AUREN SIRRI
AYSHA A BAGUDO
Page 68
Zaune yake rigingine a bayan mota direbansa Na tukasa Ahankali ,
Yayinda Kirjinsa ke cunkushe da yawan tunan tunane iri iri, Wanda zuwa yanzu ya soma suspect din wani abu ne ke shirin faruwa da rayuwarsa Wanda gashi a hakikanin gsky ba zai iya cewa ga takamaiman abinda ke son ruguza farincikinsa ba .
Kallo daya zaka masa a yan kwanakin nan ka tabbatar da hakan sannan ka gane tsantsar damuwa dake dawainiya da rayuwarsa .
zuciyarsa ke rawa da raya masa abubuwa dayawa a game da yarinyar dake zaune agidansa ,
a duk sanda zuciyarsa ta motsa game daita kirjinsa ne ke wani irin bugawa da sauri ,Yayinda tunaninsa ke yawan barin gangar jikinsa zuwa wani bagere na daban.
" I don't believe what's actually happened to my hrt yarinya tamkar wata aljana ko mayya ta tsarke min kowani shashi Na zuciya da gangar jikina ,deeni ya fadi hakan akasan zuciyarsa yana mai furzar da iska mai Tumi .
Wit that thinking har suka iso gurin aikinsa zuciyarsa fal... da damuwa " sule direbansa ne ya fito da sauri ya bude masa kofar motar yana mai Sara masa , DEENI Bai bi takansa ba ya soma tafiya 'cikin isa da takunsa Na takama...
Duk wani abu dayakamata DEENI yayi ranar domin barinsa aiki yakamala da komai .
Sai dai he fell some how akan aikinsa da zai barin Wanda yataso da tsananin so tun ba yau ba .
amman gashi Yau ba yadda Ya iya da rayuwarsa dole ya bar komai ya mayye gurbin kujerar dad dinsa, a halin yanzu Dan shi yafi komai mahimmanci a tare dashi .
Duk abinda yake zuciyarsa Na makale da tunanin yarinyar ,Wanda ya rasa dalilin jin haka, duk yadda yaso ya yakiceta a zuciyarsa hakan ya gagara domin tunaninta kokari yake ya mamaye ilahirin santsar jikinsa ,"what should I do now to stop thinking about her ?
Ya tmbye kansa yana mai rantse idanunshi gam.
'Yana Cikin wannan tunanin ne wayar faruk ta riske shi ,tare da katse masa damuwar dake shirin zautar dashi , Ahankali ya sauke naunauyen ajiyer zuciya tare da bude idanunshi ganin sunan dake yawo kan screen din wayar yasashi hanzarta daukar wayar hade dayin sallama .
Bangaren faruk kuwa byn deeni ya amsa sallamarsa ,yace" aboki kwana biyu shr kayi Sika's ba'a ganinka ,wayarka ma Haka .
DEENI yace" kai dai bari kawai wlh abubuwa ne suka sani gaba da baya a yan kwanakin nan amman Na kamala da komai sai fatan alkhari kawai "
fk yace" ok kana gida ne ?
Bana nan Ina gurin aiki amman xuwa anjima kadan zandawo ," kazo gobe Ina son ganinka game da aikin da zamuyi start .fk yayi murmushi" manager da kanshi kennan ..a she zaka saduda 'cikin sauki Haka ? "wlh ban dauka zaka iya barin wannan akin naka daka kwallafawa rai ba .
DEENI ya ja tsaki dan takaicin barin aikin nasa sannan yace" yanzu ma kama tayi Shiyasa da kuma mahimmanci dad dina dan bazai yiwu Ina kallo wahalarsa ta tashi abanza ba ,km ko bbu komai su ya Mahmood da ya sulaiman suyimin kokari sosai akan dukiyata .
"Suma zuwa yanzu suna bukatar taimakona"
F k ya numfasa sannan yace" Haka ne ,nan dai suka shiga hirar duniya deeni yaji dadi hirar
data wanzu a tsakaninsa da amininsa Dan kashe dari ta damuwarsa ta ragu.
