AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDO
Page 87
Hannuwanshi duka ta damko cikin nata sosai tana sakin wani sabon kuka me cin rai tare da cewa" idan kuwa kayi min hk deeni bansan irin farinciki da zanyi ba a rayuwata ,jikinta har rawa yake gurin fad'ar hk ta cigaba da mgn "rabuwa da wannan cikin shine muradina a halin yanzu, Ni kaina wlh sai yanzu Na tabbatar da cikin jikina ,kuma duk hanyar da zanbi gurin salwantar dashi wlh zanbi ta shiga jijiga hannushi dake 'cikin nata Tana wani irin kuka me cike da ban tausayi .
Jin abinda tace yasa gabadaya gumi ya soma tsatsafowa ajikinshi tsabar tashin hankali daya tsinci kanshi ciki
, dan ko numfashi ma da kyar ya dinga fitarwa ahankali ahankali yana kallon 'cikin idanunta abinda ya dade shekara da shekaru yana nema shine yanzu Allah Ya amsa addu'arsa ya bashi ake kokarin , za'a zubar ......
da kyar ya samu ya tattaro dan abinda yake son ce mata ."Karki damu tunda har nace zan taimaka miki zanyi ne . sai dai mu bari muga zuwan doctor .. "Nagode.. Nagode.. Nagode..deeni bazan taba manta taimakonka gareni ba ,ta sake fashewa da wani matsanancin kukan ..
Cike da sanyin jiki da tausayin kanshi ya Zare hannuwanshi dake 'cikin nata ya Ciro daya Daga 'cikin wayoyinsa ya turawa doctor saira sakon test ..kana ya janyota jikinshi ya rungumeta tsam yana shafa bayanta kusan minti biyu suka d'auka a haka sannan ya d'agota cike da kulawa da tausayawa ya tsura mata rikitattun idanunshi" is Ok kukan ya isa hk kinji.
ta d'aga masa kanta kawai tare da cigaba da kukanta domin ita kad'ai tasan irin radadin da zuciyata ke ji a game da 'cikin jikinta .ranshi a matukar bace ya cigaba da kallon yadda take wani irin kuka Wanda yasan hkn zai iya shafar lafiyarta da dan dake cikinta .
dan hk ya furzar da iska me gauraye da huci kana yace" haba..me yasa kika fiyye fitina da wahala ne?"Nace miki kiyi shr hk zan San abin yi, ko so kike nazare hannun cikin lamarin cikin jikinki ?
Tayi saurin girgirza masa kai" Ok ki bar kukan nan hk bana son jin sautinsa kwata kwata ,nan ma sake girgirza masa kai tayi alamun taji .
"Kina jin yunwa ?
Tana jin yunwar Amman ta girgirza masa kai alamun bata ji .
Byn kmr minti goma shabiyar sai Ga doctor saira ta shigo office din hannuta rike da wasu file's tana yiwa nablah sannu da jiki .
nablah ta d'ago shanyayyun idanunta Tana dubanta tare da d'aga mata kanta alamun da sauki kana ta zarce zuwa mazauninta Tana jiran isowarsu .
DEENI bai tsaya jiran saukowar nablah ba ,Ya sanya mata hijab dinta ya nade hannun suit dinsa ya d'auketa cak..
ya rungumeta ajikinshi yana kallon cikin kwayar idanunta ji yayi tamkar ya tsotsi pinky lips dinta da suka sake yin ja .ahankali ya karasa Inda doctor take zaune ya zaunar Daita kan kujera yana sake gyara mata zaman hijab din kanta sannan shima ya zauna..
Yana maida hankalinsa sosai kan doctor saira sai daya sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ya soma da cewa" doctor wani taimako nake son kiyi min akan cikin jikin yarinyar nan dan Allah idan har zai yiwu Ina son a cire mata 'cikin jikinta ....
Doctor saira tayi shiru Tana sauraronsa har sanda ya dasa ayar mgnrsa , sannan tace "gsky mu hospital dinmu bama abortion domin doka ce me karfi idan aka kama mutun da laifin aikata hakan.
nablah najin hk ta zamo kasa da sauri Tana marairaice fuska da murya ,yayinda hawayen dake makale a idanunta suka soma ambaliya suna tureneniyya gurin fitowa ta hade hannuwanta duka guri daya tasoma rokon doctor
ŞİMDİ OKUDUĞUN
AUREN SIRRI
FantastikMATARSA CE TAKE ZUBAR DA CIKI BISA WANI DALILI NATA WANDA SANADIYAR HAKA SURUKARTA TAYIWA MIJIN DATA FI QAUNA FIYYE DA KOMAI A DUNIYA AUREN SIRRI DA ME AIKINTA BATARE DA SANINRA BA..