AUREN SIRRI
AYSHA A BAGUDO
Page 71
Karfe takwas daidai nablah ta sake fitowa main parlour din domin xuba musu abinci suna zaune su dukkansu , har deeni suna hira
ta karaso har dining area .
jikinta a sanyaye ta soma xubawa ummi da zeenat har ma da safeena Abinci Amman taki xubawa deeni dake zaune yana chatting a wayarsa ..asalima ko kallon inda yake zaune batayi ba ballanantana tasan da zamansa .
Shima bai wani damu da ganin yadda ta shareeshi ba ,Sai ma gyara zamansa da yayi sosai yana son yaga iya gudun ruwanta.
ta gama duk wani abinda take ta juya ahankali da niyar barin parlour tayi taku daya zuwa biyu taji an fincikota ta baya da karfi ,
ahankali ta juyo a sanyaye dan ganin ko waye ya rikota hk , aiko juyowarta keda wuya
taji saukar mari tasssss akan fuskarta .
zeenat ce da wannan aiki nablah tasa hannuta ta dafe kuncinta daidai inda taji saukar marin tare da tsare zeenat din da shanyayun idanunta tana kallonta dasu...
take Hawaye suka shiga sintiri a kuncinta sharrrrrrr tamkar an bude pompo ... Ba nablah da,aka mara ba hatta ummi da safeena Sai da saukar marin Yasa suka ji shock jikinsu ......deeni dake hakimce agurin ko gezo baiyi ba ,sai ma very gud da yace a zuciyarsa ... hankalinsa kwance ya cigaba da operating din phone dinsa cike da jin dadin abinda Zeenat tayi mata..
"ke.... ashe Yar iskace ban sani ba?
,mijin nawa ne yazama abun wulakantawa da bazantarwa a gurinki tsabar kin rainani ....
" dan ubanki shi bai isa ki zuba masa abincin bane ko me kike nufi?
Ta karasa mgnrta tana mai sake ciro hannunta zata kara mata wani marin... ummi tadakar daita " Kull karki sake ki kuma marin Yar mutane .
"Aiki tazo yi fa ba bauta ba ,Wannan Ai wulakanci ne da tsagwaron rainin wayo zalla ?
"Me ma yayi zafi daya kai har da duka?
da bata zuba masa abinci ba ke aikin me kike ?
"kinji min rainin arziki kawai Naga mijinki ne bana ba.. .. ummi ta kasa karasa maganar illa sausauta muryarta datayi
"A'a Zeenat nifa banason irin Haka , abinda kasan idan an maka baza kaji dadi ba to karka soma yiwa wani.
ran zeenat ya kai kololuwar gurin 'baci har wani duhu duhu take Gani tsabar takaicin abinda ummi tayi mata a gaban mai aikinta..
dan hk cike da fushi tace "wlh ummi duk ke kike daurewa yarinyar nan gidin yin iskancin data gama ,
Tare da yiwa mutane kallon Gani Gani da rainin hankali, wlh tun wuri idan tasan ba zata iya yin aiki dani ba ,takama gabanta .
"inda km ta cigaba da yin irin wad'an nan iskancin wallahil azim zan gyara mata zama acikin gidan dan bazan d'auki rainin hankali ba ,Tana gama fadar hk ta juya fuuuuuu ta soma kokari barin parlour .
Nablah dake tsaye har lokacin jikinta Banda rawa rawa bbu abinda yake ,yayinda Hawaye dake idanunta ke cigaba da silalowa Cike da tausayin kanta tasa byn hannuta tana goge Hawayen wasu Na sake zubowa.ummi da ranta ya gama baci matukar ,tace" yi hakuri kijin nablah "
nablah ta girgirza mata kanta kawai batare da ta amsa ba .
"Zo ki zauna kici abinci inji cewar ummi da kyar nablah ke daga kafafunta da suka gama sagewa tsabar takaici da tashin hankali da take ciki , safeena ta Mike ahankali tare da kamo hannunta 'cikin nata tana bata hakuri ,ta zaunar daita tare da turo mata plate din abincinta data soma ci gabanta tana sake bata baki ,ummi ma hakuri tai ta bata.duk wannan abin da suke mata baya gabanta hk km bai wani birgeta ba ,
Dan gabadaya Hankalinta baya jikinta .. tunaninta ya tattara ne akan yadda zata bar gidan ta hutawa rayuwata.
"akan wani dalilin zata zauna a maidaita tamkar baiwar Ai talauci ba hauka bane kuma ba'a akanta aka soma zuwa aikatau ba ,duk yadda safeena tayi daita akan taci abinci kasawa ci tayi, Banda bakinciki bbu abinda ke dawainiyya da zuciyarta ."Ta ya'ya mijinta Na mata rainin wayo ita kuma ta dinga wulakanta ta..sbd me...Ta tmbyi zuciyata ..?
take zuciyarta ta bata amsa da ,sbd ke din talaka ce ....
