AUREN SIRRI
Page 69
Kai tsaye dakinsa ya nufa ya fada kan royal bed dinshi ya kwanta flat yana fidda numfashi ahankali.
yayinda kyawawan idanunshi suka gama rikidewa tamkar garwashi tsabar tashin hankali dayake ciki.
" why ...why ummi?
why did you want's to do this to me?
,meyasa zakiyi min Haka ummi ?
Meyasa kike kokarin son cusawa zuciyarta abinda bata so ?
,bana son yarinyar nan , Bana kaunar ganinta asalima Na tsani kusancina daita domin hakan na jifani 'cikin tsananin tunani da rasa natsuwata.
" bazan iya bijere miki ba ummi ,to meyasa kike so ki tursasani yin AUREN SIRRI da kaskantacciya macce?
tsawon lokaci ya dauka yana kwance idanunshi na kallon celing dakin gabadaya tunaninsa a halin yanzu ya ta,allaka ne akan abinda ummi take son ya aikata .
,yana son umminsa bayason abinda zai disashe farincikinta ballanantana har yakai shi Ga bijirewa
umarnita.bacin ran umminsa ,babban tashin hankalisa ne,a gareshi bancin haka da Babu abinda zai kaishi auran wannan yarinyar may idanuwa tamkar Na mage .
yaja tsaki a ranshi Dan duk wannan zance dayake yi yana yinsa ne a zuci .
ahankali ya runtse rikitattun idanunshi banda yana jin baccibacci, Sai Dan yana bukatar maido da natsuwatsa dake kokarin barin gangar jikinsa .
Bangaren nablah kuwa gabadaya duk wata surar dake jikinta ta sauya , ta murje ta sake yin kyau daita Sai dai walwalarta da kuzarinta sun ragu.
sakamakon matsi da takurar da Zeenat ke yawan yi mata, Wanda ita kanta tarasa dalilin hakan .
km kwata kwata bata dauki takurar da Zeenat din kemata amatsayin wani aibu ba .
Baya ga tunaninta Haka wasu daga 'cikin masu arziki da manyan masu hannu da shuni sukeyiwa marasa shi km marasa galihu irinta .
Duk da yawan takurar da Zeenat din ke mata hakan bai hanata samun farinciki da walwala daga gurinsu laraba da safeena ba . Dan haka ta tattara takurarta ta watsar a gefe tacigaba da abinda yakawota iyakarta daita aiki Wanda tasan dolenta ne Tayi shi Dan abinda tazo yi kennan .
Ranar Saturday ' nablah na zaune ita da safeena a main parlour din gidan sanye take 'cikin doguwar rigar material may ratsin pink and popul yayinda jikinta ke rufe da dan karamin hijab kmr koda yaushe.
babu kwaliyar komai a fuskarta kasancewar ba ma,aboyaciyar son kwalliya bace da kalekalen zamani, sai Dan Whit lip's din data shafawa lebenta.
,rashin kwalliyarta bai hana ainihin sihirtaccen kyawunta fitowa ba.haka ma kayataccen fatar jikinta choculate colour ta kwanta luf luf..koda take sanye 'cikin ' hijab kyawunta bai boyuwa ba..
Sai dai fuskarta Tayi fayau ..wanda ya nuna alamun rama atattare daita kuma hakan ya sake fidda asalin siffar halittata kyawun jikinta .
Yayinda kallo daya zakayi mata kaji farar daya tashiga ranka Wanda dama tun asali Haka yanayinta yake 'tana da saurin shiga ran duk Wanda ya daura idanushi kanta , da wuya kangata kaji bata tashiga ranka ba .
babu kowa a gidan daga ita Sai safeena shiyasa ma ta samu dama ta dan sake ta zauna a parlour Dan bata manta gargadin da matar gidan Tayi mata ba .
Ahankali suke hirarsu 'cikin harshen turanci ita da safeena 'gefe daya km hankalinsu nakan TV .
Salamarsa ce da wani wanda batasan ko waye ba ,ta doki dodon kunneta Wanda hakan yayi daidai da faduwar da gaban yayi , Wanda ta rasa dalili .
dan Kusan duk sanda zata gansa ko jiyo sautin muryarsa Sai ,gabanta yayi mummunar faduwa.
