AUREN SIRRI EPISODE 102

318 10 0
                                    

💗💗💗💗💗
  AUREN SIRRI
     💖💖💖
💗💗💗💗💗





*AYSHA A BAGUDO*









Page 102


Ummi ce ke saukowa a hankali daga matattakalar benen Gidan  har ta karasa sauka parlour'n gabadaya idanunta a kan deeni  tana mishi  wani irin kallo mai tattare da tsansar tuhuma tare da tarin tambayoyi, shi kuma Deeni ganin irin kallon da umminsa ke jifansa dashi Yasa   duk sai yaji wata matsananyar  kunya ta kamashi.
sunkuyar da kanshi kawai  yayi   yana Sosa byn keyarsa alamun rashin gaskiya atare dashi domin jikinshi ya bashi tunda yaga yadda umminsa tayi.
ba mamaki ta ganshi tare da sanyin idaniyarsa numfasawa ummi dake tsaye a gabansa tayi wace ta kasa yi masa mgn sannan can   ta jinjina Kanta tace "ni zan fita Amman iyakacina cikin estate dina ,Dan tunda akayi haihuwar nan ban leka koina ba . muryasa 'cike  da mayyen   shauki kaunar dake tangaliliya dashi yace" alright first love
muje Na kai ki duk inda kike son zuwa.
   da hannuta ta katseshi tana girgiza masa kanta alamun Yayi zamansa ta karasa inda take zaton nan nablah ta shiga tayi gyaran Murya tana duban bayan Nablah dake kokarin daukar heater ta juyo ahankali tana duban ummi  tare da gaida ita Dan kwata kwata ranar Sau daya suka hadu .

Ummi ta amsa tana cewa "to ni zan Dan fita ki kula da yaran nan  sosai please.... idan kina bukatar wani abu ki sanarwa zeenat sannan yanzu aikin me zakiyi hk ?

"Duk abinda kike so Ga larabara nan ki sata zatayi daman nasanar mata tun baya kin  daina aikin komai agidan nan.

muryarta a raunane tace" ummi bawani aiki bane fa  ruwan zafi ne kawai shima wanda zan had'awa yara abinci ne Ok ta juya ta soma tafiya Sai Na dawo adawo lfy ummi Allah ya tsare .
Ameen batare da ta km juyowa ba .

Ummi na barin gidan Da sauri deeni ya shiga 'cikin kitchen din ya tsaya abakin kofa yana kallon bayan Nablah dake tsaye komai nata tsab tsab km gabadayan ta sauya masa tayi wani irin kyau amadadin tayi baki sbd ruwan zafi Sai ma haske ta kara kafafunta da yatsun hannuwanta suyi tas tas dasu abin sha'awa sak kana kallonta kaga me d'ayen jego wani irin abu yaji yana fixgarsa gareta .
ya soma takowa ahankali har  ya karaso  gareta ya sakala hannuwanshi duka ya zagaye kugunta dashi tare da d'aura ha'barsa a gefen wuyanta a Dan frigice ta juyo duk da tasan ko aikin waye .

ta inda ya daura habarsa  ta kalla idanunsu suka sarke 'cikin juna a take zuciyoyinsu ya buga da karfi ranta Yayi mugun dagulewa taja wani irin matsanancin tsaki wanda ya ta'ba zuciyarsa Amman ya Dane abinda yaji hk kawai nablah ta tsinci kanta da sakin wani irin raunatacce kuka 'cikin muryarta mara sauti yayinda Shi km ya Sai wani  sake narkewa yake ajikinta yana shinshina wuyanta tare da goga mata gashi habarsa, ta soma kokarin raba jikinta danashi tana kara sautin kukanta "please deeni ka barni wlh bana kaunar irin abinda kake min.

"Mai yasa  babu tsoron Allah acikin zuciyarka ne? kwakumarta Yayi sosai kamshin jikinta da kashin turaren da tayi amfani dashi suka nemi fidda Shi 'cikin hankalinsa har yasa shi jin kafafunshi sun Gaza daukarsa alamun zasu zube 'cikin wani irin maseefar shaukinta ya tattaro sauran kuzarinsa da yayi saura ya janyota zuwa jikin fridge ya matse gam ajikinsa yana sakin numafashi me gyaraye da huci me zafi.

cikin rawar murya me cike da wani irin rauni ya fara mgn .. "please kiyi hakuri da duk abinda kika Ga Ina miki nablah, ni nasan akan daidai nike ba wai rashin tsoron Allah bane Amman da sannu  wata rana zaki fahimci hk.
nablah tun iya tsawon rayuwata banta aikata zina ko rabar inda ake aikatashi ba domin ubangijina ya tsareni.
duk wani jin dadin rayuwa ko jima'i Ina yin sa ne tare da halalina Dan hk Dan Allah ki daina zubda hawayenki akan na rabi jikinki,Ki daina kuka  nima zaki sani kuka domin Na fiki jin rad'ad'in wannan kukan naki me cike da zargi da fassara iri iri .

AUREN SIRRI Where stories live. Discover now