AUREN SIRRI EPISODE 86

199 13 1
                                    

AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗


AYSHA A BAGUDO


Page 86

Runtse idanunta tayi gammm..... wasu zafafan hawaye Na tsiyayowa akan kuncinta,  karo Na farko da taji wata mummunar qiyayyar wanda yayi mata wannan aika aikan ya shiga zuciyarta daram ya zauna  tare da huda duk wasu ga'bobi da jijiyon dake aiki acikin a sansar  aikinta.

koda kuwa ba halitar bil Adama bane ,wato jinsin jinni , kuka take sosai har dana fitar hankali
Kokarin zamewa take daga gangar jikinsa duk da yadda take jin kanta ajikinshi amman ta kasa raba kanta dashi , dan sake rungumeta deeni yayi tsam ajikinshi yana fidda numfashin ,cikin wani irin matsanancin kuka ta fara magana da muryarta da soma dashewa "ni ka sakar min jiki  ...

"kabarni nace ..."

"Kabarni  Naji da maseefar data sameni...."

" Ni nablah ke d'auke da cikin  shege yau ... ? DEENI ya shiga girgirza   mata kanshi batare da yasan ya aikata hakan ba   ...

"Kana jin abinda doctor tace  ciki gareni fa har Na tsawon wata hudu amman kake rungume dani ajikinka  ...ta karasa fadar hkn  tare da fashewa da wani sabon kuka me cike da cin rai da girgirza zuciyar ma'aboci sauraro...

ahankali DEENI ya sausauta rungumar da Yayi mata ajikinshi yayinda jikinta ya sake d'aukar kirrrrrrma  sun kusan minti ashirin  a haka , kafin daga baya  ya d'agota cike da kulawa ya tsura mata rikitattun idanunsa ,yana kallonta , da kallon yanayin tashin hankali da take ciki .

rasa yadda zaiyi da rayuwarsa yasashi  cigaba da kallon cikin kwaryar idanunta kawai  sannan ya hadeye abinda yaji ya tsaya masa a makoshinsa .

yayinda doctor saira ke tsaye tana kallonsu tamkar wasu jaruman shirin  fillm ,gabadaya al'amarin Nasu ya zauta hankalinta tare da girmama tunanita .
  "Barin ma Yadda taga deeni ya rud'e da gigicewa akan yarinyar, ko shine Wanda  Yayi mata cikin wa tunaninta iyakacin abinda zai yi kennan..

   ya cigaba da kallon yadda   kukan ke galabaitar daita ,
  "tayi mugun fita haiyacinta,
Ahankali  yasa hannushi ya kamo tafin  hannuta 'cikin nashi  yana shafawa da baya hannushi   'cikin sarkewar murya ya kira sunanta da sanyyayiyar muryasa .
da kyar ta bud'e shanyayyun idanunta ta zubasu  cikin nashi batare data amsa masa ba.

Ya lura gabad'aya jikinta a sanyaye yake ko dan yatsanta bata iya motsawa,kokarin son dagota yayi ta zame jikinta daga gareshi..

" ka barni DEENI bazan iya tashi ba.... ta sake  tsananta kukanta  me tsuma zuciya .

Muryarta a sanyaye ta dinga furta kalmar..."wayyohhhyyy Allahna.

" wayyohhhyyy Na shiga uku  ..waye  Wanda yayi min wannan cikin da bai  kasheni  gabadaya Na huta  da ganin wannan ranar me tattare da bakin cikin rayuwa ba?
  "... wayyo Ni nablah me zancewa mahaifina   da yace kada nazo aikatau ..?

"Me zancewa   yan'uwana da suka tattara  dukkan wata  yardarsu da amanarsu gareni tare da amincewa dani   ?

" Wayoyyy !wayyyyyoo!! Ni nablah wazan ce yayi min ciki......? Kuka take had'e da sambatu iri iri .

tausayinta ya sake kama doctor saira ya mamaye zuciyata sosai   har batasan sanda hawayen tausayin yarinyar ya shiga  tsiyayo mata ba
   , ahankali ta zare dan siririn medical glass din dake manne da fararen idanunta  ta goge Hawayen dake tsiyayo mata tare da maida medical glass dinta tana cigaba da kallonsu  ...

Mikewa nablah tayi da kyar tana layi... yayinda gafe daya kuma  tasoma ganin   juwa.
   batare da ta juyo ta hankalta da irin kallon tausayin  da doctor saira ke mata  ba
  " ta fara tafiya cike da damuwa da rud'anin rayuwa....

AUREN SIRRI Where stories live. Discover now