Ahankali Ya karasa shigowa parlour gabadaya fk Na biye dashi a baya .
har zata dago idanunta da niyar kallon inda suke tafasa ta maida Hankalinta sosai kan TV dake aiki a parlour tare da amsa sallama aciki batare da ta dubeshi ba Shima Dan sanin mahimmancin sallamar da tayi ne Yasa ta amsawa
" Dan Tasha alwashin bazata kuma gaida shi ba tunda baya amsa gaisuwa.
Fk ya karasa shigowa parlour Sosai,ahankali idanunsa suka sauka akan nablah dake zaune Kusan minti biyu ya dauka tsaye yana kallon bakuwar fuskar daya gani agidan ,yaso kwarai ya dauke kansa daga dubanta Amman ya kasa yin hakan.
,a zuciyarsa yake tasbihi Ga ubangijin halitai Dan rabon shi da ganin kamilalliyar macce mai tarin kyau da kwarjini irinta ya Dade ,kai shi bai ma taba ganin ba .
Gabanta ya tsananta bugawa da sauri yayinda a 'cikin jikinta ta dinga jin ana kallonta km still har lokacin taki ta yarda ta juyo bayanta Dan tasan deeni ne tsaye
ke dubanta , Wanda bata tayi hakan ne sbd gujewa kanta wulakanci daga gareshi .
haka kawai taji ta takura a gurin ta kasa sakewa shanyayun idanunta dake kan TV ta lumshe gabadaya hankalinta baya gangar jikinta ta matsu su bar gurin ko ta samu natsuwar zuciyarta.
Amman hakan ya gagara samuwa Sai gani tayi ma sun samu gurin sun zauna kujerar dake facing dinta suna cigaba da hirarsu.
safeena ta gaishesu suka amsa a tare amman ita nablah ta kasa bude bakinta ta gaidasu Sai ma mikewa datayi tsaye 'tana gyara hijab din jikinta Tayi hanyar step .
fk yabi bayanta da wani irin kallo yana tunanin ko wacece ita a kasan ranshi.shima oga deeni tun shigowarsa zuciyarsa ke kanta Amman ganin yadda Tayi musu banza tamkar bata gansu ba.
, yasa zuciyarsa ta sosu kwarai ranshi ya dinga baci , ballanantana da yaga fk din yayi mata kuriiiii da idanu yana kare mata kallo hakan ya sake hassala zuciyarsa ,haushinta tare da takaicinta suka taru suka mamaye ruhinsa.
'Tana shiga dakinta ta kwanta ruf da ciki 'akan gado tana sauke ajiyar zuciya ,,wayyo.. wayyo.. Allahna wannan wacce irin maseefa ce take shirin ruguzamin rayuwa ?
,,meke shirin faruwa dani?
,,hakika wani mummunar abu Na kusanto rayuwata da Al,amurana gabadaya.
,domin yawan faduwar gabar da na keyi ta yi yawa a tun sanda nazo gidan nan wanda na rasa dalilin jin hakan .
Ahankali ta dinga maganar zuci da kanta batare tasani ba .
Ahankali taji an bude kofar dakin safeena ce tashigo ahankali 'tana kiran sunanta .
,,Ya km Muna zaune Muna hirarmu zaki gudo daki ,ki barni Ni kadai ?
,,kefa Naga alamun zaman kadaici baya damunki fa Sai ma Naga kmr baki jin dadi ..
nablah Tayi murmushi yaqe may tattare da takaici kance wlh bbu komai safeena km bbu abinda ke damuna , kawai dai Ina son Na dan kwanta na huta ne sbd Ina dan jin bacci ,kafin Aunty Zeenat ta dawo .
Ke dai ki fadi gsky ba wannan ne dalilin dayasa kika dawo daki ba . safeena ta fadi hakan 'tana kokarin zama gefen nablah , nifa Sai Naga kmr shigowar bros ne Yasa duk kika rikice kika kasa zama .
Nablah dake kwance taji gabanta ya sake faduwa jin abinda safeena tace dan Haka a sukwane ta Mike zaune 'tana bin safeena da wani kallon mamaki .
Muryarta a sanyaye tace ko daya ba abinda kike tunani bane ,kawai day Ina bukatar natsuwa ne.
to Dan me ma zan rikece na kasa zama Dan Naga yashigorsa .
Ni karfin shigowata daki yana da nasaba ne da banason Aunty Zeenat ta iske ne a parlour,n sbd gargadinta gareni if not me zaisa Na taso sbd wani alhalin ba zamansa nake yi a gidan ba .