Zeenat na barin gurin Shima deeni ya Mike ahankali yana kakkabe jikinsa ranshi watse da marin da zeenat tayi mata , murna fal cikinsa yayi hanyar step ...
Ko rabi bai yi ba
ummi ta kira sunanshi "deeni ..."
Ya dan tsaya tare da juyowa yana duban ummi "kaje dakina ganin nan zuwa yanzu .
Deeni zaune a parlour ummi akan doguwar kujera ,yayinda ummi ke zaune a gefeshi ,tace" tunda ka dawo daga gidansu yarinyar nan nablah banji kace dani komai ba?
idan kasan da cewar bazaka iya bi zabina bane ka fito kasanar min , Ba wai ka dinga min yawo da hankali ba kmr wata abokiyar wasanka..deeni ya marairaice murya "haba first love meyye kawo wannan mgnr ?
Wlh naje gidan nasu kuma har na gana da mahaifinta kuma har angama komai .
"Bangane angama komai ba ummi ta tmby ?
ya juyo sosai yana fuskantar ummi da kyau sannan ya soma mata bayanin duk yadda sukayi da mahaifin nablah har zuwa inda aka daura musu aure tare da fito da wayarsa yana Nuna mata video dayasa sule yayi lokacin da'ake daurin auren ,
Yana gama nunawa ummi ya kira number sule tare da saka wayar a handsfree ,muryar sule direba ta bayyana raudau ,shima dai Karin bayani yayi mata akan yadda daurin auren ya kasance sannan deeni yayi hanging din kiran .
ummi nagama jin yadda komai ya tafi 'cikin tsari Yasa ta saki ranta sosai ba kamar farkon shigowarta dakin ba tace" yauwa Dan albarka Haka nake son ji alhamdulilllahi ,Da har Na dauka ko bazaka bi zabina bane ?
Cikin sarkewar murya yace" a koda yaushe banida zabin daya wuce na ummina duk abinda kike so shi nima nake so akan wannan baza mu taba samun saban ra'ayin ba. farincikina
shine na kasace mai biyayya a gareki,
dan Haka banida yadda zanyi , auren yarinyar shine mafuta kawai atare dani..
Ya karasa mgnr yana yin kasa da muryarsa " Ni km hk tawa kaddarar auren yake zuwa min, zuciya ba zata ta'ba samun zabinta ba .
Tsananin tausayi furuncinsa ne ya kama ummi Amman kuma bata jin zata iya canza ra,ayinta akan qudirinta na kawo farinciki a gidan diyarta ba .
Parlour ya dauki shr koina yayi tsit tamkar babu masu numfashi aciki, baka jin motsin komai Sai Na sautin TV,
ummi ta nufasawa tare da kokari kawo karshen shirun nasu ta hanyar cewa" Allah yayi maka albarka deeni ,duk abinda kake nema a duniya da lahira Allah ya baka, biyayyar da kake min kaima Allah yabaka ya'ya shiryayyu da zasu maka fiyye da hakan .
"Ameen first love ya fada tare da Mikewa kan kujera ya daura kansa akan cinyarta tamkar dai yadda kananun yara sukeyi , tare da lumshe rikitattun idanunshi .
Ahankali ummu ta kai hannuta kan sumar kanshi dake kwance luf..luf Sai sheki suke da daukar hankali 'cikin tautausar lafazi mai tsanyi ta Kira sunanshi..."NASURULDENI ....
kwata kwata bashi da niyyar amsawa Amman yadda umminsa ta kira complete name dinshi ne yasa dole ya amsa mata da " Na,am first love a kasalance domin yasan duk abinda yasa umminsa kiran ainihin sunan haka abu ne mai mahimmanci ,
dan Haka ya tattara duka hankalinsa gareta .
"Banason abin nan ya dau lokaci sbd da Haka ka hanzarta raba masu kwana kmr yadda addinin Muslinci yatanadar, kwana biyu biyu ko day day ,tunda ummi ta soma mgnr raba kwana numfashinsa ya nemi daukewa .. ko motsin kirki bai sake yi ba har ummi ta dasa aya.
idanushi a lumshe suke ,yayinda zuciyarsa ke mishi radadi da suya tare da takaicin mgnr ummi dan Haka muryarsa a dan zafafe yace" kina nufi dakinta zan dinga zuwa ?
Itama ummi a zafafe tace "Kwarai kuwa ko bazaka iya bane?
Ganin yadda ummi tayi ne Yasa shi cewa" Ni Na isa nace miki bazan iya zuwa ba, Sai dai wlh Ni kunya nakeji ya karasa fadar Haka cike da shagwaba tare da yatsina fuska.
