AUREN SIRRI EPISODE 99

182 10 0
                                    

AUREN SIRRI
      💖💖💖
💗💗💗💗💗


AYSHA A BAGUDO

     

Page 99

Cikin wannan halin da take  ciki  na soyayyar ya'yanta deeni ya kuma  shigowa d'akin fasukarsa d'auke da wani irin  murmushin farinciki ta koina ka kalleshi kasan yana 'cikin tsantsar farinciki da murna samun wayan nan kyawawan bbys din masu matukar kyawun da d'aukar hankali .

Ahankali ya karasa inda take zaune rungume da ya'yanta duka
ya tsura mata rikitattun idanunshi yana kallonta  da jin Wani irin mugun sonta da yaran yana taso masa ,Yanayin daya ganta ciki  yasashi shan jinin jikinshi
zama yayi kusa daita sosai  har cinyoyinsu Na gugar juna ya amshi ta mace Daga hannuta  ya d'aurata saman cinyarsa yana kallonta yana kallon fuskarta nablah da yaga gabad'aya ta canza ta dawo wata iri .

muryarsa a sanyaye ya Kira sunanta "nabeelah ....bata amsa masa  ba sai ma juyo da tayi inda yake zaune  tayi masa kallon second  2 kana ta d'auke idanunta Daga kanshi ta maidasu  kan yaranta dake cinyarta  ,sautin muryarsa taji a matukar sanyaye fiyye da farkon shigowarsa d'akin  .." nablah kinga kyautar da Allah Yayi mana ko?

A dakike ta amsa masa da "uhmmmm"
yayi murmushi" gsky kin iya haihuwa arayuwata ban ta'ba ganin macce data iya haihuwa  kmr ki ba ,Gsky kinyi k'ok'ari sosai ....
nan ma  tayi masa banza ta sharesa gabadaya ma  taki cewa dashi  komai ,"yanzu me kike bukata akawo miki ?
muryarta can kasa kasa tace" babu tare da kamo lip's dinta Na kasa tana cizawa ahankali ahankali tana Dan jijjiga kafarta daya akasa .

Gabad'aya deeni ya rud'e ya rasa abinda ke masa dadi tunda ta haihu ya rasa gane kanta sai wani shashsharesa take tana basar dashi  da ciccin magani wanda ya rasa dalilinta nayin hk .
runtse rikitattun idanunshi Yayi sosai
ciki Mutuwar jiki  sakamakon tuno da kyawawan baby's dinsu data haifar masa masu tsananin kamadashi  km gashi  yana tare dasu ahalin yanzu.
"To  me zai dameshi da duk abinda zatayi arayuwa ta gama masa komai tunda tabashi abinda yafi so da kauna a rayuwarsa ta duniya ,sumbatar bby  girl din  yayi  yana jin wata irin natsuwa ta daban tana ratsa kowane shashi Na gangar jikinshi sosai yake son yaransa Amman yafi jin kaunar mace fiyye da sauran acikin zuciyarsa  ,
Jikinasa cike da rauni soyayyarta  ya kamo tafin hannuta  'cikin nashi  ya soma murzawa ahankali ahankali 'hade  da  shaukin kaunarta yace "meke damunki nablah naga duk kinyi wani iri hk ?

"Ki sanar da deeni  abinda ke damunki banason ganinki 'cikin   damuwa da tashin hankalin  please ...
yanzu kin zama wata bangare Na rayuwata da farincikina gabad'aya sbd wannan kyawawan  bbys din da kika bani ..

Kimin abinda wata matar  ta kasa jura ta min arayuwa  ,
Kin bani kyautarsu alokacin da nafi bukata , akan wayan nan yaran babu abinda bazan iya miki Shi ba , matukar Bai shafi addanina ba .

"ban ji  dadin yadda na ganki  yanzu ba
idan akwai wani abu dake damun zuciyarki ki fito ki sanar min,
ni kuma nayi miki alkwarin zan yi miki maganinsa kowani iri ne .. ya karasa fad'ar hk yana matse laulausar tafin hannunta 'cikin nashi yana jin yadda sonta ke fizgar zuciyarsa  ..

So take tayi magana Amman maganar taki fitowa sakamakon wani yanayi data tsinci kanta ciki ,ita fa bbu abinda ke damunta a halin yanzu wanda ya wuce son rabata da ya'ya da za'a yi.

ta lumshe shanyayyun idanunta kana ta bud'esu ahankali ta zubesu cikin nasa still ta kasa tabuka komai shima lumshe rikitattun idanunshi Yayi sannan yace "Ok kin gama ganin yaran zan maidasu kasa sbd masu zuwa ganin bby ..
take zuciyarta ta buga da matsanancin karfi har sai data taji zubowar  gudan jini Daga kasanta , afrigice ta zare hannuta cikin nashi tana kallonsa  a tsorace bakinta da alamun son yin mgn .
kanshi ya girgiza mata yana k'ok'arin mikewa tsaye .

AUREN SIRRI Where stories live. Discover now