AUREN SIRRI EPISODE 108

405 10 0
                                    

AUREN SIRRI

Page 108

Ya tsura mata rikitattun idanunshi kawai  yana kallonta tare da jiran jin abinda  zatace masa yayinda  ahankali wutar sha'awarsa ke sake tasowa tana kokarin bawa kowa ni part na gangar jikinsa.

naunauyen ajiyar zuciya ya sauke  ahankali .
tare da sake sanyaya muryarsa "I've been talking to you and you're not replying me , plz talk to me, now zeenat.... so that I'll ve peace of mind, still shr tayi masa taki cewa dashi komai  sai dai  wani irin lugude da harbawa xuciyarta keyi har jikinta na shaking, domin Kalmar ta daina sonshi din daya Ambata tayi matukar mugun girgiza zuciyarta da raunana ilahirin jikinta cikin wani irin salo ya cigaba da murza tafukan hannuwanta cikin nashi yana sake tsareta da rikitattun idanunshi Masu saurin susuta mata gangar jiki da zuciya .

ganin yadda yanayinsa ya soma sauyawa zuwa wani babin bukatuwa gashi itama yanason tada mata  tsumin nata sha'awar ,yasa ta soma kokarin zare hannuta cikin nashi tana fizgo numfashi da kyar" Amman ina da sauri yayi saurin riko yatsun hannuta guda uku ya tsura mata idanunshi
Ido cikin ido suke kallon juna .
Ahankai ta tattaro jarumta ta sanyawa jikinta muryata a matukar raunane tmkr wacce zata zubda kwalla  tace "yaya... Kayi hkr please ka barni bana son kusancina da kai ahalin yanzu kai ko ke'bewa tare da kai banaso, ina son nisanta kaina daga gareka bana bukatar wani abu ya sake shiga tsakanina da kai....gabadaya Ina son na mantaka aduniyata Sannan  tabbas mgnrka babu karya " hakika muzeenat  ta daina sonka kmr yadda Kake tunani ,saboda   me zeenat zata  da zauna da mutumin da bai sonta bai kaunarta bai son farincikinta da walwalarta arayuwa sannan mgnr na canza maka suna na daina kiranka da zuciyata sau nawa Kana min gargadi da kashedi akan hk akan na daina kiranka da zuciyata ... hkn bai taba damuna ba  sai kaine yanzu kazaji babu dadi aranka dan na daina ... Ka rigada ka gama fice min arai ba km zan koma gidanka na cigaba da zama da kai alhalin zuciyarka naga wata ba ....
Kawai ni ka sakeni na hutawa Raina, kaima ka hutawa rayuwarka mu bar junanmu mu cigaba zumunci dake tsakaninmu ya ishemu.
" ahalin yanzu idan na tuna da wahalar dana sha a zama da kai ina jin tamkar na mutu  na barka a doron kasa ka cigaba da rayuwa da wacce ta fini daraja agurinka .

"duk da tarin abubuwan da Ka dinga min ina hadiyewa hk bai isheka ba yaya sai da kaga ka musgunawa zuciyata ta hanyar quntata mata.
ni dai na rokeka da girman Allah kamin afuwa ka sauwakemin aurenka ......
  "muryarsa  a kasalance tmkr zai Yi kuka yace" ki min afuwa zeenat wlh bazan taba iya sakinki ba sbd son da nake miki ,amman na yarda ki Xabi horo me tsanani wanda kike ganin yafi kowane horo wahala ki min shi na yarda na amince in dai zaki janye mgnr saki  ki koma gidana ....
bai gama rufe baki ba ta dakatar dashi  " wazaka yaudara  ni?
Ta nuna kirjinta da Dan yatsan hannuta tana sake kallon cikin kwayar idanunshi sosai "wallahi ko kadan kalamanka bazasu taba tasiri acikin zuciyata ba har su sanyaya min raina .
" waye zai yarda ya dangwama cikin damuwa da wahala da bakinciki rayuwa?
Kalli yadda na zama yaya .......
"nice fa wannan  muzeenat din da nke ji da kaina takowane fannin  kyau kwaliya diri uwa uba asali da nasaba me kyau Amman na zama abar wulakantawa agurinka bisa ga kuskuren da nayi maka ..
"ni wani irin hakuri ne ban baka ba Akan kuskurena gareka ?
"Wani irin azabtarwa ce bakamin ba 
Yaya?
"hk Ka Rufe idanunka ka min abinda kagadama batare da kula da wahalar dana sha ba gurin fitar cikin kansa. shine ni yanzu Kake wani bani hakuri na koma gidanka na cigaba da zama da kai ka K'arasa kasheni ko?

"  ni nasan ko mutuwa nayi alhalin yanzu baka da hasara yaya kana da me mayye maka gurbina koma nace wacce tafini da komai agurnka ni dai alfarma daya kawai nake son kamin wanda bai wuce ka Sa.....
a zabure ya mike tsaye  tare da katseta yana aiko mata da wani irin kallo yana Huci wanda sauran kadan anan ta fadi yayi saurin tarota jikinsa" kina hauka ne wai ko kuwa
kinsa abinda kike fad?
"Wannan wace irin maseefa hk? Sai lalla'baki nike kina botsarewa
laifi na miki na km baki hakuri kince na tsugunawa wata  a gabanki  tare da furta   ina sonta wanda nasan shine Abu mafi muni gareki wanda kike tunani na Miki kema km nace zan durkusa miki kince A'a nace ina sonki kin maida abun shirme to me kike son na miki?
na kashe kaina na baki shine zai Tabbar miki da ina sonki ko me ..?
kinsa Allah idan ma  zaki Hakura ki koma gidana ki koma idan km bazaki hakura ki koma ba fine kiyi tazama Saki ne dai ko zaki mutu bazan taba sakinki ba sai dai ki mutu da aurena akanki ...

