AUREN SIRRI EPISODE 118

282 4 0
                                    

AUREN SIRRI
     💖💖💖
💗💗💗💗💗

AYSHA A BAGUDO

    
Page  118

Zaman makoki akayi na tsawon kwanaki uku sannan kowa ya watse ya kama gabansa, gidan ya saura daga shi sai ahlin gidan da yaran gidan ,sai  yan tsirarun mutanen dake zuwa gaisuwa daga wajen estate din.

duk yadda mutun ya kai da taurin rai da kafiya da rashin tausayi da imani idan ya kalli yadda zeenat ta dawo a cikin wannan dan kankanin lokacin wallahil azim sai yayi  mugun tausaya mata,km sai ya zubda  mata hawayen tausayi
,tayi wata irin muguwar rama  sbd tashin hankali datake ciki.

  sosai tayi dakiya irin wacce ake so mutun yayi yayinda damuwa
ta dakewa zuciyarta taki yarda tayi kuka a idanun mutane,sai kukan zuci da take ta fama dashi wanda yafi ciwo da radadi km shine yayi mugun tasiri ajikinta har ya ramar daita.

Byn mutane sun watse kowa ya dauke kafarsa agidansu hatta ummi ta koma gidanta ,gabadaya jikin zeenat a matukar sanyaye ta dan d'osana a bakin gadonta  ta zauna hawayen da Suka dan Ziraro mata ta shiga gogewa da hannunta wasu na sake zubowa wanda sai yanzu kukan rashin diyarta ke zuwa mata gabadaya yau tazo mata da abubuwa da yawa masu raunata zuciya, babban jigon ginshikin da take dubawa wanda a iya tsawon rayuwarta bata taba  tsamman zuwansa ba km yazo mata ya tafi .

Hakika taso kasancewa da diyarta su rayu da juna cikin kulawarta gashi km ta rasata a cikin lokacin da tafi bukatarta,  ta tabbatarwa kanta da hkn ma nufin  Allah ne ubangiji talikai km ta gode masa bisa  hukuncinsa gareta, abinda  take nema shekara da shekaru ta samu km tarasa tausayin kanta ya mamaye zuciyarta batasan yaushe ne xuciyarta zata samu yanci da salamar rayuwa ba.

abinda ya faru a shekarun baya lokaci daya ya sake bijiro mata ya mamaye  zuciyarta tunaninta ,ta kauce hanyar Allah da manzonsa km ta gyara kuskurenta na shekarun baya da suka gabata..
ummi ta fado mata arai Allah sarki umminah ta soma zance Zuci uwata jigon rayuwata kiyi hakuri da hukuncin ubangiji garemu ummi hk Allah yaso xeenat dinki ta kasance kin soni kin nunamin gatan da bakowa yake samun irinsa ba,kin rike zumuncin Allah ,har wani lokacin ina tmbyr kaina da kaina shin wani irin soyayya surukarta km umminah take mata?

Take ta mike tsaye jikinta babu kwari ta soma zagaye bedroom din nata ,tana tunani tilon diyarta data rasa cikin wannan lokacin  diyar data daurawa son duniya akanta  kasancewar itace duniyarta ....
sosai ta dauki lokaci tsaye tana kai kawo acikin dakin tana yiwa yarinyarta addua
Kafin daga baya ta karasa inda Jakunkunan kayanta wanda ummi tayo mata cike da kayan babys da hotunan yarinyar wanda suka dauka ranar suna.

Ta tsurawa hoton Amna ido tana kallon kyakkyawar yarinyarta wasu sabbin hawayen masu zafi da radadi Suka shiga silalowa bisa kuncinta nasoki tun sanda nasan da zamanki kwance cikin Marata ..
na soki tun bansa wace iri bace ke acikin cikina har zuwa sanda kika zo Duniya ina daura kwayar idanuna bisa kanki naji duk Duniya kece rayuwata..
kece farincikina , na soki fiyye da komai da kowa dake cikin duniyar nan .... Amman Allah ya fini sonki amna nah hawayenta ya jike hoton yarinyar dake kwance lullube  cikin wani tsadadden showel fara ce tas tas daita kmr uwarta da ubanta .

kuka take sosai tana sambatun rasa tilon diyarta datayi  ahankali ta zauna tana cigaba da Kallon pictures din yarinyar  daya byn daya kana ta ajiye hoton yarinyar bisa cinyarta ta soma bude kayan yarinyar daya byn daya tana kallo tana kuka me wuyar misaltawa ba taji shigowarsa ba sai kamshi turarensa taji ya ziyarci hancinta.

ya tsaya  daga can nesa jikin kofa rungume da hannuwasa duka bisa kirjinsa yana kallonta sama da kasa cikin wani irin yanayi mai ban tausayi ,nan wata kwallar ta sake cikowa idanunta jikinta  na Bari ta hau sharewa lokaci daya wani matsanancin tausayinta da km sanyi rahmar so da kulawa da take masa Suka bugi zuciyarsa lallai ya tabbatawar kanshi yana matsanancin sonta raba zuciyarsa daita Abu ne ME dan Karen wahala domin kowani bangare yana da dafin soyayya ta meida kanta kasa ya karaso ahankali ya  dafe  kafadarta da hannushi daya yana kallonta .

AUREN SIRRI Where stories live. Discover now