AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDO
Page 101
Gabad'ayan suka fita daga d'akin atare zuciyar ummi da zeenat cike da matsanancin fargaba da tsoron abinda zai biyo bayan wata d'ayan da nablah tabasu..
zeenat so ta yiwa ummi magana akan hukuncin nablah akan baby's
Amman bakinta Yayi mata nauyi ta kasa cewa komai Sai dai ita azuciyarta taso ne ace ambar mata yaran gabadayansu ba wai aro aka basu da gindaya sharad'i ba..Bayan fitarsu nablah tayi kuka har da ciwon kai akan rayuwar data tsinci kanta ciki ,
Me zatacewa iyayenta da danginta akan yaran ?"Wa zata ce Yayi mata cikinsu ? Sosai tayi kuka tamkar ranta zai fita ..
Ita dai duk runtsi tana son ya'yanta kuma duk tsananin wuya tana tare dasu zata rayu da abunta domin sune duniyarta itace duniyarsu .
da daddare deeni ya shigo d'akin ta d'ago shanyayyun idanunta ta dube shi wallahi Sai taga duk ya rame mata Yayi Dan wuya , yaja stood ya zauna yana facing dinta idanunshi akanta tayi saurin yin kasa da kanta muryarsa a raunane yace "me dame kike so game da suna ?
ta sake d'ago shanyayyun idanunta ta dubeshi dasu tana maimaita abinda yace a cikin ranta ,muryarta a sarke tace ni Ina ruwana da wani suna ?
"Nifa babbar sunana ku gama abinda zakuyi da yarana Ku dawo min da abina na kama gabana .Ya kamo hannuta cikin nashi ya soma murzawa yana kallonta agalabaice " Karki damu kanki Ai za a dawo miki dasu
Amman kafin wannan lokaci Dan girma Allah ki saki ranki sosai kin dinga ci abinci kina basu nono sosai suna Sha duk kin bi kin tada hankalinki sbd yaran nan.
"uhmmmm dole ne naga kmr ana son a farmakeni akansu km mgnr ba da nono Ai ko bakace ba dole na basu idan ma ban basu me zanyi dashi?
numfashinsa ya sauke da kyar yana cigaba da kallonta ya kuma damko d'ayan hannuta cikin nashi yana murzawa ahankali ahankali yana kallon surar jikinta "nablah ya kira sunanta ta kalleshi ta sauke idanunta cikin nashi ,take kirjinsu ya buga da karfi ." wai bakya jin komai a game dani ne?
ya fad'i hk muryarsa cike da fargaban abinda zatace Sai data tsuke tsukaken bakinta had'e da lumshe idanunta sannan tace "me kake tunanin zanji a game da kai ?
"Wani abu makamancin felling akaina ko shaukin kaunata .........
Yayi mgnr yana matse yatsun hannuta sosai cikin nashi,ta girgiza masa kanta
"uhmmmm Gsky ni bana jin wani abu makamancin hk a game da kai Sai dai idan Kai ne ke jin hk agame dani .Yayi saurin lumshe rikitattun idanunshi na 2 second kana ya bud'e su fess yana kallonta tabbas abinda ta fad'a masa ba gsky bane ,
idan dai har shi yana jin wani abu akanta yasan dole ne itama ta kasance hk ..Ya Mike ya k'arasa gadon da babys dinsa ke kwance suna bacci ya sumbacesu d'aya byn d'aya amman ya dade akan baby girl dinsa yana kallonta yana jin kaunar yarinya Na sake huda zuciyarsa komai nata irinn Na nablah ne sak babu abinda ta d'auko nashi Sai hasken fata koda ya dawo gurin nablah har tayi shirin bacci ta Dan dube shi tace "kazo ka wuce bacci nake ji zan kulle kofa " babu damuwa kina iya kullewa kawai Dan nima anan zan kwanna .
"Bangane anan zaka kwana ba ? Tayi masa tmbyr a Dan hassale ,
Bai ce daita komai ba ya nema guri can karshen gado ya kwanta ,
Yana runtse idanushi
tazo inda yake kwance ta tsaya akanshi .. "please kazo ka bar d'akin nan
Nifa wallahi bana son ke'benwa da kai alhalin Kai din ba muha..tun kafin ta karasa taji
fizgota bisa kirjinsa ya rungumeta tsam yana sakin numafashi "
kiyi baccinki anan babu abinda zan miki ...
Muryarta a matukar tsorace tace "gsky ni a'a" "ada can baya banyi komai dake ba Sai yanzu kina jego ?
Ta bud'e baki kenan zata sake yin mgn ya had'e bakinsu guri d'aya yana girgiza mata kanshi da lumshe mata rikitattun idanunshi masu kashe mata sansar jikinta,
Dole tayi shiru ta lafe a fad'ad'd'en kirjinshi tana fidda numfashi sama sama shi kuwa ya cigaba da tsotsar bakinta.
YOU ARE READING
AUREN SIRRI
FantasyMATARSA CE TAKE ZUBAR DA CIKI BISA WANI DALILI NATA WANDA SANADIYAR HAKA SURUKARTA TAYIWA MIJIN DATA FI QAUNA FIYYE DA KOMAI A DUNIYA AUREN SIRRI DA ME AIKINTA BATARE DA SANINRA BA..