AUREN SIRRI EPISODE 63

192 10 1
                                    

AUREN SIRRI

AYSHA A .BAGUDO

Page 63

Bayan ta idar da sallah ta Mike ahankali jikinta a tsanyaye ta karasa jikin window dakinta ,ta makale hade da dan zuge labule window kadan ,ta yadda zata ji dadin hango abinda ke wakana a compound din estate din. Tana nan tsaye tana kallon yadda motocin ke shige da fice a cikin estate din , ta zurawa waje Ido sosai kmr mai shirin hango wani abu na daban aciki estate din, yayinda take shakar wata iska ta musamman mai dadi da ratsa jiki, wanda rabonta da jin irin haka ta dade , tun kafin shigowarta cikin gidan. har wani lumshe shanyayun idanunta take sakamakon farinciki data tsinci kainta ciki. Ta dauki tsawon lokacin makalle agurin tana shan iska karar bude kofar dakin data ji anyi ne,Yasa ta dan juyo da sauri hade da sakin labulen window. ahankali nablah ta sauke idanunta fess, akan Zeenat dake tsaye ki kam.. tana mazurai . take gaban nablah Ya shiga faduwa da sauri , a yatsine Zeenat ke watsawa nablah wani irin mugun kallon wanda ke hautsina kayan cikinta , ganin irin kallon rashin arzikin da Zeenat ke binta dashi ne ,yasa nablah shan jinin jikinta. tabe baki Zeenat tayi sannan tace" Yar iskar baiwa... kawai abinda ya kawo kennan , kin wani zo kin nemi waje a daki kin zauna tamkar boka dan tsabar munafurci , to wa kike so yayi miki sauran aiki da yayi saura uhm ? Nablah tayi saurin girgiza kanta tare da cewa "dan Allah aunty kiyi hakuri wlh na dauka ko mungama aikin ne. Zeenat ta sake watsa mata wata uwar hararar hade da kallon banza.. wanda hakan ya sake frigita zuciyar nabla dake tsaye Amman ta dake batare da ta bari Zeenat din ta gane yanayin data ciki ba . Zeenat taja tsaki tare da cewa" dan Allah malama ni fito ki kije ki karasawa mutane aiki sannan km ki daura min abinci ,Yar isakar baiwa kawai ... nablah tayi shir tare da dago shanyayun idanunta tana kallon Zeenat dasu ,yayinda take jin zuciyarta tamkar zata kama da wuta tsabar takaicin sunan da Zeenat din ta ki rata dashi . Zeenat tace "Kin wani tsareni da idanunwa narai narai kina kallona ko baza kiyi bane ? a tsanake batare da wata alamun tsoro ko fargaba ba nablah tace "zanyi .. "Ok minti biyu kacal nabaki na ganki a kitchen "idan kika kuskura kika bata min lokaci zakiga yadda zan ci ubanki a gidan nan " tana gama fadar haka ta juya fuuuuuu ta soma tafiya tana kunfar baki. Nablah tayi zuru kawai tare da bin bayan Zeenat da wani irin kallon mamaki da alajabi abinda tayi mata. dan ko kusa batayi tsammani zata fuskanci irin wannan babbar wulakancin mai cike da al,mara ba. "Yau itace akan aiki ta jawo aka zagin mahaifinta..abanza uban ta fa aka zaga ? ta furta akan akasan ranta, wato silar aikinkinta ne jawo a dinga wulakanta mata uba Haka km ma har da kiranta da sunan baiwa...? "baiwa fa ta kirani dashi? ta sake maimaita sunan a filli gabadaya abin yazo mata wani iri km abazata" tamkar ba gaske ba. " Anya kuwa rayuwar zata yiwu a Haka tun ba,aje koina ba an fara da zagar mata mahaifnta? " Anya kuwa zan iya daukar wannan kalar kaskancin da iskanci kuwa ? abinda ta tmbyi kanta da kanta Kenan. ahankali ta furzar da iska ta bakinta tana furta "wlh da sake Dan zan iya daukar komai na kunci rayuwa Amman Banda zagar min iyaye . taja tsaki itama tana harara kofar da Zeenat tabi ,cikin sanyi jiki ta nufi kitchen . Ko minti biyu ba tayi da daura ruwan abincin dare ba Zeenat ta karaso ta tsaya a bakin kitchen din " ke....ke.. " nablah