AUREN SIRRI
AYSHA A BAGUDO
75
A zafafe Ya qakaraso har zuwa inda take a durkushe sbd yanayin takaicin da yake ciki
'dan bakaramin yamutsa masa tunaninsa tayi ba musamman lokacin daya daura idanushi akanta tsaye da kB,
ji yayi kansa nayi masa wani irin Sara tamka zai rabe gida biyu ,
zuciyarsa kuwa zafi take masa tamkar zata kama da wuta.
Kuka take Sosai Na fitar hankali mai taba zuciyar , kallo daya zakayi mata kaji tausayinta ya tsarga maka kuma duk rashin imaninka idan kaga halin da take ciki wlh Dole ka tausayawa rayuwarta .
A halin yanzu bata tunanin duk duniya akwai mutumin data tsana da kin gani ......sama da mutumin dake tsaye a gabanta ...
Kukanta da halin da take ciki ko ajikinsa ,asalima kwata kwata bai damu ba kuma bai ji ajikinsa Hakan zai zama damuwarsa ba sai ma tarin haushinta da takaicinta dake daskare a kasan rashin .
gyara tsayuwarsa yayi sosai tare da rungume hannuwanshi duka a saman fadadden kirjinsa ya zuba mata rikitattun idanushi yana kallon yadda take kuka , kusan minti Goma ya dauka tsaye yana aikin kallonta batare da yace mata komai ba.
jin kukanta yaki tsayawa yasa zuciyarsa cunkushewa guri daya tasoma dugunzuma tamkar ana diga masa ruwan dalma .
Kafin ya ankare yaji
Ta sake kara sound din kukanta mai tsanani cin rai da tsuma zuciyar ma'aboci sauraro tare da dagula lisafi .
Shr kawai yayi yana tunanin abinda yakamata Yayi gabadaya ilahirin jikinsa sun gama sagewa duk da sanyin AC dake aiki a parlour hakan Bai hana zufa keto masa ta koina ajikinshi ba so yake yayi magana Amman ya kasa dan bazai iya yi ba, dan ko yace zaiyi mgnr muryarsa ba zata fito ba dan hk Ya runtse rikitattun Idanunshi gam hade da Dan kamo lip's dinshi Na kasa yayita tsotsa ahankali yana jinta tana risgar kukanta da yake jinsa har 'cikin ranshi baya kaunar ya bude idanunshi ya kalleta cikin yanayin halin da take ciki , km bai jin zai iya furta mata daidai da kalma daya ce a yadda yake jin kansa
Dan hk ya barta ta cigaba da kukanta, wa tunaninsa idan ta gaji dan kanta zatayi shr amman Ina saima ji yayi ta kara sautin kukan sosai .
Ai take haushinta mai gyaraye da tsansar takaicin abinda tayi masa Ya sake harzuka zuciyarsa .
bazato taji saukar rankwashi a tsakiyar kanta ......
Da sauri tasa hannuta ta dafe gurin tare da sakin wata irin razananniyar kara Wanda ya farga da ummi dake zaune a part dinta .
idanunta suka sake kawo ruwan hawaye mai dumi .. ya murde mata kunne da karfin gaske ta sake saki wani kara... tare da cewa "wayyo Allah na .... Wayyo Allah na ...
"wlh Allah Ya isa ban yafe ma.....ai kafin takarasa taji Yasa bayan hannushi ya buge mata baki.
da sauri ta sanya hannyenta dukka akan bakin nata tana mai zuba mishi shanyayun idanunta Wanda suke cike taf da ruwan hawaye .
Sannu ahankali ya bude idanunshi fesss suka sauka akan Kwakyawar fuskarta mai cike da haiba yana mata wani irin kallo mai tattare da tsansar tashin hankali " shiiiiiiiiiii kawai ya iya cewa.
ba shiri ta hadiye sauran kukanta Dan wani irin tsoronsa ne taji Ya caki tsakiyar zuciyarta.
yayinda gabadaya ta canza ta koma wata kala abar tausayi Banda tsine masa da zaginsa bbu abinda take a kasan zuciyarta ...
daidai wannan lokaci ne
ummi da safeena suke saukowa daga upstairs sakamakon jin sautin kukan yaki karewa km har zuwa time din DEENI na nan tsaye rungume da hannuwanshi .
Da sauri ummi ta karaso Inda suke tana tmbyrsa " "Kai lfy ?
DEENI yayi shr kawai yaki cewa komai sai ma cigaba da kallon nablah da yake batare da ya amsa tmbyr da umminsa tayi masa ba .
Ahankali ummi ta dago nablah dake durkushe a kasa tana tmbyrta "lfy nablah meke faruwa ne? "Me yayi miki ? Hk ummi ta jera mata tambaya.
shiru kake jin nabla dan babu bakin mgn sai ma kukan da take risga da iyakacin karfinta har da shesheka .
Ummi ta sake juyo inda deeni ke tsaye Wanda xuwa lokacin ya sake gyara tsayuwarsa tare da cire hannushi a saman fadadden kirjinsa ya mai dasu 'cikin aljihun wandonsa yana cicciza lips dinsa .
"Deeni....ummi ta kira sunansa muryata a kausashe ,Kasa amsawa yayi tsabar Haushi sai ma idanunshi daya dauke daga kan nablah ya maidasu gareta .
"me ya samu yarinyar mutane take kuka irin haka?
"ko wani abu kayi mata ta jiho masa tmbyr a jere ..?
Kafin yace wani abu sai daya numfasa tukun sannan ya sauke ajiyar zuciya" tare da yatsina fuskashi" muryarsa a marairaice mai cike da tsansar shagwaba kana yace" Gata nan a gabanki first love ta fada miki abinda akama mata .
ummi ta bata rai sosai tana dubansa sannan tace "bafa na son rashin mutunci deeni ....
"Ka fita idona Na rufe ...abinda kayiwa yarinyar mutane kawai nake son sani ba wanin rainin hankalinka daka sabawa yiwa mutane ba .
Shima hade rai yayi Sosai fiyye da dazu sannan yace" haba first lov ya a gaban yarinyar zaki dinga yimin hk "salon kawai ta raina mutane byn nima hk na ganta bansan abinda ya sameta ba.
yana gama fadar haka ya cire hannushi daya cikin aljihun wandonsa ya bar daya ciki tare da juyawa ahankali ya soma daga kyawawan kafafunshi ya soma takawa sannu ahankali 'cikin takun nan nasa mai matukar daukar hankali , Ya nufi bedroom dinsa .
YOU ARE READING
AUREN SIRRI
FantasyMATARSA CE TAKE ZUBAR DA CIKI BISA WANI DALILI NATA WANDA SANADIYAR HAKA SURUKARTA TAYIWA MIJIN DATA FI QAUNA FIYYE DA KOMAI A DUNIYA AUREN SIRRI DA ME AIKINTA BATARE DA SANINRA BA..