*****
Ummi kishingide akan kujera a hadadden parlour gidan yayinda safeena ke zaune kusa da ummi tana kallon zeeyword ita kuma Zeenat tana chatting a phone dinta .
DEENI yayi sallama hade da shigowa parlour kai tsaye ya nufi kujerar da ummi take zaune ya zauna kusa da ita hade da daura kansa a kafadarta yana wani narkewa sai kace karamin yaro ummi tasa hannu ta shafi sumar kansa cike da so da kulawa tace da alamun ka kwaso gajiya gashi inason zamuyi magana mai mahimmanci da kai .
take yanayin annurin fuskarsa ta dauke , Yar fara'ar daya shigo da ita ta ragu duk da Bai san takamaiman mgnr da ummi zatayi dashi ba , amman hakan Bai hanasa cewa "karki damu dani, first love bana tare da wata gajiya bara nayi freshe up na dawo muyi magana ya mike tsaye fuska nan tasa a hade ba yabo ba fallasa yana tsokanar ummi da" fatar maganar da zaki min mai dadi ce km wacce zata sakani farinciki, dan nasan maganar ummina duk masu mahimmanci ne da dadi sauraro yana gama fadar haka yasoma takawa ahankali cikin sanyi ya haura upstairs.
DEENI na shiga bedroom dinsa ya cire kakin jikinsa ya rataye ya saka rigar wanka yashiga bathroom ya sakar jikinsa ruwa .
byn ya fito daga wanka jallabiya fara kal... ya dauko yasanya tare da feshe ilahirin jikinsa da turare mai dadin kamshi sannan ya fice daga bedroom .
ummi da zeenat har da safeena duk suna nan a zaune a inda ya barsu tun kafin ya zauna safeena ta sake gaidashi ta mike tabar gurin yayinda ita kuma zeenat tashige kitchen .
Shi km ya zauna yana maida hankalinsa kacokam gurin umminsa yace ummi" Gani.
tace "eh naganka ai sannan ta kira sunansa deeni....Ya dago rikitattun idanushi yana dubanta dasu batare da yace mata komai ba sai dai gabadaya ya tattara ilahirin hankalinsa akanta .
cikin sanyi muryarta kasa kasa ta yadda bbu mai jinta sai shi DEENI din .... "hakika lokacin yayi da yakamata kasan abinda kake ciki domin zaman gidan nan shr ya soma gundurata.
zeenat ta dawo parlour'n hannuta dauke da cup din coffee ta Mika masa wata uwar harara ya gallamata sannan yace " bazaki iya ajiyawa ba ko zaki daura min akai ne ?
zeenat tayi murmushi kawai domin ita duk abinda DEENI zai mata baya damunta sai ma sake birgeta dayake karayi , Ahankali ta janyo karamin stole gabansa ta ajiye masa sannan ta juya ta koma dakinta tacigaba dayin chatting dinta ganin kmr suna bukatar abasu guri .
ummi tacigaba " a dalilin ina son ganinka da Ya'ya da Kuma saka diyata Zeenat cikin farinciki yasa na karfafa batun aurenka zuciyarka ta tunzuraka ba tun yanzu ba ,Ga wannan yarinyar nayi bincike akanta sosai ,irin kalar yarinyar danake son ka aura ce .
ganin maganar da umminsa ta dauko ne yasa shi mikewa tsaye hade da daukar cup din coffee tare da sanya hannushi ya kamo na ummi yace" ummi muje dakinki .
DEENI zaune a gaban umminsa yayi shr, ya hada uban tagumi kawai yana sauraron maganar ummi ahankali tace" na baka iya lokacin da naga zan iya baka akan maganar yarinyar nan Amman har yanzu ka kasa aiwatar da komai saboda kafi son ka auro Mai tsananin kyau da ilimi wacce tafi Zeenat Dina a komai diyar Wani kusa Kawai Dan ka kuntatawa diyata muryarta tamkar maishirin zubda kwalla tace "ko so kake na mutu batare danaga kwan ka adoron duniya nan ba ?
