AUREN SIRRI EPISODE 60

241 6 7
                                    

AUREN SIRRI
      


AYSHA A BAGUDO




Page 60




Ahankali ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta wanda kusan rashin abinyi ne ke sata yin haka, haske taga ya garwaye parlour gabadaya 'koina ya dauki haske tamkar rana ce ba dare ba
wani irin kamshi ne mai azababen dadi  yake kusantota har inda take zaune ,yayinda mamallakin turaren ke tunkarowa  zuwa inda suke haka shima kamshin ke kai kawo acikin hancin nablah ,har zuwa sanda mamallakin kamshin  ya karasa  shigowa,  gabadaya parlour ya canza wani  irin cent na daban",  take gabanta ya shiga dukan uku uku  gashi tana san  dagowa ta kalli kowaye mamallakin wannan mai azababen kamshi Amman ta kasa dago idanunta,dan ko kwakkwaran motse kasawa tayi   ballanantana tasan ko waye mamallakin wannan turaren mace ko namiji ne sakamakon  kanta dake Duke   akasa har lokacin ta kafe teas din parlour da  ido .

Ta kasan idanunta ta hango wando jeans wanda hakan ya tabbatar mata  da mammallakin kamshi turaren nan    namiji ne
"duk da   bataga komai   nashi  baya ga Zara zaran yatsun kafafuwansa da kowani ke kwance da gargasan gashi   'ahankali  yake takowa zuwa inda ummi  take zaune  .

Muryar ummi  taji tana cewa "ka fito son ?
tun da zu  muke Jira ... "matarka tace wanka kake yi  ahankali ya  juyo ga  mahaifiyarsa  yana kallonta sannan ya danyi  murmushi gefen baki
   hannunsa yasa  ya  dauki remut ya canza channel zuwa ta  kallon Ball  sannan ya   Mike kwance kan  three siter hade da cewa "gani  first lov  anything for you my beautiful mum... 
Ummi  ta saki murmushi sakamakon jin dadi abinda yace  sannan tace"  kai ko Allah ya shirya min kai ...tare da kai  hannuta  kan tilon dan nata ta shafa tautausar  sumar kansa  tana jin wani irin sanyi a ranta .

Muryata A dake  ta kira sunansa deeni.....
Ya dago rikitattun idanushi yana kallon ummi batare da yace komai ba ...
  "maganar mai aiki da mukayi da kai za'a kawo   ,to orready ma  she's here..  ta iso sauran muji meye raayinka  , ni dai na  amince daita hundred percent  ..

kasa kasa yayi da muryasa wanda  daman can  haka  yanayin maganarsa take ..
Kuma yadda yayi magana  ummi  ce kawai zata iya jin me yace ..

"tana ina .......?

abinda kunne nablah  ya ji kennan " gata can ummi ta fada tare da nuna inda nablah take zaune ...

ahankali ya juyo tare da  kallon  inda ummi  tayi mishi  nuni da hannuta idanunshi ya runtse  gam sannan cikin sanyayyayiyar muryasa mai kashi jikin duk wanda tsautsayi yasa ya fada kunne shi " yace first lov...  kice ta Mike na ganta ..

tsoro da fargaba tare da  frigice ne  suka taru suka kaiwa zuciyar nablah farmaki" tashi daya taji   jikinta yakama rawa  gabanta yashiga faduwa da sauri, tasoma  tunanin abinda   ya kawota  wannan gida mai cike da abun tsoro da abubuwan ban mamaki ...

sai kawai ta tsinci kanta da ambato sunnan Allah a kasan ranta  da karanto  duk addu'ar datazo bakinta Dan rage jin tsoro " take taji wata natsuwa tazota mata   aboye ta dinga sauke ajiyar zuciya .