Ummi ta cigaba da shafa sumar kanshi ahankali daga karshe tace "daurewa zakayi kaje gareta ba dan ta isaba Sai dan bukatar mu ,
Deeni dake kwance ya sake yatsina fuska alamun Yashiga sarkarkiyya, da kyar ya iya bude baki yace" shikennan first love zan ware lokaci da zanje gareta ,
Ummi tace "wani irin zaka ware lokaci zuwa gareta ?
"Kawai yau zuwa gobe ya Isa ka tsara komai dan ba muda wani ishashen lokaci 'batawa .
A kidime deeni ya Mike zaune yace "haba haba first love karki min hk man wani irin yau zuwa gobe gsky ni gobe yayi min wuri dan ban shirya zuwa gareta a gobe gobe nan ba .,Amman I promise next week inshallahu .
"Nest week Yayi nisa deeni kayi kokari kaje gareta zuwa jibi ,
Tamkar mai shirin rushewa da kuka yace" uhmmmm alamun yaji kawai ummi tayi murmushi jin dadi hade shafa gefen fuskarshi da tafin hannuta" duk kabi ka wani rikice tamkar mai jin tsoron yarinyar .
deeni ya zaro idanun waje yana wa ummi wani irin kallon" shi din ne yake jin tsoron yarinyar da loma daya zaiyi ya gama daita.
" haba first love .. yau kuma nine matsoraci? yana may Nuna kansa da yatsansa sannan ya cigaba tsorona ma ya rasa inda zai kare Sai akan mace ...mace ma housemaid dina..
ummi tayi saurin d'aga masa hannuta "ok ya isa to Ai kai din ne naga duk kayi wani irin tamkar kana jin tsoronta ,
Alhalin nina san yarona jarumin jarumai ne..
sadaukin nmj abin sha, awar kowace macce.
",kaga yarinyar nan bata da wani aibu uwa uba tana da kyau sosai ,
idan Allah Yasa ma akaci sa'a babys din duk sukayo kama daita
Kaga zamu samu kyawawan bbys daga gareta.
duk maganganun ummi babu wanda yaji yafi bata masa rai kmr wai yana jin tsoron yarinyar da wai tana da kyau,
dan Haka ranshi a bace yace "Ni first love ki daina wani cemin tana da kyau kyawunta Na banza ... tunda nasan ko kama kafar matata batayi ba a kyau ballanantana Ni .
"banason ma ya,yana su wani yi kama daita zanje dai gareta ne kawai sbd cika ummirniki ba dan wani kyawunta ko me ko me....
kawai ya Mike tsaye dan ya raba kanshi da sake jin zance yarinyar da ummi ta saka shi gaba dashi ,
dan zamansa agurin zai iya hadasawa zuciyarsa kamuwa da wani ciwo mai tsanani .
Zuciyarsa cike da Haushi ya nufi dakinsa ya murda handle yashiga bedroom tare da fadawa kan makeken royal bed dinshi ya jan tsaki yayinda bakinsa ke fidda wani irin iska mai zafi, hannuwanshi duka ya daura yayi pillow dashi Tare da kurawa celling daki ido tamkar may karanta wani abu..
bbu abinda yake Ban da tunanin yadda zuwansa gurin yarinyar zai kasance tsawon lokaci ya dauka kwance yana kallon celling dakin kafin daga baya ya sauke naunauyen ajiye zuciya may karfi gaske ..
ya fara zance zuci ta Ina zan fara ?
A zahirance zanje mata ko badinance ?
Zuciyarsa ta bashi amsa da " kaje mata kawai a Deeninka sak ....
" a,a kada kayi Haka ka tsaya dai ka natsu tukun kasan ta Inda ya dace kaje mata..
ya sake furzar da iska tare da jan tsaki ko ma a ya'ya naje mata dolenta ta saurareni km Hakan ba zai hanani cin ubanta ba da wannan sabon iskanci data tsiro min dashi ..
har kmr Ni ya Nuna kanshi da dan yatsansa "wata diya macce zatace Ina damun rayuwarta ina shiga lamarinta ,
Ni deeni da kaina ya girgirza kanshi kawai yana sake jin haushinta ...
*******
Ranar Wednesday ya kama rana da ummi ta umarce shi da zuwa gurin yarinya.
dan Haka tun a safeyar ranar ya gama shurinsa tsab ta yadda zai isa Gareta a saukake .
Zaune yake a dakinsa ya tasa CCTV camera dinsa ...
MMN SUDAIS CE
YOU ARE READING
AUREN SIRRI
FantasyMATARSA CE TAKE ZUBAR DA CIKI BISA WANI DALILI NATA WANDA SANADIYAR HAKA SURUKARTA TAYIWA MIJIN DATA FI QAUNA FIYYE DA KOMAI A DUNIYA AUREN SIRRI DA ME AIKINTA BATARE DA SANINRA BA..