"Ince gidan nan ma  shima tmkr matsayin gidana ne,  ki cigaba da zama acikinsa har randa kikaji zaki dawo gareni ni km wlh zan baki mamaki fiyye da tunaninki yana gama fadar hk yasa hannu ya dauki Ana ya rungumeta akafadarsa ya juya fuuuuuuuuu .
yana zuwa kasa ya ajiyeta a gefen ummi tare da yiwa ummi sallama ya wuce office ..

*****
Da rana byn zeenat ta gama baccinta ta tashi tayi wanka tasa sabon dinkinta wanda laraba ta karbo mata tasha kwalliya bazaka taɓa tunanin akwai abinda ke damun zuciyarta ba
ko tana tattare da damuwa ba  sbd hadiye damuwarta da take
tayi fess daita simple make up tayi shima abinda yasa tayi dan sbd  ya rigada ya zame mata jiki ne yin kwalliyar if not bazatayi ba.
ta sauko parlour 'n kasa hannuta rike da pos  ta ciro kudi tabawa laraba kudin cefane tare da bata instruction din abinda zata tsiyo mata sbd  sakwara take son ci yau nan dana laraba ta shirya ta fita cefano musu kayan sakwara da miyar egusi hade da busasshen kifi.

tana zaune  Wayarta ta dameta da karar shigowar massage's tana daukar wayar ta soma cin Karo da zafaffan sakwanin mijinta wanda gabadaya sakwanin ban hkr ne da yadda yake sonta cikin harshen turanci kanta yayi  mugun daurewa ta sake tsurawa wayar ido tana kallon text messages dinsa tabbas sakonnin mijinta ne take gani daki daki take sake Bin text din tana karantawa sororo tayi taji tmkr a mafarki take ganin kalaman ban hakurinsa  gareta
tmbyr ta anan yaushe Ne deeni ya soma sonta irin hk?

Km abin mamaki ta yaya zuciyarsa ta Yi saurin saukowa domin tasan da fushi ya bar gidan wanda aduk lokacin da yayi irin wannan fushi hk yana kwana da kwanaki bai sauko ba wani lokacin ma sai itace zatayi ta binshi da rarrashi sannan zai Hakura .
sosai taji dadin hkn aranta sai dai km abun bai wani birgeta ba ko dadata da kasa ba.
yayinda  a bayyane km tace" ka hadu da wahala deeni domin wlh kai ma sai kasan kimata da darajata ta diya Mace sannan ko zankoma gidanka ahankali  ta dinga bin sakonin nashi tana gogewa daya byn daya Cikin farinciki ta wuni ranar zuciyarta fess cike da tsantsar soyayyar mijinta ita kanta tasan bazata taba iya rayuwa babu shi ba
shine duniyarta, rayuwarta,
duniyar  da babu deeni cikinta, rayuwace me tattare da damuwa da kuncin rayuwa wanda daga karshe tasan zuciyarta bugawa zatayi ta mutu .

Zaune a office dinsa yake amman gabadaya zuciyarsa cike take tap da tunanin zeenat da mamakinta iya gaskiyarta fa yake hangowa acikin kwayar idanunta tabbas zeenat ta zabi rabuwa dashi ta aure waninsa, zeenat me sonshi da nuna masa kulawa ada ta daina sonshi zeenat wacce ki fargaba da tsoron gaya masa mgn ada Amman yanzu gabadaya babu wannan tsoron shi kuwa ko sama da kasa zata hade ba zai taba sakinta ba... Jikinsa a sanyaye ya samu ya dinga cike file files din dake zube bisa makaken table din dake zagaye dashi yayinda lokaci zuwa lokaci yana dago idanunshi yana kallon agogon dake manne a jikin bangon office din, wani time km ya dauki wayar ya tura mata text ahaka dai har ya samu ya kammala tarin ayyukan  dake gabansa daga office kai tsaye gidansu nablah ya nufa...


A k'ofar gidan su Nablah yayi parking din hadaddiyar motarsa Dan bai bari escort dinsa sun biyo shi ba ya fito, cikin takun nan nasa me cike da daukar hankali waige waige ya fara yi yana neman yaran da zai aika zuwa cikin gidansu nablah, Abba k'anin Nablah ya ga ya fito da gudu daga cikin gidan yana tsale ..
kiransa Deeni yayi, Abba yazo da sauri yana gaida deeni fuskarsa dauke da murmushi Deeni ya kalle shi yace yauwa Abba" Baba na ciki?
  "Eh Abba yace, " OK yi min sallama da shi, juyawa Abba yayi, ya koma cikin gidan tare  Abba da Baban Nablah suka fito,.
" har falo Baba yayiwa Deeni iso, yana ce masa " kaima ai d'an gida ne yanzu ka daina tsayawa daga waje,inda kazo, murmushi Deeni yayi hade da durkusawa har k'asa ya gaida iyayen Nablah, fita Baba yayi da kansa ya kira masa Nablah, da sallama ta shigo d'akin ta nemi waje ta zauna nesa dashi kadan tana   me had'e fuskarta tamau  , ido ya k'ura mata yana kallonta tayi masa kyau sosai tayi fresh da ita da gani hankalinta a kwance yake bata da wata damuwa.

AUREN SIRRI Where stories live. Discover now