dake tsaye tana jin Tayi banza daita duk da tasan daita take sannan km taki juyowa ... Sai ma cigaba da aikinta . Sai da Zeenat ta sake maimaita kiranta nablah da ke ..Kusan Sau uku sannan nablah ta juyo a tana kallon cikin idanunta Zeenat . Zeenat tace ,"Yar iska yarinya kawai kina jin mutane suna kiranki Amman dan dakikanci irin naki kika yi shr.." nablah ta hadiye bacin ran dataji yana taso mata tun daga tsintsiyar kafafunta ,sannan tace" kiyi hakuri basan dani kike ba" sbd ita kalmar ke.. din da kika ce bata daga cikin sunan nablah.... "eyyyye Zeenat ta fadi Haka tare da ta ware ido tana kallon nablah da mamaki "ni zaki kawa rainin hankali ? nablah tace "kiyi hakuri aunty barainin sense bane " a zafafe Zeenat tace "yi min shr stupid girl kawai ni zaki kalla kicewa ba sunanki ke ba.... Dan bakida mutunci ? " to kisani ni daga yau da sunan ke zan dinga kiraki ,Dan Allah idan na kiraki dan ubanki karki amsa kiga yadda zanyi dake a cikin gidan nan .. . nablah ta datse labbanta na kasa da karfi gaske jin zafin abinda Zeenat tace mata , kusan minti biyu tsakani nablah ta sake duban inda Zeenat ke tsaye har lokaci gabadaya gabobin jikinta sun sage muryarta cike da rauni km Haka kawai ta tsinci kanta da cewa kiyi hakuri aunty . da hannu Zeenat ta katseta .. "yimin shr dan bana son sake jin ko muryarki ne .. km ki sauke pot dinan ki daura min indomi yanzu yanzu taja tsaki tare barin kitchen din. cike da mamaki yarinyar Zeenat ta karasa ta zauna ranta a abace ta dinga fidda numfashi dan kwata kwata bata taba jin tsanar mai aikinta irin yadda take jin haushin nablah ba. Gashin yarinyar kmr bata da wani alamun tsoro atare atare daita . Cikin mintinan da basu wuce biyar ba ta sauke indomi ta yuye a plate sannan ta sake maida pot din abinci dare kan gas . zaune ta sameta ta hankice a parlour sai faman cika take tana batsewa tare da hura hanci 'tana kada kafa daya .. ahankali nablah ta ajiye mata plate din indomi agabanta akan center table tare da kwalbar vitermilk kana ta juya ,tabar parlour . ,banda tunanin da mamaki Zeenat bbu abinda nablah keyi . "ko meyasa ita ta kasance irin haka ba kmr ummi ba ,mai matsananin son mutane da kyautata musu" km tana lura da irin yadda ummi din ke matukar bawa duk wasu mutane dake shigowa cikin gidan, kulawa ta musamman " sabanin ita wannan bazanr matar mai kama da mutane China . nablah ta cigaba da aikinta na zagin Zeenat din aranta sai data gyara koina tsab sannan taje ta tambaye Zeenat din ko akwai wani sauran aikin da zatayi Dan gujewa cin mutuncinta . a yatsine Zeenat din ta dago fuskarta tamkar hadari sannan tayi mata nuni da hannuta alamun zata iya wucewa kawai . jikinta a mace tabar gurin , da kyar ta dinga daga kafafuwanta tsabar gajiya datayi , yayinda idanunta suka ciciko da Hawayen batayi kokarin hana hawayen idanunta zubowa ba,sbd tashin hankalin da take ciki, da wutar dake ruruwa a zuciyarta tana tafe tana kukan zuci yayinda hawayen idanunta ke sake cigaba da bin fuskarta... ahankali ta hau step daidai conar da zata kaita dakinta. anan suka kusan cin karo da deeni ,da ba dan Allah ya kiyaye da sai dai tajita a faffadan kirjinsa , sakamakon hannunta duka biyu datasa tana goge Hawayen idanunta .. daddaden kamshin turarensa ne ya doki hancinta a frigice tayi sauri janye jikina.. Ta makale jikin bango batare da tasan Tayi hakan ba , jikinta ya dauki kirrrrrrma hawaye km sharrrrrrr suna sake bin fuskarta ido cikin ido suke kallon juna ,itace ta soma