Me zai sa nataso sbd wani alhalin ba zamansa nakeyi a gidan ba ...safeena ta sake maimaita mgnr nablah a ranta ,har ta bude baki da zumar zatayi magana Sai km Tayi shr sbd wayarta data dauki tsiwa, ta duba screen din wayar tana picking din call din 'tare mikewa tsaye dan barin dakin .
'Byn fitar safeena nablah tacigaba da zaman shr tare da tunani iri iri Wanda Kusan yawancin tunanin Na ahlin gidan su ne .
Bangaren faruk kuwa nablah Na karasa bacewa idanunshi ya maido da hankalinsa Ga deeni tare da tmbyrsa wacece wannan yarinyar may zafi Haka ?
Wani kallon wulakancin may tattare da haushi deeni yajuyo yana watsawa fk tare da jin takaicin tmbyr da fk din yayi masa.
, kallon gefe ido Shima fk yayi masa kana yacigaba ,dan Allah a Ina ummi tasamota ko tare da safeena suka zo ?
Deeni yayi masa banza tamkar bashi da yake ba ,"kai fa dan banzan yaro ne wlh wani lokacin kana jin mutune kake nakkasasu.
Zuciyar deeni gabadaya tagama cakudewa ta cure kanta guri daya 'ta daina kai kawo a gangar jikinsa
ta rasa sukunin kanta kai kawo tsabar takaicin fk .
Sai da fk yayi ta maimaita tmbyrsa sannan deeni ya furzar da iska mai zafi ta bakinsa tare da hade hannuwansa guri daya a fadadden kirjinsa ya fara mgn 'cike da dakewa da yatsina fuska yace" housemaid din ce ....
fk ya ware iduna yana kallonsa "da gaske kai amman gsky yarinyar ba tayi kama da housemaid ba wlh wannan Ai kamata yayi ace 'tana aji tana daukar darasi domin karatu ne yafi dacewa daita .
deeni ya gyara zamansa yakoma rigingine akan kujera dayake yana sakin ajiyar zuciya tare da yin shr ....tsawon lokaci fk Na zaune har ya fidda ran deeni zai sake yin magana Sai km yaji sautin muryarsa a sanyaye "sanadin karantu ne ya kawota aiki .
Fk ya saki murmushi sannan yace" ayya ..itama tasan abinda yafi dacewa daita kennan.
"to me zai hana ka taimaka mata ka
maidata Ga iyayenta sannan ka dauki nauyin karatun nata kmr yadda kasaba taimakawa mutane marasa galihu irinta .
Tsab deeni dake zaune yana sauraron bayanin fk yayi masa kallon baka da hankali 'cikin sarkamewar zuciya da rashin tsoro tare da jin zafi furuncinsa deeni yace" baza,a takaimaka mata ba.
Ya cigaba " wannan bazanr yarinyar da bata da tarbiyya zan dauki nauyin karatunta? "yarinyar da kwata kwata batasan me ake Kira da respect ba kana kallon yadda ko kallon mutunci bamu isheta ba .
"Ni wlh haushi ma kabani da naga yadda ka tsaya kana kallonta tare da zuzuta wani wai kyau gareta ko me mtssss yaja tsaki .
fk ya kwashe da wata uwar dariya "matsalata da kai kennan idan baka son mutun ,wlh har naji yarinyar ta bani tausayi
deeni ya sake jan tsaki .
"Ta baka tausayi ko?
" to kai ka dauki nauyin karatunta man ,Ai kaima Naga kana da karfin dazaka iya yin Hakan.
Fk numfasa tare cewa "wane ni wannan Sai Ku manya ..nan dai suka bar zance nabla suka shiga abinda ya kawo fk.
*****
Wasa wasa rayuwar deeni gabadaya tasoma canzawa 'acikin yan watanni nan
rabonshi daya samu natsuwa da farinciki har ya manta tun kafin zuwan nablah gidan
Dan duk sanda zai hadu da yarinyar Sai yanayinsa ya sauya hakan ma ko 'cikin baccinsa ita yake ganin zaune a gefensa tare da wasu kyawawan yara tana Miko masa masu , har kagara yake gari ya waye ya daura idanunshi akanta yanzu kam ya soma gasgata tunaninsa na mayya ce yarinyar idan kuwa ba Haka bane to 'tana da alaka da mutane boye.
Sannu ahankali sule direbansa ke jansa har xuwa , unguwar gatan kowa dake hanya iyanu - paja .
