AUREN SIRRI
AYSHA A BAGUDO
Page 74sannu ahankali nablah ta dinga samun sauki sakamakon irin kulawar da ummi ke mata ..
Allah sarki ummi bawar Allah duk wani abu da tasan ya dace tayiwa nablah amatsayinta Na Virgin wacce akayiwa shigar sauri tayi ,yayinda ita kanta nablah batasan dalilin dayasa ummi take mata hankan ba ,
bakaramin kulawa ummi take bata ba dangane da aika aikan da DEENI yayi mata , dan yanzu bbu inda bata takawa da kafafunta .
Wanda hatta kabeer ba'a barshi a baya ba wajen zuwa duba nablah ,
Tare da kayan dubiya daidai karfinshi ,Ya Mika mata ledar da yazo mata dashi mai ruwan yellow da ratsin baki baki ajiki .
Ahankali nablah Tasa hannuta ta kar'ba hade dayi masa godiya jin dadi,ko bata bude ledar ba idanunta sun gama gane mata abinda kabeee yazo mata dashi
,kankana ce da ayaba sai abarba a 'cikin ledar.
Yayinda hakan yayiwa nablah dadi Sosai har a cikin zuciyarta, hakan kuma har 'cikin ranta taji kabeer ya birgeta matuka,
dan Haka ta sake sakin jikinta dashi sosa suna tashan hirarsu 'cikin Nishadi da annashuwa .
cikin Haka deeni ya dawo daga office on expected ya gansu tsaye abunsu hankali kwance suna sheka dariya.
yayinda kabeer ke tsaye da kodadden wandon Jeans da rigar polo tsab dashi , Dan Shima gayen babu laifi yana da nashi kyau daidai gwargwado ..
sai dai kwata kwata Bai kamo kafar DEENI da komai Na rayuwar duniya ba.
wani irin buguwa kirjinshi yayi da karfin gaske kanshi yayi masa nauyi tamkar zai tarwatse sakamakon ganin nablah da kabeer da Yayi tsaye suna wa juna murmushi.
Mamaki da tashin hankali ne suka caki zuciyarsa a lokaci daya,
Ahankali ya cigaba da takowa 'cikin takunsa nan nasa mai cike da kasaita da jin shi wani ne.
Ta kasan idanushi yake kare musu kallo tsab tare da sake mamakin yaushe ne shakuwa mai karfi irin hk Ya shiga tsakaninsu batare da sanin ba .
har yazo kusa da Inda suke tsaye basu lura dashi ba , Sai daya zo daf da shige su ne nablah ta ganshi sbd fuskarta dake facing dinsa ,
tsam.. Tasha jinin jikinta da irin kallon kasan idon da yake aiko musu dashi Dan Haka batare da wata damuwa ba Ta dan matsa gefe kadan domin bashi hanyar wucewa,
dan dama tsaye take abakin kofar da zai Kai mutun ainihin main parlour din gidan.
har ya shige ciki idanunshi basu daina hango masa ita Tare da wani namijin tsaye Wanda bashi bane.
kai tsaye dakinsa ya nufa ya bude fridge ya ciro ruwan faro mai tsanyi ya kafa robar abakinsa ya soma Sha bai ajiye ba Sai daya shanye ruwan Tare da yin flinging da robar gefe ya sauke naunauyen ajiye zuciya .
ya karasa ya kunna AC da TV kana ya zauna kan kujera yana fidda numfashi sama sama gabadaya duk wani farincikin daya dawo dashi gidan ya nema ya rasa.
zaune Kawai yake akan kujera yana aikin jijiga kafafunsa a kasa tare da xunduma kanshi 'cikin tunani .
Shr yayi tare da xubawa TV parlour,sa idanu Wanda idan ba tsayawa mutun yayi masa kallon tsab
zaka iya dauka a zahirance abinda da'ake gabatarwa a TV yake kallo ...sai dai abun ba hk bane Idanunshi ne kawai akan TV Amman hankalisa gabadaya da tunaninsa yana waje inda ya baro nablah tare da wani ,wani mai wanki gidansa...
A zuciye ya furzar da wata iska mai zafi yana jin haushin kansa da kansa , taya zai zauna akaron banza kawai yana tunani yarinyar da Bai da tabbas din cigaba da rayuwa da ita ....
amman duk da Haka abun yaki 'bacewa a idanushi .... "to me hakan yake nufi ?
"me yasa naji babu dadi sanda na ganta tare da kabeer yaje howa zuciyarsa tmby ?
Take zuciyarsa ta bashi amsa da "sbd aurenka da yake kanta ....
Ai ba ita kake tunani ba aurenka kake tunani kuma shine musababin dayasa kaji bbu dadi a ranka .
Ahankali ya runtse Idanunshi tare da hura iska ta bakinsa
tsawon lokaci ya d'auka zaune a gurin yana aikin saka da warwara .
kiran sallah magariba ne ya maidashi 'cikin natsuwarsa ya Mike jiki a sanyaye ya shige bathroom yayi wanka Tare da dauro alwala ya saka jallabiyarsa ya nufi masjid ba shi ya dawo gidan ba sai byn sallar isha'i.
yana dawo ya tadda su ummi tare da Zeenat suna hira ,
Zeenat na ganinsa ta Mike tsaye tana zuba yauki tamkar zata shige jikinsa
tace" har ka dawo my hrt?" sannu da zuwa"
YOU ARE READING
AUREN SIRRI
FantasyMATARSA CE TAKE ZUBAR DA CIKI BISA WANI DALILI NATA WANDA SANADIYAR HAKA SURUKARTA TAYIWA MIJIN DATA FI QAUNA FIYYE DA KOMAI A DUNIYA AUREN SIRRI DA ME AIKINTA BATARE DA SANINRA BA..