janye idanunta ta runtse gam tana jinra kawai taji saukar mari , tsayawa yayi cak Shima yana karemata kallo up and down . A tsorace tasa tafin hannunta duka ta rufe fuskarta dashi.. kirjinta na sake daukar lugude . Ahankali ya ja wani irin mugun tsaki wanda hakan ya sake jefe zuciyar nabla shiga cikin rudani . yana tsananin jin haushi yadda yarinyar ke behaviors kmr wata dakiykiya harara ya zabga mata kana ya sake jan tsaki sannan ya ya soma taka step ,tana jin takunsa har sai da yakurewa step din Sosai sannan ta bude idanunta da sauri ta fada dakinta tare dannawa kofar key .. ta fada kan gado ta karasa fashewa da wani sabon kuka.... Mai cin rai blaming kanta kawai take ta yadda tayi sanadin jefa kanta cikin damuwa" me ya kawoni cikin wannan matsala? "meyakawoni cikin wannan gidan ? "meyasa na kawo kaina cikin halaka irin haka ? " anya kuwa nayiwa kaina adalci Dana zabarwa kaina irin wannan rayuwar ,mai cike da kaskancin da wahala ..? "Anya kuwa zan iya cigaba da yin wannan aikin kuwa ? Haka ta dinga jerowa kanta tambayoyi iri iri batare da tasan abinda yakamata Tayi ba .. "yanzu irin rayuwar da zanyi kennan? Ta sake jeho kanta tmby. agigice ta tashi zaune ta jingina bayanta da jikin gadon dakin tare da zubawa celling dakin Ido tana tunanin abinda yakamata tayi "shr ya biyo baya na wani dan lokaci . tuno auntynta da tayi ne yasa tayi saurin sauke ajiyar zuciya, Dan tasan ita kadai ce zata iya fidda ita a wannan halin wulakancin da take ciki , batare wata matsala ba," ai aikin bai zama dole ba , da sauri ta hau goge Hawayen fuskarta tace zan kwantar da hankalina na zuwa wani lokaci "kafin na samu yin waya da auntyna . ahankali ta Mike tashiga bayi ta dauro alwala sallar magrib koda ta idar ma bata tashi ba sai datayi isha'i a gurin , bata bi takan komai ba dan ko abinci bataji zata iya zuwa ta sakawa cikinta . ballallantana ta hadu da hawan jini ,da ciwon ulcer wato deeni da Zeenat . Ta kwanta anan ta dunkule jikinta cikin hijab tare da lumshe idanunta kawai" duk da ba wani bacci takeji ba, ahankali tarinka jin yadda zuciyata ta soma beating dip....dip.... kafin daga baya ta shigayi da sauri da sauri sakamakon tunowa da deeni da tayi ... "Tarasa dalilin dayasa duk sanda tayi arba dashi ko ta tuno shi take shiga cikin tashin hankali, ba. addu'a tasoma aciki zuciyarta "ya Allah...ya Allah kamin tsari dashi da duk wani wani shirin dake tattare dashi . " Allah idan zamana acikin gidan nan alkhari ne a rayuwarta Allah kasamun natsuwa da hakuri zama da matar gidan ,idan km bbu alkhari Allah ka fidda cikin kowace irin maseefa cikin sauki . haka tayi ta addu'oita , har taji zuciyarta ta dan samu natsuwa daga tashin hankali data shiga na wuncin gadi ,daga karshe bacci mai nauyi yayi gabadaita. Acan kasa kuwa DEENI ne kwance akan thrre sites hannunsa rike da remut yayinda zeenat ke zaune a gefenshi suna hira ,rashin ganin nablah yasa duk ummi ta damu har ta kai ga tambayar zeenat ita , ummi tace "ni kuwa ina yarinyar nan nablah take ne har yanzu banga saukowarta ba ko lafiya? deeni dake zaune yaji gabansa ya fadi zuciyarsa tashiga harbawa . " zeenat ta Dan yatsina fuska kana tace "wa ummi .ai tun dazu kafin ki dawo ta sauko taci abincinta ta koma dakinta da yake fita ummi tayi yau . Ummi tace "ok na jita shr ne sannan ta cigaba yabon nablah "yarinya mai hankali wlh . Zeenat taji magannun ummi na neman saka mata ciwon kai ,tams barta da karyar data sharara mata ta ba gaira ba dalili . Zeenat ta Mike