Nesa kadan da gidan da oga deeni ya bashi address sule yayi parking ahankali tare da juyowa baya yace" mai gida mun iso Ga gidan can ya karasa fadar Haka yana nunawa deeni gidan da yatsansa .
Deeni dake hakemce a bayan mota ya sake gyara zamansa yana karewa gidan da sule direbansa ya Nuna masa .
,tsawon lokaci deeni ya dauka yana kallon gaban gidan tare da Allah wadai da wannan aure da zaiyi.
" yanzu irin gidan da zai nemi aure kennan gabadaya kofar gidan a rushe yake bbu wata ishashiyar katanga Sai dan kwanun langaga da,aka zagaye shi dashi tsabar babu ,Gabadaya unguwar a hargitse take babu kyan Gani .
Ahankali kalaman umminsa ke dawo dashi 'cikin duniyar tunaninsa yayinda natsuwarsa ke kokarin shirin barin jikinsa Yanzu shi wani irin aure zaiyi ?
Anya kuwa zai iya auren .
Tunda sule direba yayi maganrsa ta karshe Bai sake yunkurin cewa uffan ba Dan gudun maseefar ogan nasa ,a sukwane sule yaji sautin muryarsa 'cikin kunnenshi "fita kayo min sallama da mai gidan iya abinda deeni ya fada kennan yaja bakinsa yayi dif...
Sule ya kashe motar Tare da barin AC motar a kunne ,ya fito yana aikin raba Idanu ta inda zaiga yaron aike .
unguwar shr... sakamakon ruwan saman da,a kwana ana sulawa ,jifa jifa mutane ke wucewa Sai da sule Bai yi dacen samu Wanda zai aika 'cikin gidan ba
dan Haka ya koma ya jingine jikinsa ajikin mota yana addu'ar kar Allah Yasa oga ya fusata har zuwa sanda zai samu dan aike .
Fitowar wani kyakyawan dattijo ne daga gidan yasa sule jin farinciki a ransa yayinda hankalinsa ya kwanta
Dattijon dake kokarin gefta shi yana faman xuba fada ,sule ya karaso da sauri Tare da yi masa sallama yana kokarin tsugunawa dattijon yayi saurin Miko masa hannu suyi musabaha.
suka gaisa sule Na tmbyrsa ,dan Allah baba mai gidan daka fito daga 'cikin sa nake nema , dattijon ya saki murmushi Tare cewa" Ai nine mai gidan .
Sule yayi murmushi yace "yauwa daman mai gidana ne yake son ganinka yana 'cikin wacce motar "
dattijon yabi hannun sule da kallo galleleyar motar dake parke nisa kadan dashi yabi da kallo
Yace "to to yaro babu komai kana iya sanarwa mai gidan naka Gani .
Sule ya juya 'cike da natsuwa ya sanar da deeni ,dake hakemce abayan mota ya ware kafafunsa yana jiran tsammani "Ce masa yakaraso nan inji cewar deeni.
Sule sake komawa yayi ya sanarwa da dattijon.
, dattijon Bai wani damu ba ya karasa kai tsaye har inda motar take sule ya bude masa sashen da deeni yake ahankali idanun deeni suka sauka akan mutumin dayake kallo yanzu a gabansa tamkar an tsaga kara da yarinyar dake zaune a gidansa .
Dattijon ya Mikowa deeni hannun domin su gaisa deeni ba Dan son ranshi ba ya bashi hannun Sai dai fuskasa a dan sake ba yabo ba fallasa .
Yace" idan bazaka damu ba kana iya shigowa daga ciki magana ce may mahimmanci takawo gareka .
Dattijon yace "bbu wata damuwa yashigo mator batare da an rufe ba Sai da deeni ya numfasa zai mgn sai km yayi shr 'yana mai toshe hancinsa da hanky sakamakon wani wari kwata daya bugo yayi nasarar shiga hancinsa ,ganin Haka Yasa dattijon janyo kofar motar ya kulle sannan DEENI ya samu damar soma mgn.
"abinda ya kawo gareka Naga wata yarinyarka ne Ina son ka aura min ita bisa sharadin... deeni yasa hannunshi yajanwo wata yar karamar jaka dake shake da kudi , ya bude" zan mallaka maka fiyye da wannan kudin matukar ka amince ..
dattijon daya Ga jiya km yaga yau ya kalli kudi masu tarin yawa sannan ya dago ya kalli deeni yana murmushi .