"gashi ina son ganin Zeenat cikin farinciki Mai d'aurewa, yarinyar nan nablah tana da hankali da natsuwa babban abinda ya kara jan hankalina gareta kyakwan tarbiyya da take da ita, ta kwanta min arai matuka fiyye da tunaninka saboda nasan zuwa Gaba bazamu samu wata matsala atare daita ba ,dan haka ina rokonka ka bari na dangana kaina ga iyayenta kafin mutuwata ta riskeni na bar Zeenat cikin kuncin rayuwa .
da sauri DEENI ya zaro idanu yana girgizawa ummi kai yayinda gumi yashiga ka karyo masa takoina ajikinsa, jin abinda umminsa tace hannuwansa duka ya daura a sama fuskarsa zuciyarsa ta taru ta hade kanta waje daya ji ya ke tamkar jinin da ruwa basa gudana ajikinsa yadda yake so ..
ahankali ya ciro hanky daga aljihun gaban rigar jallabiyarsa yana goge gumin dake tsaftsafo masa .
ummi ta sake kiran sunansa "DEENI ..."
ya amsa" na'am first love "idan kasan bakada abinyi da yarinyar nan kasanar dani na sallameta taka gabanta ku cigaba da rayuwarku kai da Zeenat Sai Dai nasan Zeenet Dina zata fuskanci matsalolin rayuwa ko ba gurinka ba Wanda ni Kuma abinda nafi tsana Kennan ...
Tun lokacin da ummi ta fara magana deeni yake kallonta har sanda yaji tayi shr da zancenta. Jin abinda tace ne yanzu yasashi danyi murmushin gefen baki ,Wanda yafi kama Dana takaici .
muryasa kasa kasa tamkar mai shirin yin rada yace "ummi kina nufin auren yarinyar nan zanyi akan gudun bacin ran Zeenat kennan?
"Kwarai kuwa na farko faranta ran Zeenat ,cireta daga cikin kangin dangi da kuncin rayuwa na biyu na gaji da ganinku haka domin bansan har wani tsawon lokacin zaka dauka kafin burina yacika ba , duk sa'annin aurenku bbu wanda bai da dan kansa, akwai masu uku masu duhu acikinsu .
ta gama fadar haka ta xuba masa ido kawai tana nazarinsa sosai.
yayi shr Bai sake cewa komai ba , " Amman kasan tun farko sai daka amince da yadda Na tsara kafin a kawota ?
ya daga mata kai tace" to meyasa yanzu kake son min yawo da hankali ko dan kaga a bukace nake da son ganin guda jininka kai da Zeenat shine ka maida zance Na wasa ?
ya hadiye abinda ya tsaya masa a makoshinsa ya kamo tafin hannuta 'cikin nasa yace "kiyi hakuri first love kin wuce wasa awajena duk duniya banida tamkar ki kece duniyata , na rokeki kada kiyi fushi dani akan wannan matsalar ,bacin ranki bakaramin babban tashin hankali bane atare dani.
Ya numfasa sannan ya cigaba " ina baki hakuri Dan girman kiyi hakuri ki sallameta kawai Dan banji zan iya auren da yarinyar nan akan wata manufa .
Abu na farko bana sonta ban jin akwai halitar dana tsana kmr ta ,tun zuwanta gidan first love narasa natsuwata Ni kaina ban san dalilin dayasa Na amince da zamanta gidan nan ba Sannan Bana jin zanyi AUREN SIRRI daita Ki taimaka ummi .
ummi ta hade fuska sosai tace " sakar min hannu" cikin sanyi jiki ya soma sakar mata hannuta kmr yadda tace .