tsaye tsam tare da yiwa ummi sai da safe Dan itama yau bacci take son yi da wuri sbd tana da lecture karfe goma daidai na safe .. . ita data shiga dakinta da niyar samun natsuwa Amman zuciyar ta shigo mata da tunani iri iri ciki kuwa har da maganar haihuwar da bata km samu ba har yanzu wanda shine jigon rayuwarta a gidan mijinta .. Byn tafiyar Zeenat ummi ta dago Ahankali tana duban deeni tare da kiran sunanshi.. DEENI dake kwance ya amsa hade da dan mikewa zaune ya mai da hankalikasa kacokan a kan umminsa . Ummi ta numfasa sannan tacigaba " deeni naji kamin shr game da zance yarinyar nan mai aiki... , gabansa ya yanke ya fadi rasssssss ...jin abinda ummi tace "ya zubawa ummi ido kawai yayi shr ya rasa me zai ce mata " sai ma shiga wani yanayi da yayi . ahankali ya runtse idanunshi yana Jin tamkar ummi ta watsa masa ruwan zafi yake ji da wannan maganar yarinyar da tayi masa. dan zuwa yanzu ya dauka ummi tabar zance ne kwata kwata ganin bata sake mishi maganarta ba . "ummi tace" kamin shr DEENI idan kasan baka shirya yin komai ba akai ba ,me zai hanna ni ka barni na aiwatar da komai domin nasan abinda zanyi .. "ahankali deeni ya bude rikitattun idanunshi ya zubawa ummi kawai yana kallonta ,kada masa kanta tayi alamun abinda ta fada din haka take nufi . yace "first lov kiyi hakuri Dan Allah zansan abin yi Amman dan Allah ki dan karamin lokaci kadan kinji first lov . Ummi tayi shr can Kuma tace "shikenan Ni dai burina bai wuce nasamu abinda nake fatan samu daga yarinya ba .. tana Ga fadar Haka ta mike tana mishi sai da safe . Karfe shadaya daidai deeni Ya shiga dakin Zeenat byn ya gama shirin bacci cikin wasu ratsasun kayan bacci masu matukar kyau. batasan da shigowarsa ba tana can duniyar tunani "ahankali DEENI ya karaso har inda take tare da kamo tafin hannuta cikin nasa Yana murzawa sannan ta juyo 'ahankali tana sauke naunauyen ajiyar zuciya. ya tsareta da idanunshi kawai sannan yace" meke damunki Zeenat ? "Ke ke nan kullun bakya gajiya ,ki raba kanki da wannan tunani ,kisan tunani shine abu mafi sauki dake saurin na kasa rayuwar Dan Adama Amman ke kin maidashi abincin cinki kullun .. kinsa Allah ba tunaninki ke damuna ba ,halin da first lov zata shiga sanadin wani abu da zai sameki nake . idan kinsa akwai abinda ke dumunki please tell me... tayi shr kawai tana kallonsa sun dade a haka suna kallon junansu sannan , ko me ta tuna Kuma ta sakar masa murmushi karfin hali ta matse hannushi cikin nata gam tare da lumshe masa idanunta ta girgiza masa kai alamun bbu komai . Deeni yace I you sure babu komai? " ta dage masa girarta daya kmr yadda yake mata shima, har taso ta bashi dariya yayi murmushi tare janyota jikinsa ya rungumeta ajikinsa tsam tsam Yana aika mata da sakwanninsa masu matukar birkita mata kwalkwaluwa .. hannuwansa duka yasa ya zagaye kugunta dashi Haka kawai Yashiga aiyanata yarinyar ce, 'ahankali ya sake narke mata ajiki yana shafa duk inda hannushi yaci karo dashi ,itama cikin kwarewa tasoma romancing dinshi . ranar dai kwana sukayi suna jiyar da kansu dadi deeni yayi Tayi batare gajiya ba . Iya murzuwa Zeenat Tayi shi a hannun DEENI har sai data saka masa kuka sannan yabarta ya Mike Yana mata korafin tacika ragunwaci. ita batace masa komai ba . washegari gari ma da kyar ta tashi yayinda da kyar ta dinga daga kafafunta , bayi tashiga ta gasa jikinta da ruwan zafi . bai ta bar gidan ba Sai wuraren 9 AM .. ..

MMN SUDAIS CE

AUREN SIRRI Donde viven las historias. Descúbrelo ahora