AUREN SIRRI
AYSHA A BAGUDO
Page 89
A hankali ya yunkura zai tashi daita ajikinshi, tayi saurin Kai duka hannuwanta ta zagaye cikinsa ,cikin raunanniyyar muryarta tace" please deeni ..........
ka zauna kada ka fama ciwonka man ....dole Tasa ya koma ya zauna ba dan yaso ba.
sai dan gudun abinda zai sameta idan ya matsa lallai sai ya tashi da karfi kmr yadda yayi Niyya ...yadda take kwance ajikinshi yasa ya k'ara jin gabad'aya notikan dake d'aure a jikinsa suna neman kwance masa da son fallasa abinda ke boye cikin zuciyarsa wanda hakan zai iya jawo afkuwar komai atsakaninsu batare daya shiryawa yin hkn ba .kamo lip's dinsa na kasa yayi ya soma ciccizawa ahankali ahankali.
wani irin zazzafan shaukinta yake sake jin yana bin jini da 'bargon jikinsa yana bawa kowane part Na ruhinsa sako na musamman ..
ya runtsa rikitattun idanunshi sanda yaji ta zare hannuwanta ajikinsa tana sakin numafashi da kyar tamkar me cutar asma .
Idanunsa ya tsura mata yana kallon cikin kwayar idanunta dake walanniya da aikin jujjuyawa, sosai ya tsura mata idanushi kawai Yana aikin kallonta,haka kawai ya tsinci kanshi da kasa ce mata komai sai ma Kai hannuwanshi da Yayi ya kamota ya mannota da kirjinsa yana sakin naunauyen ajiyar zuciya ,kana ya kai bakinsa daidai shashin wuyanta yana shinshinawa da sumbatar duk inda bakinsa yaci karo dashi , had'e da goggomata gashin dake kwance a fuskarsa .
jin Yayi saitin kunneta yasa ta dago hannuta cikin mutuwar jiki a dan tsorace ta dora akan bakinsa saboda bata shirya jin abinda yake son fad'a mata ba
,cikin sarkewar muryarta tace" please kayi hakuri man ,saboda Gani irin kallon da yake antayo mata ...
lumshe rikitattun idanunshi Yayi yana shakar kamshin tafin hannunta mai taushi akan bakinsa ,ta kula da yadda yake yi din kuma tasan bakaramin aikinsa bane ya canza salon yanayinsa zuwa zafafan wasannisa masu hautsina mata lissafi ,
dan hk tayi sauri zame hannuta ahankali zata tashi da sauri Ya rukunkumeta ajikinsa tare da shafo wasu wuraren a sansar ajikinta kana ya dire hannuwanshi duka akan tudun nonuwanta da suke cike bammmmmm dasu abin sha'awa da bukatar kowani cikakken namiji, ahankali yake shafo saman nonuwanta yana lumshe idanunshi , ta dan saki kara 'cikin sanyi muryata mai dadi tare da cewa .
"Wayyo NASU...RUL..DEENI zan suuuume ..me .. maka fa ..."
Har cikin kasan zuciyarsa yaji maganarta ta shigeshi ya rinka jin wani irin abu me kama da sonta yana kara fizgar zuciyarsa gareta ,cike da kuzari
ya sake rukunkumeta sosai ajikinshi yana mamakin wannan abu da yake d'awainiyya dashi akowani lokaci koda kuwa baya tare daita .cikin natsuwa ya shiga mamakin yadda Sam bata shakkarsa , kalli yadda ta ambaci sunansa yanzu kai tsaye batare da wani tsoro ko fargaba ba ,Wanda ba duk mutane ke iya kiransa da sunan Kai tsaye ba ......
Ita kuwa nablah tsoro ne ya kamata domin ita kanta ji tayi kawai sunan nashi ya fito daga bakinta batare data shiriyawa hakan ba ,yawo ya shigayi da hannushi a sansar jikinta batare da Yayi la'akari da irin raunin dake kafarsa ba , rasa yadda zatayi dashi ne yasa ta soma mutsun mutsun ajikinshi tare da ce masa tana jin yunwa ,tasan yanzu zai kyaleta.
Hakan ce kuwa ta faru dan sausauta rungumarta Yayi yana sakin numafashi da kyar, ya juyo da fuskarta daidai tashi suna fuskantar junan, yayinda kowanensu Na shaqar numfashin juna , atare suka lumshe idanuwansu take kuma zuciyoyinsu suka shiga bugawa atare muryarsa cike da shaukinta.
yace a" Ina kika San sunana hk ?