Ummi ta xuba masa ido kawai tana dubansa Dan takaicin abinda yace , numfashi taja ta fitar sannan tace "son Na lura so kake ka bata min lokaci, Amman kasan ba dole nayi maka ba tun farko kaine da kanka ka bukaci kara aure ,kuma yan aiki nawa aka kawo gidan kafin ita kace basu maka ba?
da kanka ka amince da zaman yarinyar nan a gidan nan fa sannan yanzu zakace ga zance Ga mgn saboda Kaga ba irin type dinka bace a dole Sai ka auro wace zaka muzgunawa Zeenat ko ,amman bbu komai haka Allah yaso dani daman can bazanga jininku ina raye ba...
ta karasa mgnr 'tamkar mai shirin zubda kwalla.
muryasa a sanyaye "haba first love karkice haka ma akwai hanyoyin da dama dazamu bi gurin cimma burinmu ba lallai sai ta hanyar auren yarinyar nan ba.
taya za'ace kamata da matsayina da komai Na bige da auren kaskantacciya mara galihu irinta ?
Ai dana yi auren nan wlh gara hakura na cigaba da zama da Zeenat haka koda bazamu taba haihu ba .
Duk da ummi taji dadin furucinsa Amman Hakan Bai hanata katseshi a fusace ba ta hanyar daga masa hannu sannan tace "angaya maka sbd jin dadi ne kawai nake son kayiwa diyata kishiyar boye uhm?
" kasani badan haka bane ,kai kanka kasan dalilina aikata hakan ,zan aikata Hakan ne kawai a dalilin farincikin diyarta ...
" Dan haka idan kai zaka iya hakura da kowani irin auren Ni bazan zauna ba nan gaba diyarta tashiga tashin hankali akan rashin haihuwa .... .
" Ok first love yanzu abinda za'a yi ya, sunkuyar da kansa kasa sosai saboda jin kunyar abinda zai ce, cikin wata irin raunanniyyar murya yace" first love me zai hana tacigaba da zama agidan nan a matsayin mamata kawai batare da an daura aure tsakaninmu ba.
ummi ta tsare shi da idanunta 'tana kallonsa dashi sannan tana mamaki jin furucinsa , tamkar wani mai tabin hankali , Ahankali ta dinga aiyana
kode dan nata ya soma shayeshaye ne batare da sanin ba.
"inda wani ne ya tareta da wannan banzan mgnr da deeni yasanar mata da bakinshi ,to wlh da kotu ce zata rabata da duk Wanda ya fada mata hakan, Amman sai gashi, da kansa yake kokarin fayace mata ya gwammaci aikata lafin zina akan , yayi auren sirri da yarinyar .
Gumi ya karyowa ummi ta mike tsaye tana furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun ...'tana
ta sake kallonshi da jin takaici acikin ranta .
ganin irin kallon da umminsa ke jifanshi dashi ne ya sashi shan jinin jikinsa tare da ya sanin fadar maganar .
Duke kansa yake a kasa yana nadamar abinda ya fadawa ummi Wanda har Ga Allah ba nufinsa kennan ba" shi dai yafada ne kawai Dan yarasa yadda zaiyi da ummi .
Tsawon lokaci ,ummi Na tsaye 'tana binsa da kallon mamaki kana tace "wlh azim DEENI you really gave me double surprise .
sannan kuma bani kunya daman can abinda ka ke aikatawa da yaran mutane a gari kennan....bansani ba?
shine Dan rashin tsoron Allah yanzu kake kokarin ka fahimtar dani halin ka na boye.
Da sauri DEENI ya dago yana kallon ummi da rikitattun idanushi da suka gama rikewa suka dawo jawur tare da matsowa kusa da ummi sosai, yana mai girgiza mata kanshi tamkar wani karamin yaro.
Ummi tasa hannu ta dakatar dashi .. " kar ka kuskura kakaraso gareni deeni fatana Allah Ya shirya min kai shirin addinin Muslinci "first love Dan Allah kiyi hakuri wlh ba hali bane"
" nida katashi kabar min dakina kawai bana son ganinka a halin yanzu.
"ayau naji kunyar kasancewata uwa agareka ,deeni ban dauka haka zuciyarka ta gurbace da mayagun laifuka ba .
Kullun nake yabonka 'cikin kawayena da dangina ,dana tsananin kamewa mai daraja a cikin al,umma ashe bansani ba yaudarar zuciyata da mutane kawai nakeyi da kyawawan halinka .
Deeni bai daddara da kashedin umminsa garesa ba .