"Kwata kwata kasa dauke idanunshi tsohon yayi daga kallon DEENI Sai ma nazarinsa da yake .
Kusan minti goma yana nazarinsa har DEENI ya tsargu kansa sannan dattijon yace "yaro kennan wacce daga 'cikin yaran nawa kake so da aure kafin aje ga mgnr kudi babu wata shakka ko tsoro deeni yace" nablah....
dattijon yace "garama daya zama nablah ce Yar albarka duk da ina jin haushinta a raina amman hakan ba zai sa nakasa ji dadi aurar maka ita ba .
Deeni ya sauke naunauyen ajiyar zuciya jin abinda tsohon yace hakan ya tabbatar wa kansa samunta bbu wani shamaki sai dai yayi mamakin yadda dattijon yace yana Jin haushin diyarsa ta cikin .
Dattijon ya cigaba" Sai dai ita wannan yarinyar da kake magana akanta bata nan , asalima ban san inda take ba ahalin yanzu ,deeni ya numfasa sannan yace "wannan ba zai zama da wata damuwa ba muddin ka amince zaka bani aurenta ,nima tafiyace a gabana zuwa wata kasa ,dan Haka auren kawai nake da bukata a daura inyaso idan Na dawo daga tafiyar sai ayi bikin kaga itama nasan zuwa lokacin ta dawo .
Dattijon yaji dadi mgnr Sosai daman yana ciki da abinda Salmah Tayi masa Na daukar masa yarinya, ta kai gidan aikatau 'byn yace Bai amince akai masa ita aiki ko Ina ba.
,yanzu hakan ma daya fito daga gidan yana fada da Salmah " yake ce mata ta dawo masa da diyarsa muddin batason bacin ranta , dan shi baya wani bukatar Taje neman kudin karatu, yafi son ta zauna agabansa har zuwa sanda zai aurar da abarsa .
Ahankali dattijon ya dawo daga duniyar tunani daya lula yace "yaro zuwa yaushe kennan kake son auren nata .
Deeni yace " idan zai yiwu ayanzu Ma zan fi so Haka "
dattijon yace " may zai hana yiwar hakan wannan Ai abune may sauki tunda Sai ka dawo daga wata uwa duniya za'a yi bikin .
Deeni yayi shr kawai yana kallon dattijon dake zaune Kusa dashi yana kokarin amince masa batare da yasan ko shi waye ba .
Cikin mintuna da basu fi talatin ba mlm salisu ya nemo aminnansa guda hudu na nan kusa da shi cikonsu na biyar ,
Sai deeni da sule da aka daura auren nabeela salisu gulunbe da nasuruldeeni aliyu khaliyal bisa Ga sadaki naira duba dari cassssssssssss Wanda sule ne ya kasance wakilin deeni yayinda wani aminin mlm salisu din ya zama wakilin nablah .
Sule yaji mamakin wannan auren daka daura abu kmr a al,mara "to daman ogansa aure zaiyi batare da sanin kowa ?
" wannan wani irin aure ne Haka?
Byn angama daurin auren deeni ya mikowa mlm salisu jakar kudin amman mlm salisu yaki kabar sai ma cewa da yayi" nasuru ka rike kudinka domin bbu abinda zanyi dashi .
duk da bansaka ba km bansan daga inda kazo neman auren diyata ba Haka kawai naji Na amince na baka auren nabeelah Ni kawai abinda nake bukata daga gareka shine ,idan Allah Yasa ka dawo daga tafiyar da zakayi lfy kasadani Ga danginka amman bazan karbi kudinka ba .
Wani irin kunyar dattijon ne ya kama DEENI yaji tamkar kasa ta bude ya netsina ciki dan kwata kwata bai yin tunanin dattijon zai ki amsar irin wannan kudin ba a wannan zamanin da ake ciki, na kaka na kanyi,
da wuya ka samu irin dattijon duk da alamun babu da yake hangowa atattare dashi muhalinsa kadai ya isa ya tabbatar wa mutun yadda yake gudanar da rayuwarsa.
Haka kawai deeni ya samu kanshi da kiran dattijon da" baba ...
dan Allah karkayi min Haka kar kace baza karba kudin nan ba .
"Da farko nayi tunanin ba zaka amincemin da aurenta bane 'cikin wannan lokacin da nafi bukata shiyasa kaji na daura sharadi akai .