Ahankali ummi  takira sunata  "nablah  Mike tsaye  man ya ganki " batare da wata gardama ba ko bata lokaci ta Mike tsaye kmr yadda ummi tace ,Amman still jikinta Bai bar kirma ba haka ma  hannuwata suna sarkafe  da juna tana cigaba da wasa dasu  " yayinda ta cikin hijab dinta  kuwa uhmmmm tashin hankali kennan 'dan kuwa  jikinta sharkaf yake  da gumi tsabar frigici datake ciki  ,duk da tsanyi AC dake aiki a  parlour hakan bai hana  gumi tsassafowa ilahirin jikinta  ba .

idanunshi da Suke a runtse ya kafeta dasu yana kallonta ,jin shirun da yayi yawa ne yasa nablah dago fararen idanunta dan satar   kallon  mutumin da taji an Kira da suna DEENI  take zuciyoyinsu suka buga a lokaci daya .......


Yayinda  jikin nablah  ya dauki  kirma... zuciyarta ta sake amsawa daf..daf..'da sauri tayi kasa da idanunta  ta furta  "wayyo Allah na.. a kasan ranta.. mutun ko aljani nake Gani yau ./?

tsabar kyauwu halitta  da Allah yayi masa tunda take  a rayuwarta bata taba ganin mai tsananin kyawu halitta  da kwar jinin irin mutumin da take gabansa tsaye a halin  yanzu ba .

kusan   tsawon  minti  5 ya dauka yana kallonta batare daya bude Idanunshi ba" sannan 'ahankali ya dauke idanunsa daga gareta  yakoma ya  kwanta sosai acikin kujerar da yake "ummi  tace "ya'akayi ne DEENI  naji kayi shr...  ....

"Tayi....."
.
abinda kawai nablah ta iya  ji  kennan daga bakinsa , Dan gabadaya ma jitayi kunneta ya daina jin magana tsabar tsoro da rikici   hakan  km  sai lokacin hankalinta ya dawo gangar jikinta daga mummunar damuwar data tsinci kai  ciki ...
Amman fa duk da Haka  a tsorace take da mutumin dake kwance a gabanta .

ummi kuwa take ta shiga furta kalmar alhamdulilllahi kafin daga baya ta kalli nablah  a tsanake  tace" jeki nabla ma hadu gobe  kinji ..

muryar nablah a sarke tace "to ... sai da safenku" sannan   ta juya  cikin tsanyi jiki  ahankali take tafiya yayinda itama   ummi  ta juyo tana sake bin bayan nablah din da  kallo har tabar parlour  zuciyarta na karanto mata abubuwa dayawa game da yarinyar ga wani irin tausayin yarinyar daya mamaye zuciya ...


Bangaren   deeni kuwa gabadaya ji yayi tamkar am masa wanka ne da ruwan sanyi  , jikinsa ya mutu murus tamkar mara lfy haka ya dinga ji ajikinsa tun sanda yabi hannu ummi  da ido .

kwarai  yaso ya bude idanunshi yakarewa  yanayinta kallo Amman sam  ya kasa aitawatar da hakan , sai ma tsintar kansa da yayi da mummunar faduwar gaba a lokacin da yake kallonta , wanda har yanzu da yake kwance a wajen  bai daina jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri  ba ..

ahankali ya sake runtse idanunshi gam ko zai daina jin abinda yake ji  ajikinsa ,amman kwata kwata sabanin haka  Ya dinga  ji  Sai ma  zuciyarsa da ta cigaba da  harbawa da sauri da sauri .

abinda bai taba ji atare dashi ba kennan tun iya tsawon rayuwarsa wai faduwar gaba akan mace  ....
Macce ma , mai matsayin mai aiki ...

ahankali ya furta sunan  da yaji umminsa  takira yarinyar dashi "nab....lah... Yadda ba mai jinsa ....

muryar matarsa yaji tana cewa ummi  " ai wannan yarinyar bakaramin  daga mata tuta tayi ba ,  tunda har my hrt yace tayi.

ummi  tace "al,amarin Allah kennan nima gsky  naji dadi matuka da tamasa saboda da ganin  yanayin yarinyar ba tmby akwai natsuwa atare daita "kema kiyi kokarin ki sota a ranki " ba mamaki wata rana tayi miki amfani
  dan gani   bazamu samu matsalar daita ba .

AUREN SIRRI Where stories live. Discover now