AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDO
Page 117
Tun karfe bakwai na safe nablah ta shiga kitchen domin daura musu abinda zasuyi breakfast bisa ga nata adalcin ,ta shirya abinci kala kala kusan kala biyar masu rai da lafiya ta shirya dinning ta koma d'akinta ta tsalla wanka tasha kanan kaya wando pencil jeans da riga pinky wace gabanta aka rubuta I promise to be with you ta gyara gashinta ta tufke shi a tsakiyar kanta da rebon ta janyo wayarta dake charge ta shiga yanar gizo tayi zurfi sosai sai dai duk abinda take hankalinta naga mijinta.
su deeni kuwa basu samu damar fitowa ba suna can suna gurzan junansu shida zeenat tmkr sabbin shiga amarci , sai gurin daya na rana Sannan suka fito kasancewar week end ce.
aiko nablah ta sake cika tayi fam ta dinga jin haushin deeni Cikin ranta har da kiransa jarabbbe kawai ,wani lokacin km har hawaye ke zubo mata , Sun sha kyau sai kamshi suke zubawa tare suka jero zuwa dinning table da yake nablah ta kira a waya tasanar mata ta gama shirya dinning, zeenat tayi mata godiya.
Byn Sun kammala da breakfast suka nufi ainihin main parlour 'n din gidan deeni ya zauna kan three star yana kunna TV da remut , ita kuma zeenat ta kwanta ta daura kanta bisa laps dinsa.
Wuni ranar duk inda kaga deeni da zeenat manne suke da junansu kmr zasu had'eye juna no any space atsakaninsu,
ko tana kwance ajikinsa, ko bisa cinyarsa suna shan soyayya.yayinda hkn yayi matukar d'aga hankalin nablah zuciyarta takasa sukuni da sakat ,dauriya kawai take irin nata da hakuri, yayinda shi deeni ya dinga zakewa, wani abun ma da biyu yake dan kawai ya kular daita ya tunzira zuciyar nablah da nuna mata ba'ita kaɗai ce matarsa da zata dinga shamasa kamshi ba ,Sai da yamman sosai zeenat suka rabu da deeni kowa ya kama gabanshi sbd lokacin duty nablah ya shigo.
Ahankali ya shiga dakin nablah bakinsa dauke da sallama, ko kallo bai isheta ba ta amsa sallamar aciki ,shima dan tasan mahinmacinta ne ,shima deeni ganin yadda tayi masa yasa ya shareta ya nuna mata ya fita iya miskilanci ,
daren rana deeni yaki zuwa dakinta yana son ganin iyakarta akanshi itama taki binshi dakinsa dan hk kowannensu ya kwana da zugin Zuci da rashin jin dumin junan dan'uwansa .Washegari
girkin zeenat ta shiga kitchen da kanta ta shirya lafiyayyen abinci tuwon farar shinkafa da miyar ogoro soup wacce taji kayan hadi nama da busashen kifi ,da jusit din cucumber ta tasha kwalliya da wata arniyar gezner sai kamshi take zubawa kana ganinta kasan ita din wace ta taso cikin gata da arziki ce .
suna zaune gabadayan su a parlour har nablah lokacin yaran na tare da baba bilki tana masu wankan yamma nablah ta hade cikin riga da siket wanda suka kar'bi jikinta suka fidda Shep din surar jikinta kana hango tudun nonuwanta azahirance bazaka taba cewa ta haihu ba tana da tuwon dukiyar fulani deeni ya dawo zeenat ta mike tsaye jikinta na rawa gurin tarosa tana bashi hot kiss ta ko ina.
Ta ciro hanky wanda yasha kamshi turare ta soma goge masa fuska dashi duk da ba wani gumi ta gani fuskarsa nashi ba , ta jawo hannushi zuwa hanyar dakinta ,nablah tayi masa sannu da zuwa yana tafiya ya amsa,
zuciyar nalah tayi tmkr ta buga ta shiga tsalle tana Kai kawo" kai ashe hk kishi yake da ciwo da Cin rai ? har ta dinga adduar Allah yasa ayiwa zeenat kishiya alokacin tana matsayin me aikinta ashe abun kanta zai komawa , Ta bi bayansu da kallo wato ko gurinta baza'a Barshi yazo ba
ko ɗan kiss din nan daya saba yiwa duk wace ba itace dashi ba , tayi shr kawai tana nazarin abubuwa.
YOU ARE READING
AUREN SIRRI
FantasyMATARSA CE TAKE ZUBAR DA CIKI BISA WANI DALILI NATA WANDA SANADIYAR HAKA SURUKARTA TAYIWA MIJIN DATA FI QAUNA FIYYE DA KOMAI A DUNIYA AUREN SIRRI DA ME AIKINTA BATARE DA SANINRA BA..