"Amman yanzu dattakonka gareni yafi karfin wannan kudin agurina dan Haka har ga Allah Na baka wannan kudin idan ma kana bukatar wasu zan karaka maka ..
mlm salisu yace" Sam ba zai karba ba sai da wani abokinsa yasa baki sannan yasa hannu ya amshi jakar kudin Tare da sanyawa deeni albarka daman km yana da bukatarsu Sukayi sallama da zumar Sai Allah Ya dawo dashi ..
***
Mlm salisu Ya shiga gidansa cike da murna yana duban Salmah da nurat Sai mahafiyarsu dake zaune suna tattaunawa akan batun nablah din .
Ya karasa shigowa yana murmushi Tare da ajiye musu jakar kudi a gabansu ya zuge.
Kudin suka bayayyana bbu Wanda Bai ji tsoron ganin kudin ba sbd tsabar yawansu .
Mlm salisu yace "
Ku duba kuga ikon Allah sanadin diyata nabla Yar albarka Na samesu suka shiga dubansa da alamun tmby a saman fuskokinsu .
ya cigaba" yanzu nan Na daurawa nablah aure da wani mutumin kirki daya zo neman aurenta km shiya bani wannan kudaden da kuke Gani .
mahaiyarsu saratu wacce suke Kira da mama tace "wacce nabeela kake mgnr ka daurawa aure ?
"Ina da wata nabeela ne byn diyata ?
"Kuma ita din aka daurawa aure yanzu
gama sadakinta nan ya fidda wasu kudin daga aljihunsa .
Mama tace "cewa zakayi kasiyar min da yarinya kawai bawai ka daura mata aure ba amman abinda zai sa hankalina ya kwanta sanin inda nablah take a halin yanzu Dan haka duk ma Wanda kabawa aurenta ka bashi gaibu , Ka dai daura aure dashi ne Amman bashi da mata .
Mlm salisu ya hade rai "Ke dai kika sani Yar Bakin ciki kawai Ai ba tun yau nasan bakya son cigaba Na ba, Yariya dai tawa ce to Na aurar daita Ga Wanda nake so km kina zaune za'a yi bikin nablah ta wuce gidan aurenta .
Duk magangun da mlm salisu ke yi mama Tayi shr batare da ta sake cewa komai ba sbd alamun da Salmah Tayi mata Na kar tayi mgn .
"Ke km Salmah mlm salisu ya koma kanta " wlh wlh kinji ransuwar muslimi kwana biyu kacal na baki ke dawo min da yarinyata mai kan sa'a da kashin arziki kafin nasoma cin uwarki ,
dan wulakanci ke kina zaune a gidan mijinki lfy Sai tawa Yar ce ta iya zuwa neman abin duniya ke kar ma Na sake ganin kafarki a gidan nan muddin ba da nabeela bane shasha banza dabatasan ciwon kanta ba yaja tsaki yana kokarin shegewa ciki kuryar da jakar kudinsa , Gabadayansu da idanu suka bishi da shi hankalinsu ,a tashe.
"Kirrrrrrrrrr... kirrrrrr ......kirrrrrrrr... karar bell ya cika koina a gidan nablah dake tahowa daga kan step ta hanzarta saukowa da sauri ta nufi Bakin kofa ta bude .
Kabiru mai wankin Zeenat ta Gani tsaye a 'bakin kofa yana sakar mata murmushi itama murmushi Tayi masa tare da gaidashi.
Daidai lokacin da motar deeni ta sanyo kai 'cikin estate din idanunshi suka sauka akan fuskar nablah dake sakarwa kabiru murmushi
take annurin dake fuskarsa ya dauke gabansa ya daki uku uku ya fadi take zuciyarsa tashiga aikinta data saba wato dokawa da sauri har sanda sule yayi parking motar idanunshi na kansu ya kasa daukewa.
"malama nablah kennan ya gida da aiki inji cewar kabiru ?
Nablah tace "duk lfy wlh ya naka aikin ?
Shima ya amsa mata da "lfy"
Nan suka shiga hira sama sama dashi sbd sun dan saba .
Kusan minti goma deeni yayi zaune a mota ya kasa fitowa sakamakon dokawar da zuciyar keyi da sauri ya dinga jin tamkar ana masa wanka ne da tafashashen ruwan zafi ajikinsa yayinda natsuwarsa ke kokarin barin gangar jikinsa take gumi ya rufe shi takoina ajikinsa .
ahankali ya ciro hanky daga aljihun gaban rigarsa ya goge gumin dake tsaftsafo masa batare da ya sauke idanunshi daga kallonsu ba har zuwa sanda yaga kabir ya Miko mata kaya a wata jaka ya juya yana sake yiwa nabla murmushi
Wanda sauran kadan zuciyar deeni ta tarwatse tsabar frigici .