" yacigaba da karaso inda ummi take yace "dan Allah first love ki yarda dani karki min mummunar fahimta wlh bantaba aikata makamanci abinda na fada ba, baya ga matata ta sunna.l, Amman Ina neman afuwarki game da abinda nace.
ummi ta sauke ajiyar zuciya Ahankali 'tana godiya ga Allah duk da tasan ba halinsa bane Dan Tasha jin yadda mutane da dama suke yabonsa akan kyawawan halinsa ,
tasan irin kalar tarbiyar da tabawa dan nata ,sake sauke ajiyar zuciya Tayi ,Dan tasan ba'a shedar Dan ,yau .
Ya kamo tafin hannuta wannan karon bata hanashi ba ,ya sake cewa "Dan girman Allah first kiyi hakuri nayi nadamar fadar haka kinji Ya fadi hakan yana langwabar da kansa ,alamun Tayi hakuri.
hakan da yayi ne Yasa taji tausayinsa aranta yana sonta baya son ganinta 'cikin fushi da tashin hankali Dan haka ummi tace "to Shikenan naji Allah Ya sake Kare min kai .
Take yaji hankalinsa ya kwanta yayinda jijiyoyin jikinsa da suka tsaya cak suka daina aiki na wuncin gadi suka cigaba da aiki tare da sauke ajiyar zuciya.
Sannan ya numfasa tare da juyowa yasa hannu ya dauki cup din coffee ya soma kurba Ahankali ahankali .
muryar ummi yaji " yanzu km sai maganar auren ko Dan gaskiya yarinyar 'tana da abubuwa masu mahimmanci da zai sa a hada zuri'a daita .
A frigice DEENI ya zaro idannu waje coffee daya kurba bai san lokacin daya hadiye da karfi ba.
" ai ko ya sarke shi take yafara Tari kmr ransa zai fita ummi sai faman sannu take jero masa da kyar aka samu tarin ya tsaya ya dago rikitattun idanunshi da suka gama canza kala ya saukesu bisa fuskar umminsa .
" yanzu ummi bazata rabashi da zance auren yarinyar nan ba ya fadi haka a kasan ransa?
yayi shr can kuma ya fara magana ahankali yace" ummi duk wayannan ababen da kika lisafa akan yarinyar nan nifa ba ko daya da yayi min bawai na kushe zabinki bane " Amman zan aureta da zumar samun ya'ya daga gareta .
Dan a halin yanzu gara na zauna da zeenat kadai na karasa rayuwata daita ya karasa fadar kmr zai yi kuka .
ummi ta gyra zamanta ta riko hannushi tana sauke numfashi " ka amince aje ga iyayenta kennan ?
muryasa a sukwane yace "uhm Na amince zan aureta Amman ba Sai kinje da kanki nema min AUREN SIRRI ba... da kaina zandangana Ga iyayenta tunda oready kina da address din gidansu .
Ya cigaba" a gsky first love zan dai aureta yarinyar ne kawai badan Ina so ba Sai Dan farincikinki , na yarda ta zauna matsayin matata sannan ta haifa miki yaran da kike kwadayi samu daga gareta Ki bawa Zeenet batare da ita kanta tasan da zaman nine mijinta ba Dan sanin nine mijinta zai sa naji some how..'yana gama furta haka ya Mike yayi waje ranshi a bace zuciyarsa tamkar zata tarwatse tsabar takaici .ummi tabi bayansa da kallo sarai taji abinda yace a karshe sai dai bata fuskanci inda maganarsa ta dosa ba ,ta numfasa ita babu ruwanta da abinda yake nufi ,damuwarta daya ce ya amince mata da auren yarinyar, tunda ya amince mgn takare .
MMN SUDAIS CE
YOU ARE READING
AUREN SIRRI
FantasyMATARSA CE TAKE ZUBAR DA CIKI BISA WANI DALILI NATA WANDA SANADIYAR HAKA SURUKARTA TAYIWA MIJIN DATA FI QAUNA FIYYE DA KOMAI A DUNIYA AUREN SIRRI DA ME AIKINTA BATARE DA SANINRA BA..