Tayi shr tana tunanin inda taji sunan yayinda gabadaya zuciyarta ta cika da frigici da tsoron tambayar da Yayi mata idanunta suka soma ciccikowa da ruwan Hawaye.
Muryarsa a kasalance yace" ba kuka nace ki min ba amsa kawai zaki bani Ina kika San complete name di na ?
Muryarta cike da in ..inna tace" uhm ammm daman ajikin hotonka dake manne a d'akin sama na gani .
Ya lumshe rikitattun idanunshi yana cigaba da yawo da hannuwanshi ajikinta yace "Kinsa kuwa kin fi kowa iya sarrafa harshenki gurin iya Kiran sunana..... ya karasa fad'ar haka yana bude rikitattun idanunsa masu kashe Mata sansar jiki.
Ta tsurawa kwayar idanushi ,idanunta itama kawai Tana kallon yadda Ya dawo mata tamkar wani karamin yaron goye sannan ta bude bakinta da kyar .
"kowa fa kace ?
Ya kashe mata idonsa daya alamun haka abun yake "abinda ke sake narka da zuciyar nablah kennan har ta manta da Wanda take tare ,ta dinga jinsa ajikinta tamkar shi din nata ne na har abada.
Yayinda maganarsa Ta sata jin kamar ana mata wanka da ruwan sanyi ne ,"har da ummi da aunty ze...cak ta katse harshenta gurin k'arasa maganar , take kuma gabanta ya yanke ya shiga dukan uku uku sakamakon tunowa da zeenat din da tayi .
Ta tuna ashe fa deeni da take tare dashi ahalin yanzu mijin wata ne wanda tafi so da kauna fiyye da komai dake cikin rayuwar duniyar nan ,shine take tare dashi har take rayuwa dashi tamkar wani mijinta .
"Ya kika yi shiru yarinya
ki karasa Kiran sunan matata man ?
Ta runtse idanunta Tana jin yadda bugun zuciyarta ke sake k'aruwa kirjinta Na mata wani irin zafi da rad'ad'i Wanda ta rasa name ne ?
"Ok bazaki iya karasawa ba ,saboda kin fara son mijinta ko ?
Ta bude shanyayyun idanunta da suka gama canzawa tsabar tashin hankalin data tsinci kanta ciki ta watsa su 'cikin kwayar idanunshi kana ta girgirza masa kai wasu zafafan hawaye suka samu nasarar biyo kuncinta ,Ya dan yi murmushin gefen baki yana me kamo lips dinsa na kasa ya cigaba da ciccizawa ahankali, sannan ya sauke ajiyar zuciya da karfi.
"Kina kishin matata ko nablah ?
Unexpected taji ya jiho mata tambayar tun bata gama jimamin wancen ba ..
Muryarta a matukar sanyaye tace "a'a wallhi bana kishi matarka sannan bana jin sonka cikin zuciyata Ni kaina bansan abinda ya sani kasa karasa Kiran sunan nata ba , ya girgirza Kanshi kawai domin sanin dalilin da yayi ,kana yace "zaki sani ne inda lokacin haka Yayi .
"dan kin rigada kin makaro yarinya tuni soyayyata ta gama da zuciyarki tsab "kin fad'a cikin tafkin kogin son mijinta kin nutse kiris ya rage zuciyarki ta mace akan shaukin soyayyata ....
Ya fad'i haka yana me sakar mata killing smile dinsa me sake kashe Mata ilahirin jikinta akanshi.
" Allah Ya tsareni da macewa akan sonka deeni ta fadi hk muryarta cike da kuka tana mikewa tsaye ahankali yayinda wasu Hawayen takaicin mgnrsa suka sake biyowa kan kuncinta
" kalli yaddda kike kuka nablah akan soyayyata da kishin matata Amman kice a'a .
YOU ARE READING
AUREN SIRRI
FantasyMATARSA CE TAKE ZUBAR DA CIKI BISA WANI DALILI NATA WANDA SANADIYAR HAKA SURUKARTA TAYIWA MIJIN DATA FI QAUNA FIYYE DA KOMAI A DUNIYA AUREN SIRRI DA ME AIKINTA BATARE DA SANINRA BA..