AUREN SIRRI EPISODE 97

192 13 1
                                    

AUREN SIRRI
     💖💖💖
💗💗💗💗💗




AYSHA A BAGUDO




           
Page  97



Bayan Deeni ya koma d'akinsa Da kuzari ajikinshi ya fad'a kan makeken royal bed d'insa zuciyarsa cike da farinciki Mara misaltuwa,
shiru yayi kawai ya tsurawa celling d'akin idanunsa  yana tuna abubuwan  masu mahimmaci da dadi atattare da lamarin yarinyar..

Duk ta yadda  ya runtse idanunshi ita yake gani rungume ajikinshi tana aikin  sarrafashi  Da susuta masa jiki ,
gaba daya abubuwan da suka faru a tsakaninsu yanzu  ya dinga tunawa daya bayan d'aya Yana had'awa guri d'aya
sai murmushin dad'i  yake  had'e da lumshe rikitattun idanunshi ,
da kyar ya samu barci ya d'aukeshi cike da mafarkaiya  masu dad'i  .

Washegarin ranar da wani sabon  kuzari Deeni ya tashi fuskarsa wasai  d'auke da annuri babu wani alamar damuwa a tattare dashi ko bakinciki ,
sai dai kallo daya zaka masa ka gane miskili  ne Sosai   domin duk wannan farinciki Bai bari sun bayyana akan fuskarsa ba ,
miskilancin nan nasa na nan  ba inda yaje.

D'akin Nablah   ya nufa Kai tsaye ,tura kofar yayi ya shiga had'e da sallama,jingine ya sameta a jikin gadonta  hannayenta duka  a saman ruwan cikinta.
tayi zurfi cikin tunanin abinda ke faruwa daita lokaci xuwa lokaci ...

A duk sanda deeni yayi sex daita tana ji ajikinta duk da ba'a zahirance take ganin hk ba ,
Amman  tafi d'aukar abin amatsayin mafarki ne irin wanda ta saba  .

  Bata ji shigowar Deeni ba har sanda  ya  karaso gabanta bata sani ba,
zama yayi a Gefen gadon tare  da rungumeta  a faffad'an kirjinsa yana kaiwa wunyata sumba.

Ita kuwa nablah jin an rungumeta ya sata dawowa Daga duniyar tunani data lula tare da sauke A jiyar zuciya  da karfi ta tsura masa shanyayyun idanunta tana narke fuska .

Shima rikitattun idanunshi ya tsura mata yana kallon cikin kwayar idanunta masu narkar da zuciyarsa da gangar jikinshi ,ahankali yake fidda wani  numfashin sama sama tamkar wanda yayi gudun tsare ,
wani irin feeling's yake ji yana taso masa marar misaltuwa a duk lokacin da yake tare da ita.


sake lafewa tayi sosai  a jikinsa tana  sake sauke  ajiyar zuciya tana shakar daddad'an kamshinsa
sun d'auki tsawon lokaci a haka kowannensu da abinda zuciyarsa take saka masa ahankali ya d'agota daga jikinsa ya kafeta da rikitattun idanunsa, itama shi take kallo da shanyayyun idanunta.

fuskarsa ya had'e da fuskarta yayinda suke shakar  numfashin juna, cikin maganarsa Me kama da  rad'a yace "tunanin me kikeyi ne haka?"

Muryarta a raunane tace "  babu  komai fa  ta fad'a  tare da kauda fuskarta Daga gareshi,
yace "koma meye yakamata ki rage wallahi banason  tunaninnan da kike yi , kar yazo  ya shafi lafiyar babyna"
ya fad'a yana kashe mata ido tare da shafo cikin nata cikin wani irin shauki ya karasa fadar hk.

Bakinshi ya kai daidai tsaitin kunnenta yace" ki  shirya  anjima dake zan wuce   asibiti aduba min  lafiyarku ke da  bby nah
shagwab'e fuska tayi sosai tana turo masa Dan karamin tsukaken bakinta kana  tace "uhm uhm gaskiya ni banason  xuwa hospital
ko ba shi bama  ni gani nake tamkar  za'a gane  cikin dake  jikina.

Sai daya tsotsi lip's dinta sannan  " yace "waye ma zai  ganki, a mota ta fa zaki shiga"
tace "nidai a'a"
" shiiiiii banason jin komai Daga bakinki Yar rainin hankali kawai  Amman  shekaranjiya  da yake gidanku zakije bakiji kunyar fita da 'cikin ba, bananan ma kika yi tafiyarki ... sannan kina jin  tsoron xuwa hospital  sbd kada wani ya ganki da ciki  ,kika iya shigowa motar wani jaki tun daga geto area din ku har zuwa nan ,bakiji komai ba sai yanzu ne zaki kawo wa mutane salo.

AUREN SIRRI Where stories live. Discover now