AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDO
Page 88
Rayuwar deeni gabadaya ta canza 'cikin 'Yan kwanakin da basu wace asharin da wani abu ba
,rabon shi daya samu kanshi 'cikin natsuwa da farinciki irin hk a zuciyarsa har ya manta .matsuwa Yayi yaga yadda cikin jikin nablah zai bayyana ya tona asirin kansa domin hkn shine cikar burinsa, sbd shi ahalin yanzu idan akwai abinda yafi so da kauna bai wuce 'cikin dake jikinta ba ,wato burin rayuwarsa .....
Gama wayarsa kennan da matarsa ya Mike tsaye zuwa dakin da nablah take .
Jingine take akan makeken gadonsa yayinda Wani irin zazzafan zazzabi me zafi da tsuma gangar jiki ya samu nasarar cafketa sakamakon ruwan saman da aka kwana da yini ana shekawa a garin Lagos wanda ya had'e mata da yanayin gurin na sanyi gidan glass.
" cikin rawar jiki ta Kai hannuta ta dan janyo tautausar blanket dinsa dake nade a gefe daya me cike dadadden kamshi turarensa Wanda ya cika mata hanci,da koina Yayi mata Kane Kane acikin zuciyarta, ta lullube sansar jikinta dashi .
wani irin numfashin take fitarwa ahankali me gyaraye da zafin zazzabi ,yayinda ta cikin blanket din ta kudindine jikinta guri daya, sosai take rawar sanyi , hakoranta har karkarwa suke da junansu, har zuwa sanda deeni ya shigo dakin ya tadda ita 'cikin wannan halin.Kai tsaye gurinta ya nufa da sauri ya hayo gadon hade da zamo da blancket din data rufa jikinta dash.
Yayi shiru tare da tsura mata rikitattun idanunshi kawai yana kallon yanayin datake ciki .
da kyar ta samu tasanya hannuta ta fexgo bargon dayake rike dashi ta sake maidashi jikinta tana cigaba rawar sanyi Kana ta kawar da kanta.
'cikin sarkewar muryarya tace masa" Ina wuni... batare da ya amsa ba Ya cigaba da kallonta kawai dan ba gaisuwarta yafi bukata ba ...
ganin yanayinta yasa shi
cewa baki da lfy ne ?Shr tayi masa itama taki ce masa komai tamkar yadda Yayi mata sannan taki dago idanunta .
ya motso sosai kusa daita har yana jin hucin zafin zazzabi jikinta, gabadaya tana jin yadda ya gigice ya rude ajikinta Amman taki dago idanunta ta dubi yanayinsa ..
yace" talk to me now please what's wrong with you ?
Wasu zafafan hawaye suka cicciko idanuta kawai ta tsinci kanta da gyada masa kanta.
Alamun bada da lfy ..Take yaji zuciyarsa tayi wani irin matsanancin bugawa da karfi har ya samu kanshi da dafe tsaitin zuciyarsa da hannuwanshi duka yana cigaba da kallonta ,
Yayinda gefe daya km ya daura alhakin ciwon nata akanshi Domin da baije ya bata sama da awanni yana hira da zeenat dinsa ba
, may be da yanzu bbu wani abinda zai sameta .runtse rikitattun idanunshi Yayi sosai yana jin zafi sosai har 'cikin zuciyarsa , tare da saukowa Daga kan gadon batare da ya sake ce mata komai ba .
" jikinsa a sanyaye ya fitce daga dakin zuciyarsa cike da tsananin tausanyinta Wanda yanzu ya zamemasa jiki .
Fitar shi da kmr minti shabiyar ya sake shigowa dakin hannushi rike da Whit lailon da ruwan roba.
ya sake hawowa kan bed din ya km yaye bargon Wanda zuwa lokacin tuni ta kwanta ya tada ita zaune still jikinta rawar sanyi yake .
ya ballo magani da ruwa yayi mata alamun ta bude bakinta Amman taki sai miko masa tafin hannunta tayi ,ya saka mata maganin tare da jan yantsun hannuta sai da taji wani iri ajikinta sannan ta saka maganin abakinta Tasha ruwa.
tana kokari komawa ta kwanta yayi saurin tarota jikinshi , muryarta Na rawa tace "please...ka barni kar ka takura min dan Allah ...
"ki dan tsaya man maganin ya dan narke so that sai ki kwanta
ta shiga girgirza masa kanta tana kuka da son kwatar kanta Daga gareshi , rasa yadda zatayi dashi ne
yasa dole ta hakura ta kwanta lamo ajikinshi ba dan taso ba sai dan yafi karfinta gashi ita bata da wani kuzari ajikinta ..
YOU ARE READING
AUREN SIRRI
FantasyMATARSA CE TAKE ZUBAR DA CIKI BISA WANI DALILI NATA WANDA SANADIYAR HAKA SURUKARTA TAYIWA MIJIN DATA FI QAUNA FIYYE DA KOMAI A DUNIYA AUREN SIRRI DA ME AIKINTA BATARE DA SANINRA BA..