AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDG
Page 106
....Byn kowa ya watse, parloun'n ya ɗauki shiru na tsawon wani lokaci big dady ya dinga kallon deeni yana mamakin reaction dinsa na d'azu daya dinga yi akan yarinyar.
"ahankali Big dady ya cigaba da kallonsa tamkar wani sabon Halitta a gabansa,
sakamakon yadda cikin kankanin lokaci gabadaya kamaninsa suka sauya ya dawo wani irin mutun Abin tausayi.big dady yake kalleshi tare da nazarinsa Kana ya numfasa muryarsa a matukar raunane irin ta Manya ya kira sunan shi..... deeni ya d'ago rikitattun idanunshi da suka gama canza kala tsabar rud'ani da tashin hankalin da yake ciki
ya zubawa big dady yana kallonsa batare da yace uffan ba.
" sai ma hadiye abinda ya tsaya masa amakoshi yayi yana maida hankalinsa sosai gurin sauraron abinda big dady zai ce .Big dady ya sake fuskantarshi da kyau sannan yace "nasuruldeeni na fuskacin kana matsanancin son yarinyar nan nabeelah kana mata mahaukacin so fiyye da tunanin me tunani wannan kalubali ne a gareka sannan km babban yaki ne akanka daka San yadda zaka shawo hankalin yarinyar nan cikin sauki
saboda da ganin yarinyar tana da kafiya da taurin Kai da taurin zuciya sai kayi mugun aiki da kuma yaki sannan Zaka samu ka shawo kanta da hankalinta, " musamma sbd abinda akayiwa yarinyar wanda kowace Mace akayiwa hk zata iya yin hauka fiyye da nata .
Kuma na lura sosai kafi son yarinyar akan zeenat duba da yadda ka dinga yi wasu abubuwa agabanmu gabadaya idanunka sun rufe deeni akanta,so ni dai abinda zance anan bai wuce nace ka yiwa Allah kayi aldalci atsakaninsu.." kayi adalci atsakanin matanka kada ka taba fifita ɗaya akan ɗaya karka sake ka bari ɗaya ta gane kafin son daya a kanta ,duk wacce Kake so axuciyarka ka barwa ranka ya zama sirrin zuciyarka .
daman dole ne sai ka samu wacce zakaji kafi so a tsakanin matanka
Amman karkar kuskura ka bayyanawa kowace daga cikinsu,ka barwa zuciyarka kayi adalci kaji tsoron Allah ka rike matanka amana dan karkaga nabeelah ce me haihuwa uwar ya'yanka kace zaka wulakanta zeenat sannan kada kaga zeenat yar'uwarka ce ka biyewa mahaifiyarka ku taru ku wulakanta nabeelah..
sosai big dady ya dinga masa Nasiha me ratsa jiki da huda zuciya da saka zuciya nadamar abinda ta aikata."Sannan zance ita yarinyar nan nabeelah ka barta anan tukun kafi asan abin yi ya daga kanshi alamun yaji.
byn big dady ya gama dashi yace idan ya fita ya turo masa zeenat Jikinsa a matukar sanyaye ya mike tsaye da kyar yana yiwa big dady sallama hade da godiya...Byn ya fito ya iske zeenat zaune a karamin parlour'n gidan ya zauna kusa daita sosai yana jin wani irin matsanancin tausayinta yayinda sound din kukanta ke taba zuciyarsa gaba-daya nadamar abinda ya aikata agabanta yake ,
hakika bata cancanci hk daga gareshi ba kodan duba da yadda take matukar kaunarshi fiyye da komai arayuwata , cikin sayin jiki ya kamo tafin hannuta cikin nashi ya soma murzawa ahankali ahankali kafin yace wani Abu.Da sauri ta zame hannuta cikin nashi tare da juyar da kanta alamun bata son ganinsa
yaja numfashi da karfi ya fetsar yana tsura mata rikitattun idanunshi yana kallonta cike da tausayawa ,sannan ya bude bakinsa da kyar ya kira complete Name dinta" muzeenat ..........
zeenat taki juyowa ta kalli inda yake ballantana yasa rai da samun amasart.
sai ma jijjiga kafar ɗaya da take tana cizan lips dinta, muryarsa a raunane ya sake kiran sunanta "My Zeenat am sorry.... am very sorry for what I did...nasan ban kyauta miki ba
sannan baki cancanci hk agurina ba.
" tabbas naso na kuntatawa rayuwarki alokacin da kikayita zubar min da cikina arariya ....Amman bata wannan hanyar ba
Ko auren sirrin dana Yi da nablah ba'a son Raina nayi ba.
Umarnin first love nabi wanda alokacin gabadaya daurewar farincikinki take nema agidana amman kiyi hakuri please ki yafemin bisa biyyewa first love da nayi gurin boye miki..
duk wannan bayanani dayake mata bata juyo ta kalleshi ba har ya gaji ya Mike da niyar wucewa tare da Sanar mata da sakon Big dady.
YOU ARE READING
AUREN SIRRI
FantasyMATARSA CE TAKE ZUBAR DA CIKI BISA WANI DALILI NATA WANDA SANADIYAR HAKA SURUKARTA TAYIWA MIJIN DATA FI QAUNA FIYYE DA KOMAI A DUNIYA AUREN SIRRI DA ME AIKINTA BATARE DA SANINRA BA..