AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDO
Page 96
"idan ance maka kana son yarinyar nan nablah kace Sam baka sonta
" yanzu gashi nan tsabar kishi ji yadda gabadaya yanayinka yakoma
tunda Na haifeka deeni har zuwa yanzu ban ta'ba ganin kamanninka sun sauya ka zama wani irin mutun abun tsoro kmr irin yau ba ."kama manta da cikar burinka wato 'cikin dake tare daita sbd tsabar kishi idanunka sun rufe kazo ka kwakwad'awa yarinyar mutane mari,
in banda ma Allah Yasa Ina nan nashiga tsakani da sai kamata dukan dakayi asarar bby'n cikinta ."idan ance kana sonta kace Kai ba Haka ba yanzu meyye wannan kayi ?
"Deeni Ga son yarinyar nan k'arara Ina Gani acikin kwayar idanunka tare da zunzurutun kishinta Wanda Yasa har zuciyarka ke bugawa da karfi, alokacin fa daka shigo dafe da tsaitin kirjinka kake sbd tsabar jarabar kishi da kunar da zuciyarka ke maka akanta ...
"Deeni kana son yarinyar nan ko ka yarda ko karka yarda kanawa nabla wani irin mahaukacin so ka duba yadda kishi Yasa zakawa yarinyar nan nakaso,ka duba yadda kake huci kmr zaki , ka duba yadda ka kama Yar mutane zaka mata dukan mutuwa kana kokarin son illata musu 'ya deeni ..
" tunda ummi tasoma mgn deeni Yayi shr kawai yana sauraronta batare da Yayi yunkurin cewa komai ba.
sai ma rikitattun idanunshi daya tsura mata yana mata wani irin kallo me cike jin tsoron furucinta ...
"uhm kayi shr kana dubana kaki cewa dani komai, sbd kana tunanin zance na ba hk bane.. muryarsa a sarke km can kasa kasa yace "first love ....sai km Yayi shr ..
" Deeni kennan karyata mgnta zakayi ko ?
" Ba wai karyatawa zanyi ba first love Amman ni bana jin hkn atare dani km har cikin zuciyata da ruhin jikina bana jin wai sonta nake ..Ni dai nasan Ina matukar kishin igiyoyin aurena dake kanta ya k'arasa fad'ar Haka zuciyarsa Na tsananta bugawa da sauri da sauri....
"Babu komai lokaci shi zai nuna Haka
can km ummi tayi kasa sosai da muryarta" ni dai Dan girman Allah ka sausautawa kanka akan lamarin yarinyar nan..
Sannan km karage wannan mugun son da kake mata sbd gaba.. domin idan har yadda nake hango tsagwaron kaunarta 'cikin idanunka idan suka zarta hk akwai matsala wanda gaba bani da abinyi ...." ka tausayawa zeenat dina kada ta fuskanci wannan son da kakewa Nablah " ka boye mata kada ruhinta Yayi baki wanda nasan sanadiyar hkn zata iya shiga 'cikin wani hali ......
"hakika Ina tausayawa diyata ummi ta k'arasa mgnrta tamkar zata zubda hawayen tausayin zeenat.jikinsa a matukar sanyaye ya kamo hannuwan ummi dukka cikin nashi sannan ya Kira sunanta ... "first love ki daina ce min hk sannan ki daina cewa Ina son yarinyar nan.
kada bakinki ya kamani .."bawai bakina zai kamaka bane deeni olready ka rigada kayi wannan saken...
dan ka fada tarkon soyayyarta ."Ni farincikinka shine nawa ka nutsu ka daina takura kanka akanta dayawa ....a zafafe ya Mike tsaye ta riko hannunshi dake 'cikin nata" Ina zuwa km sbd nace ka daina takura kanka akanta ne kayi fushi ..?
runtse rikitattun idanunshi Yayi sannan ya bude fess yana duban fuskar umminsa ..
" Sam wlh ba hk bane my first love zuwa zanyi nayi wannan yarinyar warning da kyau "
Dan wallahi first love zan iya ilatata a duk sanda Na sake ganinta da wani Kato ...
"karka sake ka kuma ta'ba lafiyar jikinta ..
Cikin jin zafin abinda ummi tace Ya kamo lips dinsa na kasa yana cizawa yana zame hannunshi cikin nata tare da hawa step ...yayinda duk wannan dramar da'ake madam zeenat Na can dakinta ta manne kunneta da earpiece tana faman aikin chatting..
Yana shigowa dakin ya isketa zaune tana kuka sosai har da shesheka wani irin kallo wulakanci ya jefo mata wanda Yasa kirjinta bugawa da sauri ta yunkura ta Mike tsaye da saurinta jikinta Na kirma ..
a fusace deeni ya nuna Nablah dake tsaye da Yatsansa daya kana yace "Daga Ina wannan mummunar mutumin ya daukoki ?
YOU ARE READING
AUREN SIRRI
FantasyMATARSA CE TAKE ZUBAR DA CIKI BISA WANI DALILI NATA WANDA SANADIYAR HAKA SURUKARTA TAYIWA MIJIN DATA FI QAUNA FIYYE DA KOMAI A DUNIYA AUREN SIRRI DA ME AIKINTA BATARE DA SANINRA BA..