Ahankali ya soma kokarin fitowa daga mota byn sule ya bude masa
'Tana shiga gidan taje ta, ajiye kayan a inda tasaba ganin ana ajiyewa sannan ta nufi kitchen ta soma aikin girki hade da wanke kayan da akayi amfani dasu, kasancewa yau Sunday ce.
Laraba tana church ummi kuma sun fita tare da aunty zeenat da safeena ba yadda ummi da safeena basu daita akan tazo su fita tare tace A'a saboda ita bata damu da yawan fita ba ko agidansu.
cikin sanyi jiki take aikinta da zeenat ta gama koya mata kalar abinci da mai gidan yafi son cin ne yau aka bata practices dan aga yadda kwarewarta tayi.
kamshin turaren mat Hamilton 27 data shaka ne ya haddasa mata faduwar gaba Wanda tun safe take jinta Haka .
DEENI tsaye abakin Kofar kitchen din yana aiko mata da kallon tsana bayan yaje yayi freshe up .
Cikin tsananin tsoro da fargaban abinda zata Gani ta juyo karaf idanunsu suka sarke cikin juna take zuciyoyiinsu ya bagu... gabansu Yashiga faduwa da sauri tayi kasa da kanta ta dinga karanto duk wata addu'a datasani na neman tsari .
Ahankali ya tabe bakinsa ya karaso cikin kitchen din Sosai cikin muryasa may matukar dadi da sauraro yace" ke..uban me kike Jira da har yanzu baki gama abinci ba ?
wani irin shock...ne ya jata ,jikinta ya soma sheking ta kasa furta komai ya daka mata wata irin razananniyar tsawa "ke ..
Ba magana nake miki ba? ya karasa maganar cikin kunar rai .
muryarta na rawa tace "dan Allah kayi hakuri wlh na kusan gamawa yace" you are very stupid dake da gamawarki kina tunanin an daukeki aiki ne dan kidinga yiwa mutane iskanci da aikin ba'a kan lokacin ba.?
mamaki hade da tsoro sukayi nasarar lullubeta ko kwakwarar motse gagararta yayi .
yayinda haushinta ya sake turnuke wuyan DEENI a harzuke ya fizgo hannuta yace "ke me kike takama dashi ke waye ma ubanki duk fadin Africa da har zandinga miki magana kiyi banza dani?
tayi kokarin fizge hannuta sai dai kashi ...ta kasa abunka ga soja gata yarinya karfin su ba daya ba , ko namiji DEENI yarike da wuya ya iya kwatar kansa.
ranta ya baci matukar dan haka itama fusace tace "dan Allah malam ka sakar min hannu .
kallon baki isa ba ya watsa mata sannan ya sake matse mata hannu Sosai yana kallonta cikin tsigar wulakancin hade da sake damke laulausar fatar hannuta.
yace "ki kwace hannu mana idan kin isa " ta soma girgiza masa kai dan wani irin radadin azaba da takeji acikin kashin hannuta ,
tayi kasa da kanta 'tana zubda hawaye tausayin kanta domin ita ta kawo kanta cikin wannan maseefar da take ciki,
ashe rabon wahala ne yakawota gidan batasani ba .
sai da yaga ji dan kansa sannan ya wurgar da hannu nata da karfe ya juya cikin tafiyarsa ta kasaita da jan hankalin duk wanda ya kalleshi.
" minti goma kacal na baki kigama sannan ya karasa barin kitchen.
ta durkusa kasa tare da fashewa da wani matsanancin kuka ta soma datasanin zuwanta aiki uguwar lekki ,da kyar ta iya mikewa ,
tacigaba da aikin girkin hawaye nabin kuncinta sai da ta kammala da komai ta shirya akan dening area sannan tazo ta wuce ta gabansa yana kwance a kan three siters hannunsa dafe da kirjinsa har tayi step daya zuwa uku ta jiyo shigowarsu ummi ta dawo ahankali hade dayi musu sannu da zuwa .
ummi da safeena suka bita da kallo byn ta amsa sannan ummi tace" ya na ganki haka wani afrigice afrigice?
nablah ta kirkiro murmushin dole tace" bbu komai ummi .
