  ya soma operating,
ita km doctor saira ta sake maida hankalinta sosai a kan nablah .

"yauwa  kanwata Ina jinki  yi kokari ki sanar min da abinda ke damunki da kyar dai doctor saira ta samu nablah tace mata  wani abu .
"A gaskiya Ni bana jin ciwon komai ajikina ,sai dai sometimes   nakan ji  motsin wani abu acikina.......
cikin wani irin yanayi na shock DEENI ya d'ago rikitattun idanunshi ya zuba mata yana kallonta ,ta Dan tsuke bakinta ganin yadda yake kallonta sannan  ta shareshi  tamkar batasan ita yake kallo ba, ta cigaba da magana da muryarta a shagwabe.
"Amman Ni doctor Allah  Ina ganin kamar appendix  ke damuna.

ba doctor saira ba hatta deeni sai da maganarta ta kusan sashi dariya ,
Aiko yayi saurin juyar da kanshi gefe yana fitar da sanyayyir murmushi ,
haka kawai  ya tsinci kanshi 'cikin wani irin farincikin Na daban kuma mara misaltuwa .

Doctor saira ma dariya tayi sosai sannan tace" ba kece zaki yanke hukunci abinda ke damunki ba, computer ce zata sanar mana
" mu dai inda ke miki ciwo kawai zaki sanar mana .
A Dan hassale tace" to babu inda ke min ciwo baya Ga motsin danake ji acikina .

AUREN SIRRI Where stories live. Discover now