AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDO
Page 93
Tare da aika mata da wani irin kallo me cike da tsansar jin haushin abinda ta aikata,
ba zeenat dake tsaye rike da kuncinta ba hatta ummi hankalinta Yayi mugun tashi akan abinda deeni Yayi domin bata ta'ba tunanin deeni zai iya koda zagin zeenat bane akan nablah agabanta ballanantana mari, marin ma ba d'aya ba har biyu ajire ..wani irin kallo zeenat ke bin nablah dake kamale ajikin mijinta kuma wanda tafi so fiyye da komai dake cikin duniyar nan Ahankali ta soma yin kasa kasa cikin slow motion ta zauna jagwab akan kujera data tashi tana cigaba da kallonsu zuciyata Na mata wani irin zafi da radadi .
kishin mijinta ne kawai ke cin ranta da kirjinta take zuciyarta tashiga harbawa da surin maseefa ..ta rantse idanunta gam dan bata kaunar sake d'aura idanunta a kansu dake like da juna tamkar wasu miji da mata ..
Yayinda nablah dake jikin deeni ta soma kokarin fixgewa Daga jikinsa Amman yaki sakinta sai kallon zeenat yake da rikitattun idanunshi, domin ita kanta nablah wani irin razanannen tsoro ne ya shigeta ta shiga tunani kardai da abinda take tunani ne ke shirin faruwa ?
"Kennan gaske ne deeni ya fada tarkon sonta ko yaya?
Matarshi fa ya mara agabanta akan cikin jikinta wanda tasan bashine mutumin da yayi mata ba idan kuwa haka ta faru bata San yadda zatayi da rayuwarta ba wani kuka me karfi ya kufce mata ..Ahankali deeni ya d'auke idanunshi akan zeenat batare da ya kalli inda ummi ke tsaye tana aiko masa da kallon mamaki ba yayi hanyar step da nablah a barin jikinshi har suka wuce zeenat bata samu damar bud'e idanunta ba sai ma wasu Hawayen takaicin ne suka samu nasarar biyo kuncinta gabad'aya komai ya tsaya mata cak.
"To me haka yake nufi?
"Me take shirin Gani yau a gidanta Daga dawowarta ?
"Allah Allah ka duba min al'amarina ....
Ka tausayawa rayuwata kamin maganin maseefar dake shirin kusantoni da al'amarina gabadaya, kada ka bari wata maseefa tashiga tsakanina da mijina,
Haka ta dinga fad'a a cikin ranta.ummi ta matso sosai kusa daita tana goge mata hawayen dake silalowa a kuncinta batare da tace mata komai ba Domin ita kanta taji mugun zafin marin da deeni Yayi mata a gaban nablah, amman tasan abinda zatayi ..
Har sanda deeni ya kaita dakinta kuka nablah take Na fitar hankali sbd gabadaya a tsorace take da ganin yanayin zeenat da ummi,cikin natsuwa ya karasa ya zaunar daita akan gadonta hade da janyo karamar stood din dake gefen bedside dinta ya zauna ya kamo hannuwanta duka cikin nashi yana murzawa ahankali ahankali tare da tsurawa beauty face dinta rikitattun idanunshi yana kallonta,
zuciyarsa Na masa wani iri tsalle tamkar zata tarwatse ta fasa kirjinsa ta fito muryarsa a sarke ya Kira sunanta ,"Nablah "
ta d'ago shanyayyun idanunta ta zuba cikin nashi kukan ya isa haka ....Ko wani guri Na miki ciwo ne?Ta girgiza masa Kanta batare da tace komai ba
"Ok ki natsu yanzu ki bar kukan nan haka kinsa bake kad'ai bace damuwarki zata iya shafar lafiyar bby nah ,
still shiru tayi taki cewa komai yayinda kuma aranshi ya dinga jin zafin hasarar da zeenat taso yi masa." meyasa zeenat bata tausayin takala da ra'barsa ?
" Meyyasa take kyamar talaka da nisanta kanta Daga gareshi ?
"Meyasa girman Kai da kudi ke fusgarta da yawa.. har ta dinga manta kalar tarbiyar da umminsa ta bata?
shi yasan wannan ba kalar tarbiyar umminsa bane sannan kuma ba halin mahaifiyarta ta dauko ba, mace me tsananin hakuri da son mutane ,Shi ya rasa Ina ta soma wannan halin nata Na girman Kai da Kin talaka da nuna kowa bakomai bane wanda ko acikin family itace leder ,gabadaya zuwa yanzu halayenta sun sake canzawa fiyye da kowani lokacin Wanda can da Bai santa da hkn ba Amman yasan hakan ma yana da nasaba da sababbin kawayen da tayi .
YOU ARE READING
AUREN SIRRI
FantasyMATARSA CE TAKE ZUBAR DA CIKI BISA WANI DALILI NATA WANDA SANADIYAR HAKA SURUKARTA TAYIWA MIJIN DATA FI QAUNA FIYYE DA KOMAI A DUNIYA AUREN SIRRI DA ME AIKINTA BATARE DA SANINRA BA..