"Amman naga idanuki kmr kinyi kuka cikin sanyi murya tace "uhm ....dazo ne danake aiki wani abu ya fadamin a ido .
ummi tace" ok sannan ta juya gun zeenat dake zaune kusa da DEENI tana tambayarsa ko yaci abinci a harzuke ya bude idanunshi tare da watsa mata harara sannan ya juya mata baya "please i don't won't any distoping ... now.
Zeenat bata daddaraba Ta sake tmbyesa kowani abu Na damunsa ne " Zeenat.... yakira sunanta a kausashe " why are you distracting my hrt ...?
tace sorry Tare da mikewa tsam tayi dakinta gudun kada ya wuce akanta duk da batasan sanadin fushin nashi ba.
nablah dake tsaye kusa ummi dan olready safeena ta bar gurin tace "bari nima na bace daga nan .
dan abinda nablah tayi noticing daga deeni hatta matar aurensa ba raga mata yake ba
,Ina Ga ita bazanr bazara dan Haka ta zame ta gudu dakinta ta barshi da ummi .
Ummi ta zauna gefensa tana tofeshi da addu'oi ta rasa wani irin zafi rai ne haka ke damun dan nata abin fushi dama wanda bana fushi ba duk yi yake tsawon lokacin yana kwance har sanda yaji kiransa daga masallaci dake 'cikin gidan ya mike a sukwane ya dan kalli ummi kmr zaiyi mata murmushi sai kuma ya fasa ta kira sunansa ya dago batare da ya amsa ba Kaci abinci ?
ya yasina fuska har dimple dinsa na lotsawa dan haka ta gane bai ci ba .
da hannuta ta nuna masa alamun ya koma ya zauna
da kanta taje dinning ta bude kulolin abinci taji kamshin ya bugi hancinta ta zubo masa abinci takawo masa har gabansaTace "oya ci abinci ahankali ya soma motsi bakinsa f"irst love nifa bazan ci wannan jagwalgwalon yarinyar nan ba ummi ta koma ta zauna inda ta tashi ta hade fuska tamau ta kiyin magana sai idanu data zuba masa 'tana kallonsa
dan haka yake wani lokacin idan yana cikin fushi dayaga ta hade rai sai kaga ya soma shiga taitayinsa dan HK ya dan sake fuska kadan yasoma cin abinci yana kai lomar farko yaji kunnenshi ya dan yi sheking yasa hannunsa yana tsosa gun wasa wasa dai sai da oga DEENI ya tashi da Rabin plate sannan ummi ta sakin ranta tana masa dariya tace "har ka koshi kennan da dai kakarasa cin jagwalgwalon mana?
" shegen salo da iyayi kawai "
ya yasina fuska yana kallon umminsa yace "uhmm bayan manage kawai nayi wajen tura abinci ummi ta sake yin dariya "tooo ..nagode da kayi manage Kaci ya gane sarai tsokanarsa ummi take dan haka bayan mike yana ce mata shi ya wuce masallaci .
Ita kuwa nablah tana shiga dakinta karamin Fridge din dake dakin ta bude Tasha ruwan.
gashi tana jin wani irin maseefaffen bacci Amman batason tayi bacci byn la'asar sai yanzu tasoma kwadayin rike waya a hannuta dan ko ba komai zata rinka rage mata kewargida. tajawa kanta tsaki tace kai nablah kin cika yawa wlh karfe biyar daidai ta sauko parlour kasa tasamu lokacin duk suna kallo .
ko kallon inda ummi da deeni su ke zaune batayi ba wajen zeenat tayi tana tmbyrta ko akwai aikin da zatayi duk da tasan ta kammala da komai kuma laraba ma ta dan jima da dawo wa
Zeenat ta girgiza kai kawai batare datace komai ba Shima ganin ummi dake zaune.
dan yanzu takanyi shakkan yi mata wani abu a gaban ummi.
Nablah ta juya takoma dakinta ta zuge handbag dinta ta dauko currency affairs 'tana dubawa ahankali har aka Kira sallah magariba.
MMN SUDAIS CE
YOU ARE READING
AUREN SIRRI
FantasyMATARSA CE TAKE ZUBAR DA CIKI BISA WANI DALILI NATA WANDA SANADIYAR HAKA SURUKARTA TAYIWA MIJIN DATA FI QAUNA FIYYE DA KOMAI A DUNIYA AUREN SIRRI DA ME AIKINTA BATARE DA SANINRA BA..